Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 10/1 p. 10
  • Jehobah Yana Yin Farin Ciki ko Baƙin Ciki Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Yin Farin Ciki ko Baƙin Ciki Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Gama Ni Ubangiji Allahnka, Ina Riƙe Hannun Damanka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • “Muna Roƙon Ka Ka Bari Mu Dawo Gida”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Menene Jehobah Yake Bukata a Gare Mu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Abin da Za Ka Yi Idan Wani a Iyalinku Ya Bar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 10/1 p. 10

Ka Kusaci Allah

Jehobah Yana Yin Farin Ciki ko Baƙin Ciki Kuwa?

IDAN amsar e ce, wata tambayar ita ce: Halinmu yana shafan yadda Allah yake ji kuwa? Wato, ayyukanmu za su iya sa Allah farin ciki ko kuma baƙin ciki ne? Wasu ’yan falsafa na dā sun ce a’a. Suna da’awar cewa babu wanda zai iya shafan yadda Allah yake ji saboda haka, Allah ba ya jin kome. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana da juyayi kuma yana damuwa sosai da abubuwan da muke yi. Ka yi la’akari da kalmomin da aka rubuta a Zabura 78:40, 41.

Zabura ta 78 ta nanata yadda Allah ya yi ma’amala da al’ummar Isra’ila ta dā. Bayan ya ’yanta al’ummar daga bauta a ƙasar Masar, Jehobah ya ba su damar ƙulla dangantaka ta musamman da shi. Ya yi musu alkawari cewa idan suka ci gaba da bin dokokinsa, za su zama ‘keɓaɓɓiyar taska’ kuma zai yi amfani da su a hanya mai ban al’ajabi don ya cika nufinsa. Mutanen sun yi na’am da hakan kuma suka amince da Dokar alkawarin. Sun yi abin da suka ce za su yi kuwa?—Fitowa 19:3-8.

Wani marubucin zabura ya ce: “So nawa suka tayar masa a cikin jeji!” (Aya ta 40) Ayar da ke biye ta daɗa da cewa: “Suka yi ta jarraba Allah a kai a kai.” (Aya ta 41, Littafi Mai Tsarki) Za ka ga cewa marubucin ya nuna yadda suka riƙa yin tawaye. Wannan halin rashin biyayyar da tawaye ya soma ne a cikin jeji jim kaɗan bayan an cece su daga ƙasar Masar. Mutanen suka soma yi wa Allah gunaguni, suna shakkar ko Allah yana da ƙarfin kula da su kuma ko yana da niyyar yin hakan. (Littafin Lissafi 14:1-4) Wani littafin bincike domin masu fassara Littafi Mai Tsarki ya ce ‘wata hanya dabam da za a iya faɗin kalmomin nan’ “suka tayar masa,” ita ce ‘sun ƙandare zukatansu ga Allah’ ko kuma ‘sun ce “A’a” ga Allah.’” Duk da haka, saboda jin ƙansa, Jehobah yana gafarta wa mutanensa sa’ad da suka tuba. Amma sai su koma ga halayensu na dā kuma su sake yin tawaye, kuma hakan ya ci gaba da faruwa.—Zabura 78:10-19, 38.

Yaya Jehobah yake ji a duk lokacin da mutanensa da ba sa riƙe amincinsu suka yi tawaye? “Suka ɓata masa rai,” in ji aya ta 40. Wata fassara ta ce suna “sa shi baƙin ciki.” Wani littafin bincike na Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa: “Ma’anar ita ce halayen Ibraniyawan ya jawo mugun baƙin ciki, kamar halin ɗan da ya yi rashin biyayya da kuma tawaye.” Kamar yadda ɗa kangararre zai iya jawo wa iyayensa mugun baƙin ciki, Isra’ilawa da suka yi tawaye sun “cakuni [ɓata ran] Mai-tsarki na Isra’ila.”—Aya ta 41.

Mene ne za mu iya koya daga wannan zaburar? Abin ƙarfafawa ne mu ga cewa Jehobah yana da dangantaka ta kud da kud da masu bauta masa kuma ba ya saurin fid da rai a kan su. Haka kuma, ya kamata mu riƙa yin tunani sosai kuma mu natsu, sanin cewa Jehobah zai iya yin baƙin ciki ko farin ciki kuma halayenmu za su iya shafan yadda yake ji. Ta yaya sanin hakan ya shafe ka? Hakan ya motsa ka ka so yin abin da ya dace?

Maimakon mu bi tafarkin zunubi kuma mu sa Jehobah baƙin ciki, muna iya bin tafarki mai kyau kuma mu faranta masa rai. Ainihin abin da yake nema daga masu bauta masa ke nan: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata.” (Misalai 27:11) Babu abu mafi daraja da za mu iya ba Jehobah fiye da yin rayuwar da za ta faranta masa rai.

[Bayanin da ke shafi na 10]

Babu abu mafi daraja da za mu iya ba Jehobah fiye da yin rayuwar da za ta faranta masa rai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba