Ka Kusaci Allah
‘Gama Ni Ubangiji Allahnka, Ina Riƙe Hannun Damanka’
“KA RIƘE hannuna,” hakan wani mahaifi ya gaya wa ɗansa sa’ad da suke son su tsallaka titi. Yaron ba ya fargaba domin mahaifinsa yana riƙe da hannunsa. Ka taɓa yin tunanin cewa zai yiwu wani ya yi maka ja-gora a wannan rayuwar da ke cike da matsaloli? Idan haka ne, kalmomin da Ishaya ya rubuta za su ƙarfafa ka.—Karanta Ishaya 41:10.
Ishaya yana magana ne ga Isra’ilawa. Ko da yake Allah ya ɗauki al’ummar a matsayin “keɓaɓiyar taska” tasa, al’ummar tana kewaye da maƙiya. (Fitowa 19:5) Ya kamata Isra’ila ta tsorata ne? Jehobah ya gaya wa Ishaya ya idar da wani saƙo mai ƙarfafawa. Yayin da muke bincika waɗannan kalmomin, mu tuna cewa sun shafi masu bauta wa Allah a yau.—Romawa 15:4.
‘Kada ku ji tsoro,’ in ji Jehobah. (Aya ta 10) Waɗannan kalmomin ba fanko ba ne. Jehobah ya bayyana dalilin da ya sa mutanensa ba sa bukatar jin tsoro: ‘Gama ina tare da ku.’ Shi ba wani ɗan agaji ba ne da ke nesa, wanda zai kawo ɗauki sa’ad da matsaloli suka taso. Amma yana son mutanensa su san cewa yana tare da su a kowane lokaci, don ya taimake su. Hakan tabbaci ne mai ban ƙarfafa, ko ba haka ba?
Jehobah ya ci gaba da tabbatar da masu bauta masa cewa: ‘Kada ku yi fargaba.’ (Aya ta 10) Kalmar Ibrananci da aka yi amfani da ita a nan tana nuni ga waɗanda suke “duba ko’ina domin su ga ko akwai wani abin da zai iya cutar da su.” Jehobah ya bayyana dalilin da ya sa mutanensa ba sa bukatar jin tsoro: ‘Gama ni ne Allahnku.’ Hakika, waɗannan kalmomi ne masu ƙarfafawa. Jehobah shi ne “Maɗaukaki,” “Mai-iko duka.” (Zabura 91:1) Tun da yake Jehobah mai iko duka ne Allahnsu, tsoron me za su ji?
Mene ne masu bauta wa Jehobah suke sa ran samu daga wurinsa? Ya yi alkawari: ‘Zan taimake ku, i, zan riƙe ku da hannun dama na adalcina.’ (Aya ta 10) Ya kuma ce: ‘Ni Ubangiji Allahnku zan riƙe hannun damanku.’ (Aya ta 13) Mene ne ya zo zuciyarka sa’ad da ka ji waɗannan kalmomin? Wani littafi ya bayyana cewa, “idan aka yi la’akari da waɗannan ayoyi guda biyu, za a ga cewa sun ba da kwatanci mai kyau na mahaifi da ɗansa. Ba wai [Mahaifin] yana tsaye a gefe ɗaya don ya kāre yaron ba ne, a’a, yana tare da yaron a kowane lokaci; ba zai yarda yaron ya rabu da shi ba.” Ka yi tunani, Jehobah ba zai taɓa yarda wani abu ya raba shi da mutanensa ba, ko da suna cikin matsanancin hali.—Ibraniyawa 13:5, 6.
Masu bauta wa Jehobah a yau za su iya samun ƙarfafawa daga kalmomin da Ishaya ya rubuta. A waɗannan “miyagun zamanu,” a wasu lokatai muna iya jin cewa matsaloli na rayuwa sun yi mana yawa. (2 Timotawus 3:1) Amma ba ma bukatar mu fuskanci waɗannan matsalolin mu kaɗai. A shirye Jehobah yake ya taimaka mana. Kamar yaran da suka amince da mahaifinsu, bari mu amince da shi, mu ba da gaskiya cewa zai yi mana ja-gora a hanyar da ta dace kuma zai taimaka mana a lokacin da muke cikin matsala.—Zabura 63:7, 8.