Ka Yi Gaba Gaɗi Irin Na Irmiya
“Ka yi sauraro ga Ubangiji: Ka ƙarfafa, ka bar zuciyarka ta ɗauki ƙarfin rai; I, ka yi sauraro ga Ubangiji.”—ZABURA 27:14.
1. Wace albarka ce mai yawa Shaidun Jehovah suke morewa?
SHAIDUN JEHOVAH suna cikin aljanna ta ruhaniya. (Ishaya 11:6-9) A cikin wannan duniya da ta wahala, suna zama cikin mahalli na musamman na ruhaniya tare da ’yan’uwa Kiristoci cikin salama da juna da kuma Jehovah Allah. (Zabura 29:11; Ishaya 54:13) Kuma aljannarsu ta ruhaniya tana girma. Dukan waɗanda suke ‘yin nufin Allah da ransu’ suna tallafa mata sosai. (Afisawa 6:6) Ta yaya? Ta yin rayuwa da ke daidai da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ta koya wa mutane su yi hakan, suna gayyatarsu su sa hannu cikin albarka mai yawa ta wannan aljanna.—Matta 28:19, 20; Yohanna 15:8.
2, 3. Menene Kiristoci na gaskiya suke bukatar su jimre masa?
2 Amma, zamanmu cikin aljanna ta ruhaniya ba ya nufin cewa ba za mu jimre wa gwaji ba. Har ila mu ajizai ne kuma muna shan wahalar ciwo, tsufa, da kuma mutuwa. Ban da haka, muna ganin cikar annabce-annabce game da “kwanaki na ƙarshe.” (2 Timothawus 3:1) Dukan mutane suna shan wahalar yaƙe-yaƙe, yin laifi, yunwa, waɗannan ma suna shafan Shaidun Jehovah.—Markus 13:3-10; Luka 21:10, 11.
3 Ban da dukan wannan, mun sani sarai cewa a waje da mahalli na aljanna ta ruhaniya, muna fuskantar iskar hamayya. Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi: “Domin ku ba na duniya ba ne, amma ni na zaɓe ku daga cikin duniya, saboda wannan duniya tana ƙinku. Ku tuna da magana wadda na faɗa muku, Bawa ba ya fi ubangijinsa girma ba. Idan suka yi mini tsanani, su a yi muku tsanani kuma.” (Yohanna 15:18-21) Haka ma abubuwa suke a yau. Har ila yawancin mutane ba sa fahimtar ko kuma daraja irin sujjadarmu. Wasu sukan yi sūka, su yi ba’a, ko kuma—su ƙi mu—yadda Yesu ya gargaɗe mu. (Matta 10:22) Sau da yawa muna zama waɗanda ake yin ƙarya game da su da kuma tsegumi a hanyar watsa labarai. (Zabura 109:1-3) Hakika, dukanmu muna fuskantar yanayi masu wuya, don haka kuma wasunmu za su iya yin sanyin gwiwa. Ta yaya za mu iya yin jimiri?
4. Daga ina muke neman taimako don mu jimre?
4 Jehovah zai taimake mu. Mai Zabura da aka hure ne ya rubuta: “Masifu na mai-adalci dayawa su ke: amma Ubangiji ya kan tsamarda shi daga cikinsu duka.” (Zabura 34:19; 1 Korinthiyawa 10:13) Yawancinmu za mu iya tabbatar cewa sa’ad da muka yi gaba gaɗi wurin Jehovah, yana ba mu ƙarfi mu jimre wa kowacce wahala. Ƙaunar da muke masa da farin ciki da ke gabanmu ne ke taimakonmu mu yaƙi sanyin gwiwa da kuma tsoro. (Ibraniyawa 12:2) Saboda haka, a lokacin wahala, mu ci gaba da tsayawa da ƙarfi.
Kalmar Allah ta Ƙarfafa Irmiya
5, 6. (a) Waɗanne misalai muke da su na masu bauta da suka iya jimrewa? (b) Yaya Irmiya ya yi da aka kira shi ya zama annabi?
5 Duk cikin tarihi, bayin Jehovah masu aminci sun yi farin ciki duk da yanayi na wahala. Wasu sun rayu a lokacin hukunci sa’ad da Jehovah ya zartar da fushinsa a kan marasa aminci. Irmiya da kalilan tsaransa suna cikin waɗannan masu bauta masu aminci, da kuma Kiristoci na ƙarni na farko. An rubuta waɗannan misalai cikin Littafi Mai Tsarki don su ƙarfafa mu, kuma za mu daɗa koyo ta yin nazarinsu. (Romawa 15:4) Alal misali, ka yi la’akari da Irmiya.
6 Da yake yaro, an kira Irmiya zuwa hidima ta annabi a Yahuda. Wannan ba aiki ba ne mai sauƙi. Mutane da yawa suna bauta wa allolin ƙarya. Ko da yake Yosiya, wanda shi ne sarki sa’ad da Irmiya ya fara hidimarsa mai aminci, dukan sarakuna da suka bi bayansa marasa aminci ne, kuma yawancin waɗanda suke koyar da jama’ar—annabawa da firistoci—ba sa bin gaskiya. (Irmiya 1:1, 2; 6:13; 23:11) To, yaya Irmiya ya ji sa’ad da Jehovah ya kira shi ya zama annabi? Ya tsorata! (Irmiya 1:8, 17) Irmiya ya tuna da yadda ya ji a farko: “Na ce, Ai, Ubangiji Yahweh! ga shi, ni ba ni iya magana: gama ni yaro ne.”—Irmiya 1:6.
7. Yaya mutanen yankin da Irmiya yake wa’azi suke, kuma yaya ya ji?
7 Yankin da Irmiya yake, masu taurin kai ne, sau da yawa ya shaida hamayya ƙwarai. A wani lokaci Pashhur, firist ya mare shi kuma ya sa aka sa shi a mari. Irmiya ya rubuta yadda ya ji a lokacin: “Na ce, Ba ni ambaton [Jehovah], ba ni ƙara faɗin magana cikin sunansa.” Wataƙila kai ma a wani lokaci ka taɓa jin haka—ka so ka kasala. Ka lura da abin da ya taimake Irmiya ya nace. Ya ce: “Cikin zuciyata in ji [kalmar Allah, ko kuma saƙo] kamar wuta mai-ƙonewa a kulle cikin ƙasusuwana, in gaji kuma da haƙuri, in kasa jimrewa.” (Irmiya 20:9) Maganar Allah haka take shafanka?
Abokan Irmiya
8, 9. (a) Wane kumamanci ne annabi Uriya yake da shi, da wane sakamako? (b) Me ya sa Baruch ya yi sanyin gwiwa, kuma ta yaya aka taimake shi?
8 Irmiya ba shi kaɗai ba ne a aikinsa na annabci. Yana da abokai, kuma lallai wannan ya ƙarfafa shi. Amma, a wasu lokatai abokansa sun yi wauta. Alal misali, wani abokinsa annabi mai suna Uriya ya taƙure a idar da saƙonnin faɗaka game da Urushalima da kuma Yahuda “daidai da maganar Irmiya duka.” Sa’ad da Sarki Yehoyakim ya umurta a kashe Uriya, domin tsoro annabin ya gudu zuwa Masar. Amma bai tsira ba. Mutanen sarki suka bi shi, suka kama shi kuma suka mai da shi Urushalima, inda aka kashe shi. Lallai wannan zai sa Irmiya fargaba!—Irmiya 26:20-23.
9 Wani abokin Irmiya shi ne Baruch, sakatarensa. Baruch ya tallafa wa Irmiya da kyau, amma a wani lokaci ya kauce a daidaita a ruhaniya. Ya soma gunaguni yana cewa: “Kaitona yanzu! gama Ubangiji ya daɗa baƙinciki a kan azabata; na gaji da nishina, ban sami wani hutu ba.” Baruch ya yi sanyin gwiwa, bai ga darajar abubuwa na ruhaniya kuma ba. Duk da haka, Jehovah ya yi masa gargaɗi mai kyau, kuma aka yi masa gyara. Sai aka tabbatar masa cewa za ya tsira wa halakar Urushalima. (Irmiya 45:1-5) Lallai Irmiya ya sami ƙarfafa sa’ad da Baruch ya daidaita ruhaniyarsa!
Jehovah Ya Tallafa wa Annabinsa
10. Waɗanne alkawura na tallafawa ne Jehovah ya yi wa Irmiya?
10 Abu mafi muhimmanci shi ne, Jehovah bai yashe Irmiya ba. Ya fahimci yadda annabinsa yake ji, ya ƙarfafa kuma ya tallafa masa yadda ya kamata. Alal misali, a farawar hidimar Irmiya sa’ad da ya furta shakka game da gwanintarsa, Jehovah ya gaya masa: “Kada ka ji tsoronsu: gama ina tare da kai domin in cece ka, in ji Ubangiji.” Bayan ya gaya wa annabinsa game da aikinsa, Jehovah ya ce: “Za su yi yaƙi da kai; amma ba za su yi nasara da kai ba: gama ina tare da kai, in ji Ubangiji, domin in cece ka.” (Irmiya 1:8, 19) Abin ta’aziyya kuwa! Jehovah kuma ya cika maganarsa.
11. Ta yaya muka sani cewa Jehovah ya cika alkawarinsa ya tallafa wa Irmiya?
11 Saboda haka, bayan da aka saka shi cikin mari kuma aka yi masa ba’a, Irmiya da gaba gaɗi ya ce: “Ubangiji yana tare da ni, ƙaƙarfa ne mai-ban tsoro: domin wannan masu-jan raina za su yi tuntuɓe, ba za su rinjaya ba: za su kunyata ƙwarai.” (Irmiya 20:11) A shekarun da suka biyo baya da aka nemi a kashe Irmiya, Jehovah ya ci gaba da kasancewa tare da shi, kamar Baruch, Irmiya ya tsira wa halakar Urushalima ’yantacce, sa’in nan kuma waɗanda suka tsananta masa da waɗanda suka yi banza da gargaɗinsa suka halaka ko kuma an kai wasu Babila.
12. Duk da dalilan yin sanyin gwiwa, me ya kamata mu tuna?
12 A yau, kamar Irmiya, Shaidun Jehovah da yawa suna jimre wa wahala. Kamar yadda aka ambata ɗazu, ajizancinmu ne ke jawo mana wasu wahala, wasu kuma don rikicewar wannan duniyar ce, har ila wasu daga waɗanda suke hamayya da aikinmu ne. Irin wannan wahalar abin sanyin gwiwa ne. Kamar Irmiya, za mu kai lokacin da za mu ji kamar mu daina hidimar. Hakika, daidai ne mu yi sanyin gwiwa a wasu lokatai. Sanyin gwiwa yana gwada yadda yawan ƙaunarmu ga Jehovah take. Saboda haka, bari mu dage kada mu yarda sanyin gwiwa ya sa mu bar hidimar Jehovah yadda Uriya ya yi. Maimako, bari mu yi koyi da Irmiya kuma mu yi gaba gaɗin cewa Jehovah zai tallafa mana.
Yadda Za a Yaƙi Sanyin Gwiwa
13. Ta yaya za mu bi misalan Irmiya da Dauda?
13 Irmiya yana magana da Jehovah Allah kullum, yana gaya masa yadda yake ji kuma yana roƙonsa ya ƙarfafa shi. Wannan misali ne mai kyau da ya kamata mu bi. Dauda na dā ma ya biɗi samun ƙarfi wajen wannan Tushen, ya rubuta: “Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga zancena, Ka lura da tunanina. Ka saurari muryar kukata, ya Sarkina, Allahna: Gama a gareka ni ke yin addu’a.” (Zabura 5:1, 2) Hurarren labarin rayuwar Dauda ya nuna cewa sau da sau Jehovah ya amsa addu’o’insa na neman taimako. (Zabura 18:1, 2; 21:1-5) A wannan hanyar ma, sa’ad da muke fuskantar matsi ko kuma matsalolin da kamar sun sha kanmu, abin ta’aziyya ne mu juya wajen Jehovah cikin addu’a mu gaya masa dukan zuciyarmu. (Filibbiyawa 4:6, 7; 1 Tassalunikawa 5:16-18) Jehovah yana sauraronmu. Yana kuma tabbatar mana cewa ‘yana kula da mu.’ (1 Bitrus 5:6, 7) Amma, ba zai dace mu yi addu’a ga Jehovah sai kuma mu ƙi sauraron abin da ya ce ba.
14. Yaya maganar Jehovah ta shafi Irmiya?
14 Yaya Jehovah yake magana da mu? Ka sake yin la’akari da Irmiya. Tun da yake Irmiya annabi ne, Jehovah ya yi magana da shi kai tsaye. Irmiya ya kwatanta yadda maganar Allah ta motsa zuciyarsa: “Aka iske maganarka, na kuwa ci su: zantattukanka sun zama mini murna da farinciki na zuciyata: gama an kira ni da sunanka, ya Ubangiji Allah mai-runduna.” (Irmiya 15:16) Hakika, Irmiya ya yi farin ciki cewa an kira sunan Allah game da shi, kuma Kalmominsa suna da daraja ga annabin. Saboda haka, kamar manzo Bulus, Irmiya yana ɗokin ya sanar da saƙon da aka ba shi.—Romawa 1:15, 16.
15. Ta yaya za mu shuka maganar Jehovah cikin zukatanmu, kuma menene zai sa mu ƙudura kada mu yi shuru?
15 Ba wani cikinmu da Jehovah yake magana da shi kai tsaye. Amma, muna da maganar Allah a shafofin Littafi Mai Tsarki. Shi ya sa, idan muna nazarinmu na Littafi Mai Tsarki kuma muna bimbini ƙwarai a kan abin da muka koya, maganar Allah za ta zama “murna da farinciki na” zuciyarmu mu ma. Kuma za mu yi farin cikin cewa muna ɗauke da sunan Jehovah sa’ad da muke gaya wa mutane maganarsa. Kada mu manta da cewa a yau babu mutane da suke shelar sunan Jehovah a duniya. Shaidunsa ne kawai suke sanar da bisharar Mulkin Allah da aka kafa kuma su suke koyar da masu tawali’u yadda za su zama almajiran Yesu Kristi. (Matta 28:19, 20) Lallai mu masu albarka ne! Yaya za mu yi shuru game da abin da Jehovah ya ba mu?
Mu Tsare Kanmu Daga Muguwar Tarayya
16, 17. Yaya Irmiya yake ɗaukan tarayya, kuma yaya za mu yi koyi da shi?
16 Irmiya ya rubuta wani abin da ya taimake shi ya yi gaba gaɗi. Ya ce: “Ban zauna a cikin taron masu-nishatsi ba, ban kuwa yi murna ba: na zauna ni kaɗai domin hannunka; gama ka cika ni da haushi.” (Irmiya 15:17) Irmiya ya so ya zauna shi kaɗai maimakon abokansa su ɓata shi. Mu ma a yau muna yin hakan. Ba ma manta da gargaɗin manzo Bulus na cewa “zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki,” har ma su ɓata halaye masu kyau da da daɗewa muke da shi.—1 Korinthiyawa 15:33.
17 Muguwar tarayya za ta iya sa ruhun duniya ya ɓata tunaninmu. (1 Korinthiyawa 2:12; Afisawa 2:2; Yaƙub 4:4) Saboda haka, bari mu koyar da hankulanmu mu san muguwar tarayya kuma mu ƙi su sarai. (Ibraniyawa 5:14) Da Bulus yana da rai a duniya a yau, me kake tsammani zai gaya wa Kirista da yake kallon siliman na lalata ko kuwa da ake mugunta ciki? Yaya zai yi gargaɗi wa ɗan’uwa wanda yake abokantaka da baƙi da bai sani ba a Intane? Yaya zai ɗauki Kirista da yake yin sa’o’i yana wasan bidiyo ko kuma yana kallon telibijin amma ba ya nazari mai kyau na kansa?—2 Korinthiyawa 6:14b; Afisawa 5:3-5, 15, 16.
Ka Ci Gaba da Zama Cikin Aljanna ta Ruhaniya
18. Menene zai taimake mu mu kasance da ƙarfi a ruhaniya?
18 Muna daraja aljannarmu ta ruhaniya. Babu abin da yake kama da ita a duniya a yau. Har marasa bi ma suna magana game da ƙauna, kulawa, da alherin da Kiristoci suke wa juna. (Afisawa 4:31, 32) Duk da haka, muna bukatar mu yaƙi sanyin gwiwa yanzu fiye da dā. Tarayya mai kyau, addu’a, da kuma hali mai kyau na nazari zai iya taimakonmu mu kasance da ƙarfi a ruhaniya. Za su ƙarfafa mu mu fuskanci gwaji da gaba gaɗi wajen Jehovah.—2 Korinthiyawa 4:7, 8.
19, 20. (a) Menene zai taimake mu mu jimre? (b) Talifi na gaba game da su wanene, kuma su wa za su amfana a ciki?
19 Kada mu yarda wa waɗanda suka ƙi saƙonmu na Littafi Mai Tsarki su tsoratar da mu kuma su sa mu bar bangaskiyarmu. Kamar magabta da suka tsananta wa Irmiya, waɗanda suke fāɗa da mu suna fāɗa ne da Allah. Ba za su yi nasara ba. Jehovah wanda ya fi magabtanmu ƙarfi ya gaya mana: “Ka yi sauraro ga Ubangiji: Ka ƙarfafa, ka bar zuciyarka ta ɗauki ƙarfin rai; I, ka yi sauraro ga Ubangiji.” (Zabura 27:14) Bari kada mu kasala a yin nagarta da yake muna sauraron Jehovah da dukan zuciyarmu. Bari mu yi gaba gaɗi kamar Irmiya da Baruch, za mu girbe idan ba mu kasala ba.—Galatiyawa 6:9.
20 Yin yaƙi da sanyin gwiwa kokawa ce da Kiristoci da yawa za su ci gaba da yi. Amma, matasa suna fuskantar ƙalubale na musamman. Ko da yake suna da zarafi masu kyau. Talifi na gaba zai bayyana wannan ga matasa da suke tsakaninmu. Abin marmari ne ga iyaye da kuma dukan manya da suka keɓe kansu cikin ikilisiya da za su iya tallafa wa matasa a cikin ikilisiya ta kalmomi, misali, da kuma taimako na kai tsaye.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa za mu yi tsammanin yanayi na sanyin gwiwa, kuma a wajen wa ya kamata mu nemi taimako?
• Ta yaya ne Irmiya ya yi nasara da sanyin gwiwa duk da cewa aikinsa mai wuya ne?
• Menene zai sa zukatanmu ‘murna da farin ciki’ ko a yanayi mai wuya ma?
[Hoto a shafi na 17]
Irmiya yana jin cewa shi yaro ne kuma bai san kome ba ya zama annabi
[Hoto a shafi na 18]
Ko da an tsananta masa, Irmiya ya sani cewa Jehovah yana tare da shi “ƙaƙarfa ne mai-ban tsoro”