Ka Koya Daga Kalmar Allah
Yaya Ya Kamata Mu Tuna da Mutuwar Yesu?
Wannan talifin ya tattauna tambayoyin da wataƙila ka taɓa yi kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. A wace hanya ce ya kamata mu riƙa tunawa da mutuwar Yesu?
Yesu ya gaya wa mabiyansa su riƙa tunawa da mutuwarsa ta wajen yin amfani da abinci na alama, wato, gurasa da ruwan anab. Gurasar tana alamta jikin Yesu, kuma ruwan anab yana wakiltar jininsa.—Karanta Luka 22:19, 20.
Yesu ya yi amfani ne da gurasa marar yis. A cikin Littafi Mai Tsarki, sau da yawa yis yana nufin zunubi. Saboda haka, irin wannan gurasar ta dace sosai wajen alamta kamiltaccen jikin Yesu. Hadayar da ya yi da jikinsa, ta kawo ƙarshen hadayar da ake yi da dabbobi a ƙarƙashin Dokar Musa. (Ibraniyawa 10:5, 9, 10) Ruwan anab ɗin ya alamta jini mai tamani na Yesu wanda ya yi hadaya da shi domin zunubanmu.—Karanta 1 Bitrus 1:19; 2:24; 3:18.
2. Yaushe ne ya kamata mu tuna da mutuwar Yesu?
Yesu ya mutu a ranar 14 ga Nisan, wato, ranar Idin Ƙetarewa. A al’adar Yahudawa, ana soma ƙirga yini ne sa’ad da rana ta faɗi. Yesu ya ci gurasa da ruwan anab na Idin Ƙetarewa tare da manzanninsa a yamman da ya mutu. Bayan haka, ya gabatar da sabon jibin da za su riƙa ci don tunawa da mutuwarsa.—Karanta Luka 22:14, 15.
A yau, mutanen Allah suna tunawa ne da tanadin da Allah ya yi ta hanyar Yesu don ya ’yanta dukan mutane daga zunubi da mutuwa. (Fitowa 12:5-7, 13, 17) Kamar yadda ake yin Idin Ƙetarewa sau ɗaya a shekara, hakazalika, ana yin taron Tunawa da mutuwar Yesu sau ɗaya a shekara a ranar 14 ga Nisan bisa kwanan watan Yahudawa.—Karanta Yohanna 1:29.
3. Su waye ne ya kamata su ci gurasar kuma su sha ruwan anab ɗin?
Sa’ad da Yesu ya miƙa wa mabiyansa ruwan anab, ya ce: “Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne.” (1 Korintiyawa 11:25) Sabon alkawarin ya sauya alkawarin da Allah ya yi a cikin Dokar da ya ba Musa, inda Allah ya yi wa Isra’ilawa alkawari cewa idan suka yi masa biyayya, za su zama mutanensa. (Fitowa 19:5, 6) Amma, Isra’ilawa ba su yi biyayya ga Allah ba. Hakan ya sa Jehobah ya yi sabon alkawari.—Karanta Irmiya 31:31.
Ta hanyar wannan sabon alkawari, Jehobah ya yi amfani da mutane kaɗan don ya albarkace mutane da yawa. Waɗanda aka ƙulla alkawarin da su ba su da yawa, wato, mutane 144,000 kawai. Ta wurin su, miliyoyin mutane daga dukan al’ummai za su samu rai na har abada a cikin aljanna a duniya. Waɗansu da suke bauta wa Jehobah a duniya a yau suna cikin waɗanda aka yi wa wannan alkawarin. Su kaɗai ne ya kamata su ci wannan gurasar kuma su sha wannan ruwan anab ɗin, domin Jehobah ya ƙulla alkawarin da su, kuma jinin Yesu ya tabbatar da hakan.—Karanta Luka 12:32; Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3.
4. Ta yaya taron Tunawa da mutuwar Yesu zai amfane mu?
Tunawa da mutuwar Yesu da muke yi a kowace shekara tana sa mu ƙara nuna godiya ga Jehobah saboda irin ƙauna mai girma da ya nuna mana. Ya aiko Ɗansa ya mutu domin zunubanmu. Saboda haka, sa’ad da muka halarci taron Tunawa da mutuwar Yesu, ya kamata mu yi tunani sosai a kan amfanin mutuwar da Yesu ya yi domin mu. Ya kamata mu yi tunani a kan yadda za mu nuna godiya ga Jehobah da Yesu domin abin da suka yi mana.—Karanta Yohanna 3:16; 2 Korintiyawa 5:14, 15, Littafi Mai Tsarki.
Don ƙarin bayani, ka duba shafuffuka na 206-208 na wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.