Ka Kusaci Allah
“Ba Za A Tuna da Al’amura Na Dā Ba”
WAIWAYE, shi ne adōn tafiya. Idan muka tuna abubuwa masu daɗi da muka yi tare da waɗanda muke ƙauna, hakan yana sa mu farin ciki. Amma akwai lokatai da tuna abubuwan da suka faru a dā zai sa mu baƙin ciki sosai. Akwai abubuwan da suka faru a rayuwarka a dā da suke sa ka baƙin ciki? Idan haka ne, kana iya cewa, ‘Wai akwai ranar da zan daina tuna abubuwa na baƙin ciki da suka faru a rayuwata?’ Za mu iya samun amsar da za ta ƙarfafa mu a cikin kalmomin da annabi Ishaya ya rubuta.—Karanta Ishaya 65:17.
Jehobah yana da niyyar kawar da duk wani tunanin da ke sa mu baƙin ciki. Ta yaya? Zai kawar da mugun yanayin da duniya take ciki da kuma wahala, kuma zai sauya hakan da kyakkyawan yanayi. Jehobah ya yi wannan alkawarin ta bakin Ishaya: “Ga shi, sabobin sammai da sabuwar duniya na ke halitta.” Fahimtar wannan alkawarin zai sa mu kasance da bege.
Mene ne sababbin sammai? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abubuwa biyu da za su taimaka mana mu fahimci hakan. Na farko, akwai wasu marubutan Littafi Mai Tsarki su biyu da suka ambata sababbin sammai, kuma a wurare biyun da hakan ya bayyana, sun ambata gagarumin canjin da za a samu a duniya. (2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 21:1-4) Na biyu, a cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan “sammai” a wasu lokatai tana nufin sarauta ko kuma gwamnati. (Ishaya 14:4, 12; Daniyel 4:25, 26) Saboda haka, sababbin sammai yana nufin sabuwar gwamnati wadda za ta sa adalci ya dawwama a duniya. Gwamnati guda ce kawai za ta iya cim ma hakan, wato, Mulkin Allah, ita ce gwamnati ta sama da Yesu ya koya mana mu riƙa addu’a cewa ta zo. Wannan Mulkin zai sa a yi nufin Allah a dukan duniya.—Matta 6:9, 10.
Mece ce sabuwar duniyar? Ka yi la’akari da dalilai guda biyu da aka ɗauko daga Nassi da suka taimaka mana mu san amsar. Na farko, a cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan “duniya” a wani lokaci tana nufin mutane, ba duniyar da muke ciki ba. (Zabura 96:1) Na biyu, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa a ƙarƙashin sarautar Allah, ’yan Adam masu aminci za su koyi adalci, kuma hakan zai bazu a duniya. (Ishaya 26:9) Saboda haka, sabuwar duniya tana nufin mutanen da za su miƙa wuya ga sarautar Allah kuma su bi ƙa’idodinsa masu adalci.
Ka soma ganin yadda Jehobah zai kawar da duk wani tunanin da ke sa mu baƙin ciki? Ba da daɗewa ba, Jehobah zai cika dukan alkawarinsa na sababbin sammai da sabuwar duniya, wato, sabuwar duniyar da ke cike da adalci.a A sabuwar duniya, abubuwan da za su sa mu tuna dā da baƙin ciki, kamar su rashin lafiya da duk wani irin tunani na baƙin ciki, za su shuɗe. ’Yan Adam masu aminci za su more rayuwa yadda ya kamata, kuma za su kasance a cikin farin ciki a kowace rana.
Amma, baƙin cikin da ke damun mu fa yanzu? A alkawarin da Jehobah ya yi ta bakin Ishaya ya ce: “Ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.” Duk wani baƙin cikin da muka yi a wannan duniyar zai shuɗe. Sanin hakan ya faranta maka rai ko? Idan haka ne, me ya sa ba za ka bincika yadda za ka kusaci Allahn da ya yi alkawarin yin waɗannan abubuwa a nan gaba ba?
[Hasiya]
a Don samun ƙarin bayani game da Mulkin Allah da abin da zai cim ma ba daɗewa ba, ka duba babi na 3 da 8 da kuma 10 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? wanda Shaidun Jehobah suka wallafa.
[Bayanin da ke shafi na 29]
Jehobah ya yi alkawarin kawar da duk wani abin da ke sa mu baƙin ciki