Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 4/1 pp. 10-11
  • “Muna Roƙon Ka Ka Bari Mu Dawo Gida”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Muna Roƙon Ka Ka Bari Mu Dawo Gida”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Na Tuba”
  • ‘Hakika Zan Yi Masa Jin Ƙai’
  • “Ya Jehobah Ka Bar Ni In Dawo Gida”
  • “Ranka Zai . . . Durƙusa a Kaina”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Darussa Daga Littafin Irmiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Yi Gaba Gaɗi Irin Na Irmiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehobah Yana So Kowa Ya Tuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 4/1 pp. 10-11

Ka Kusaci Allah

“Muna Roƙon Ka Ka Bari Mu Dawo Gida”

Ka taɓa bauta wa Jehobah? Kana tunanin sake soma bauta masa amma kana shakkar ko zai karɓe ka? Don Allah ka karanta wannan talifin da wanda ke biye da shi a hankali. An shirya su ne musamman domin ka.

“NA ROƘI Jehobah ya bar ni in sake soma bauta masa kuma ya gafarta mini zunubaina.” In ji wata matar da ta daina bauta wa Allah kuma ta bijire wa ƙa’idodin Kirista da aka koya mata sa’ad da take girma. Ka ji tausayin ta ko? Ka taɓa tunanin, ‘Yaya Allah yake ji game da waɗanda suka taɓa bauta masa? Yana tunawa da su kuwa? Yana son su “dawo gida”?’ Bari mu bincika abin da Irmiya ya ce don mu amsa waɗannan tambayoyi. Babu shakka, amsoshin za su sa ka farin ciki.—Karanta Irmiya 31:18-20.

Ka yi la’akari da yanayin da ake ciki sa’ad da Irmiya ya rubuta waɗannan kalmomin. A shekara ta 740 K.Z., shekaru da dama kafin zamanin Irmiya, Jehobah ya ƙyale Asuriyawa su kai ƙabilu goma da ke daular Isra’ila zuwa bauta.a Allah ya ƙyale masifar nan ne ta faɗa wa mutanensa don ya yi musu horo, saboda mugayen zunuban da suka yi kuma sun yi kunnen uwar shegu wa annabawan da ya aika su gargaɗe su a kai a kai. (2 Sarakuna 17:5-18) Bayan da aka raba su da Allahnsu da kuma ƙasarsu, wahalar da mutanen suka sha a bauta ta sa sun canja halayensu ne? Jehobah ya manta da su ne gaba ɗaya? Zai yarda su dawo ƙasarsu ne kuma su sake bauta masa?

“Na Tuba”

Sa’ad da mutanen suka fahimci cewa sun yi kuskure, sai suka tuba. Jehobah ya lura cewa sun tuba da gaske. Dubi yadda Jehobah ya kwatanta halin da Isra’ilawan da aka kai bauta suke ciki, waɗanda a dunƙule aka kira su Ifraimu.

“Hakika na ji Ifraimu yana kuka domin kansa,” in ji Jehobah. (Aya ta 18) Ya ji Isra’ilawa suna kuka domin sakamakon zunubin da suka yi. Furucin nan “kuka domin kansa” yana nufin “rawar jiki” in ji wata masaniya. Suna kama ne da yaron da ya iskance amma daga baya ya zo yana girgiza kansa yana da-na-sani saboda irin wahalar da ya jawo wa kansa kuma yana begen komawa gida domin ya ci gaba da yin rayuwa mai kyau da yake yi a dā. (Luka 15:11-17) Mene ne mutanen suka ce?

“Kā fore ni . . . kamar ɗan maraƙi wanda ba ya saba da karkiya ba.” (Aya ta 18) Mutanen sun yarda cewa sun cancanci horon da aka yi musu. Balle ma, suna kama ne da ɗan maraƙin da bai saba da karkiya ba. Wannan kamantawar wataƙila tana nufin cewa suna kama ne da ɗan maraƙin da aka yi wa tsinke domin yana gwagwagwa da karkiyar da aka ɗora masa, in ji wani littafin bincike.

‘Juyar da ni, zan kuwa juyu: gama kai ne Ubangiji Allahna.’ (Aya ta 18) Mutanen sun dawo cikin hankalinsu, kuma suka nemi gafara daga Allah. Sun bi tafarkin zunubi, amma yanzu suna roƙonsa ya nuna musu rahama. Wata fassara ta ce: “Kai ne Allahnmu—muna roƙonka ka bari mu dawo gida.”—Contemporary English Version.

‘Na ji kunya, . . . har na damu.’ (Aya ta 19) Mutanen sun yi nadama saboda zunubin da suka yi. Sun amsa laifinsu. Sun sunkuyar da kansu saboda kunya da baƙin ciki.—Luka 15:18, 19, 21.

Isra’ilawan sun tuba. Sun yi baƙin ciki sosai, sun gaya wa Allah zunuban da suka yi, kuma sun tuba. Tuban da suka yi zai sanyaya zuciyar Allah kuwa? Zai bari su sake komawa ƙasarsu?

‘Hakika Zan Yi Masa Jin Ƙai’

Jehobah yana da dangantaka ta musamman da Isra’ilawa. Ya ce: “Uba ni ke ga Isra’ila, Ifraimu kuma ɗan fārina ne.” (Irmiya 31:9) Akwai mahaifi mai ƙauna da zai ƙi marabtar ɗansa da ya tuba? Da kyar! Dubi abin da Jehobah ya ce game da yadda yake ji da mutanensa.

“Ifraimu ɗana ne ƙaunatacena? Ɗan lele ne? Gama gwargwadon zarginsa da ni ke yi, gwargwadon ƙara tunawa da shi ni ke yi da anniya.” (Aya ta 20) Waɗannan kalmomi ne masu daɗi! Kamar mahaifin da ke ƙaunar ’ya’yansa amma ba ya sakaci, Allah ya yi wa ’ya’yansa faɗa, kuma ya sha ja musu kunne game da zunuban da suke aikatawa. Sa’ad da suka ƙi jin abin da ya ce, ya sa an kai su zaman bauta, wato, ya sa sun bar ƙasarsu. Ko da yake ya yi musu horo, bai mance da su ba. Ba zai taɓa yin hakan ba. Uban da ke ƙaunar yaransa ba zai taɓa mancewa da su ba. Amma, yaya Jehobah ya ji sa’ad da ya ga cewa yaransa sun tuba da gaske?

“Zuciyata tana wahala a kansa: hakika zan yi masa jinƙai.” (Aya ta 20) Jehobah yana begen sake ganin yaransa. Tuban da suka yi ya ratsa zuciyarsa kuma yana son su sake soma bauta masa. Kamar mahaifin da ke misalin da Yesu ya ba da, na ɗa mubazzari, Jehobah “ya yi juyayi na tausayi” kuma yana begen marabtar ’ya’yansa sa’ad da suka dawo gida.—Luka 15:20.

“Ya Jehobah Ka Bar Ni In Dawo Gida”

Kalmomin da ke Irmiya 31:18-20 sun ba mu ƙarin haske a kan irin tausayin da Jehobah yake da shi. Allah ba ya mantawa da waɗanda suka taɓa bauta masa. Idan irin waɗannan mutanen suna son su sake soma bauta masa fa? Allah “mai-hanzarin gafartawa” ne. (Zabura 86:5) Ba zai taɓa yin watsi da waɗanda suka tuba da gaske ba. (Zabura 51:17) Akasin haka, yana farin cikin sake yi musu maraba zuwa cikin ƙungiyarsa.—Luka 15:22-24.

Matar da aka ambata a farkon talifin nan ta ɗauki mataki don ta sake soma bauta wa Jehobah kuma ta ziyarci ikilisiyar Shaidun Jehobah da ke inda take da zama. Da farko, tana bukatar ta daina yin tunani marar kyau da take yi game da kanta. Ta ce, “Na ji kamar ban cancanci bauta wa Jehobah ba.” Amma dattawan ikilisiya sun ƙarfafa ta kuma sun taimaka mata ta sake daidaita dangantakarta da Jehobah. Cike da godiya, ta ce, “Ina farin ciki sosai cewa Jehobah ya ba ni damar dawowa cikin ƙungiyarsa!”

Idan ka taɓa bauta wa Jehobah kuma kana tunanin sake soma bauta masa, muna gayyatar ka ka ziyarci ikilisiyar Shaidun Jehobah da ke yankin da kake. Ka tuna cewa Jehobah yana nuna tausayi da jin ƙai sa’ad da waɗanda suka tuba suka roƙe shi, “Muna roƙon ka ka bari mu dawo gida.”

[Hasiya]

a Ƙarnuka kafin hakan, a shekara ta 997 K.Z., an raba Isra’ilawa zuwa dauloli biyu. Ɗayan daular ita ce Yahuda, wadda ta ƙunshi ƙabilu biyu ta kudu. Daula ta biyu ta ƙunshi ƙabilu goma a Arewancin Isra’ila, waɗanda ake kiransu Ifraimu, domin ƙabilar Ifra’imu ce mafi yawa a cikinsu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba