Ka Yi Tsaro Yadda Irmiya Ya yi
“Ni [Jehobah] ina yin tsaro game da maganata domin in cika ta.”—IRM. 1:12, NW.
1, 2. Me ya sa aka kwatanta yadda Jehobah yake “yin tsaro” da itacen almond?
ANA sanyi a ƙasar Lebanon da Isra’ila a watannin Janairu da Fabrairu. Itatuwa ba sa yin furanni a lokacin. Amma itacen almond yana yin furanni. Yana da kyakkyawan furanni masu launin hoda da kuma masu farin kala. Yana ɗaya daga cikin itatuwa na farko da suke yin furanni kafin lokacin zafi. Saboda haka, sunansa a Ibrananci yana nufin “mai farkawa.”
2 Sa’ad da Jehobah ya naɗa Irmiya a matsayin annabinsa, an yi amfani da yadda wannan itacen almond yake yin furanni don ya kwatanta wani batu mai muhimmanci. Da ya soma hidimarsa, an nuna wa annabin tsiron itacen. Me hakan yake nufi? Jehobah ya bayyana: “Ni ina yin tsaro game da maganata domin in cika ta.” (Irm. 1:11, 12) Kamar yadda itacen almond yakan “tashi” da wuri, hakan ma Jehobah a alamance yakan “tashi da wuri” don ya aiki annabawansa su yi wa mutanensa kashedi game da hukuncin da za a yi wa marasa biyayya. (Irm. 7:25) Kuma ba zai huta ba, zai ci gaba da ‘kasancewa a faɗake’ har sai an cika maganarsa ta annabci. Jehobah ya hukunta al’ummar ’yan ridda na Yahuda a shekara ta 607 K.Z., daidai a kan lokaci.
3. Za mu kasance da wane tabbaci game da Jehobah?
3 Hakazalika a yau, Jehobah yana a faɗake, yana mai da hankali ga yin nufinsa. Ba zai yiwu ya ƙi cika kalmarsa ba. Ta yaya yadda Jehobah yake yin tsaro yake shafanka? Shin ka gaskata cewa a wannan shekara ta 2011, Jehobah yana “yin tsaro” ga cikar alkawarinsa? Idan muna shakkar tabbatattun alkawuran Jehobah, yanzu ne lokacin da ya kamata mu farka daga barci a ruhaniya. (Rom. 13:11) A matsayin annabin Jehobah, Irmiya ya yi tsaro. Bincika yadda da kuma dalilin da ya sa Irmiya ya kasance a faɗake ga yin aikin da Allah ya sa shi zai taimake mu mu fahimci yadda za mu nace ga yin aikin da Jehobah ya ba mu.
Saƙo na Gaggawa
4. Waɗanne ƙalubale ne Irmiya ya fuskanta sa’ad da yake idar da saƙonsa, kuma me ya sa ya kasance da gaggawa?
4 Wataƙila Irmiya yana ɗan shekara ashirin da biyar sa’ad da Jehobah ya ba shi aikin yin tsaro. (Irm. 1:1, 2) Amma ya ji kamar shi ƙaramin yaro ne, bai cancanta ya yi magana da dattawan al’ummar ba, mutane da suka manyanta kuma suna da matsayi. (Irm. 1:6) Yana ɗauke da hukunce-hukunce masu tsanani da masu ban tsoro da zai sanar, musamman ga firistoci da annabawan ƙarya da masarauta da kuma waɗanda suke ‘kama gabansu’ kuma suka koya rashin aminci “tuttur.” (Irm. 6:13; 8:5, 6) Za a halaka haikali mai girma na Sulemanu, wanda ya kasance cibiyar bauta ta gaskiya kusan ƙarnuka huɗu. Ƙasar Urushalima da Yahuda za su kasance kango, kuma za a kwashe mutanenta zuwa bauta. A bayane yake cewa, saƙon da aka ba Irmiya ya idar na gaggawa ne!
5, 6. (a) Yaya Jehobah yake amfani da rukuni na Irmiya a yau? (b) Za mu mai da hankali a kan mene ne a nazarinmu?
5 A zamaninmu, Jehobah cikin ƙauna ya yi wa mutane tanadi na rukunin Kiristoci shafaffu waɗanda suke aikatawa a matsayin masu tsaro na alama don su ba da kashedi game da hukuncin da zai wa wannan duniyar. A cikin shekaru da yawa, wannan rukuni na Irmiya suna yi wa mutane kashedi su mai da hankali ga lokacin da muke ciki. (Irm. 6:17) Littafi Mai Tsarki ya nanata cewa Jehobah, Mai-Kula da Lokaci Mai Girma ne, kuma ba ya jinkiri. Ranarsa za ta zo daidai kan lokaci, a sa’ar da ’yan Adam ba su sa zato ba.—Zaf. 3:8; Mar. 13:33; 2 Bit. 3:9, 10.
6 Ka tuna cewa Jehobah yana a faɗake kuma zai kawo sabuwar duniyarsa ta adalci a daidai lokacinsa. Ya kamata sanin hakan ya motsa waɗanda suke rukuni na Irmiya kuma ya taimaka wa ’yan’uwansu da suka keɓe kansu su yi tsaro ga saƙonsu da yake daɗa kasancewa da gaggawa. Yaya hakan yake shafanka? Yesu ya nuna cewa dukanmu muna bukatar mu goyi bayan Mulkin Allah. Bari mu bincika halaye uku da suka taimaka wa Irmiya ya yi tsaro ga aikinsa da kuma za su taimake mu mu yi hakan.
Ƙauna ga Mutane
7. Ka bayyana yadda ƙauna ta motsa Irmiya ya yi wa’azi duk da yanayi mai wuya.
7 Mene ne ya motsa Irmiya ya yi wa’azi duk da yanayi mai wuya da yake ciki? Yana ƙaunar mutane. Irmiya ya san cewa makiyayan ƙarya suna jawo yawan matsala da mutanen suke fuskanta. (Irm. 23:1, 2) Sanin wannan ya taimaka masa ya yi aikinsa da ƙauna da kuma juyayi. Yana son mutanen ƙasarsu su ji maganar Allah kuma su rayu. Ya damu ƙwarai da har ya yi kuka don masifar da za ta faɗo musu. (Karanta Irmiya 8:21; 9:1.) Littafin Makoki ya nuna ƙaunar Irmiya da kuma kulawarsa ga sunan Jehobah da mutane. (Mak. 4:6, 9) Sa’ad da ka ga mutane “suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi” a yau, kana son ka kawo musu labari mai ban ta’aziyya na Mulkin Allah kuwa?—Mat. 9:36.
8. Mene ne ya nuna cewa wahala bai sa Irmiya baƙin ciki ba?
8 Irmiya ya sha wahala a hannun mutanen da yake son ya taimaka wa, duk da haka bai rama ba ko kuma ya yi fushi. Shi mai tsawon jimrewa ne da kuma mai kirki, har ga Sarki Zadakiya mai ha’inci! Bayan da Zadakiya ya ce a kashe shi, har ila Irmiya ya roƙe shi ya yi biyayya ga muryar Jehobah. (Irm. 38:4, 5, 19, 20) Shin muna ƙaunar mutane sosai yadda Irmiya ya yi?
Ƙarfin Zuciya da Allah Yake Ba Da
9. Yaya muka san cewa gaba gaɗin Irmiya daga wurin Allah ne?
9 Irmiya ya yi ƙoƙari ya ja da baya a lokaci na farko da Jehobah ya yi magana da shi. Daga wannan mun ga cewa bai gāji gaba gaɗi da dagewa da ya ci gaba da nunawa ba. Da yake ya dogara ga Allah sosai ne ya sa Irmiya ya kasance da ƙarfi a lokacin hidimarsa a matsayin annabi. Hakika, Jehobah yana tare da annabin kamar ‘ƙaƙarfa mai-ban tsoro’ da yake ya tallafa wa Irmiya kuma ya ba shi ƙarfi don ya yi aikinsa. (Irm. 20:11) Irmiya yana da gaba gaɗi da kuma ƙarfin zuciya sosai da a lokacin hidimar Yesu a duniya, wasu sun ɗauki cewa Yesu Irmiya ne da ya sake dawowa duniya!—Mat. 16:13, 14.
10. Me ya sa za a iya ce shafaffu da suka rage suna ‘bisa kan al’ummai, da mulkoki’?
10 A matsayin “Sarkin al’ummai” Jehobah ya aiki Irmiya ya idar da saƙon hukunci ga al’ummai da mulkoki. (Irm. 10:6, 7) Amma a wane azanci ne shafaffu da suka rage suke “bisa kan al’ummai, da mulkoki”? (Irm. 1:10) Kamar annabin na dā, Mamallakin sararin samaniya ya ba rukuni na Irmiya aiki. Da hakan an ba bayin Allah shafaffu izinin yi wa dukan al’ummai da mulkoki na duniya kashedi. Da yake Allah, Maɗaukaki Duka ya ba su iko kuma suna yin amfani da yaren da ya fita sarai na hurarriyar Kalmarsa, rukuni na Irmiya ya sanar cewa za a tumɓuke al’ummai da mulkoki na zamanin nan kuma a halaka su a lokacin da Allah ya ga ya dace da kuma a hanyar da ya zaɓa. (Irm. 18:7-10; R. Yoh. 11:18) Rukuni na Irmiya ya ƙuduri aniya cewa ba zai daina aikin da Allah ya ba su na sanar da saƙon hukuncin Jehobah a dukan duniya ba.
11. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da wa’azi babu fasawa sa’ad da muke fuskantar yanayi mai wuya?
11 Ba sabon abu ba ne mu yi sanyin gwiwa a wani lokaci da muke fuskantar hamayya da ƙiyayya ko kuma yanayi mai wuya ba. (2 Kor. 1:8) Amma kamar Irmiya, bari mu ci gaba da aikin. Kada ka yi sanyin gwiwa. Bari kowannenmu ya ci gaba da yin addu’a ga Allah, ya dogara a gare shi, kuma ya kasance da “ƙarfin hali” yayin da yake biɗan taimakonsa. (1 Tas. 2:2) A matsayin masu bauta ta gaskiya, dole ne mu ci gaba da yin tsaro ga hakkin da Allah ya ba mu. Muna bukatar mu ƙuduri aniya mu ci gaba da wa’azi ba tare da fasawa ba game da halakar Kiristendam, waɗanda suke wakiltar mutane marasa aminci na Urushalima. Rukuni na Irmiya za ya yi shelar “shekara ta alherin Ubangiji,” da kuma “ranar sakaiya ta Allahnmu.”—Isha. 61:1, 2; 2 Kor. 6:2.
Farin Ciki da Dukan Zuciya
12. Me ya sa za mu iya kammala cewa Irmiya ya ci gaba da farin ciki, kuma mene ne ainihi ya taimake shi ya yi hakan?
12 Irmiya ya yi farin ciki a aikinsa. Ya gaya wa Jehobah: “Aka iske maganarka, na kuwa ci su: zantattukanka sun zama mani murna da farinciki na zuciyata: gama an kira ni da sunanka, ya Ubangiji.” (Irm. 15:16) Ga Irmiya, gata ne ya zama wakilin Allah na gaskiya kuma ya yi wa’azin kalmarsa. Yana da kyau mu lura cewa sa’ad da Irmiya ya mai da hankali ga ba’ar da mutanen suke masa, sai ya daina farin ciki. Sa’ad da ya juya hankalinsa zuwa ga kyaun da kuma muhimmancin saƙonsa, sai ya soma farin ciki kuma.—Irm. 20:8, 9.
13. Me ya sa cin abincin ruhaniya mai zurfi yake da muhimmanci don mu ci gaba da farin ciki?
13 Don mu ci gaba da farin ciki a aikin wa’azi a zamaninmu, muna bukatar mu ciyar da kanmu da “abinci mai-ƙarfi” na zurfafan koyarwa na Kalmar Allah. (Ibran. 5:14) Yin nazarin sosai yana ƙarfafa bangaskiya. (Kol. 2:6, 7) Yana nuna mana yadda Jehobah yake ji game da ayyukanmu. Idan muna kokawa mu nemi lokacin karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki, ya kamata mu sake bincika tsarinmu. Ko ’yan mintoci na nazari da yin bimbini kowace rana zai sa mu kusaci Jehobah kuma zai sa mu yi ‘murna da farinciki na zuciya’ yadda ya kasance a batun Irmiya.
14, 15. (a) Wane amfani ne aka samu domin Irmiya ya ci gaba da aikinsa da aminci? (b) Mene ne mutanen Allah a yau suka fahimta game da aikin wa’azi?
14 Irmiya ya yi shelar kashedin Jehobah da saƙon hukunci babu fasawa, duk da haka ya tuna da aikinsa na ‘gina da kuma dasa.’ (Irm. 1:10) Aikinsa na gina da kuma dasa ya ba da amfani. Wasu Yahudawa da kuma waɗanda ba Isra’ilawa ba sun tsira wa halakar Urushalima a shekara ta 607 K.Z. Mun san labarin Rekabawa da Ebed-melek da kuma Baruch. (Irm. 35:19; 39:15-18; 43:5-7) Waɗannan abokan Irmiya masu aminci da kuma tsoron Allah sun kwatanta waɗanda suke da begen zama a duniya a yau waɗanda suke abokantaka da rukuni na Irmiya. Rukuni na Irmiya suna farin ciki sosai wajen ƙarfafa bangaskiyar wannan “taro mai-girma.” (R. Yoh. 7:9) Haka nan ma, waɗannan masu aminci, abokan shafaffu suna samun gamsuwa sosai wajen taimaka wa mutane masu zuciyar kirki su zo ga sanin gaskiya.
15 Mutanen Allah sun fahimci cewa aikin wa’azi ba hidima kaɗai ba ce ga dukan waɗanda suka ji ba amma bautarmu ce ga Allah. Ko da mutane sun saurare mu ko babu, yin tsarkakkiyar hidima ga Jehobah ta wurin yin wa’azi yana sa mu farin ciki sosai.—Zab. 71:23; karanta Romawa 1:9.
‘Ka Yi Tsaro’ ga Aikinka!
16, 17. Ta yaya Ru’ya ta Yohanna 17:10 da kuma Habakkuk 2:3 suka nuna gaggawar kwanaki da muke ciki?
16 Lokaci na gaggawa da muke ciki yana a bayyane sa’ad da muka yi la’akari da annabcin da aka hure da ke Ru’ya ta Yohanna 17:10. Sarki na bakwai, wato, Ikon Duniya na Haɗin Amirka ya soma sarauta. Game da shi mun karanta: “Sa’anda [ikon duniya na bakwai] ya zo, zai yi kwanaki kaɗan.” Amma a yanzu “kwanaki kaɗan” ya kusan ƙarewa. Annabi Habakkuk ya ba mu wannan tabbaci game da ƙarshen wannan mugun zamani: “Gama ru’yan har yanzu da ayanannen lokacinta, . . . ka dakata mata; gama lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba.”—Hab. 2:3.
17 Ka tambayi kanka: ‘Shin rayuwata tana nuna cewa na san gaggawar kwanaki da muke ciki? Shin hanyar rayuwata tana nuna cewa ina son ƙarshen ya zo da sauri? Ko kuwa shawarwari na da abubuwan da suka fi muhimmanci a gare ni suna nuna cewa ba na son ƙarshen ya zo da sauri ko kuwa ban ma tabbata da zuwansa ba?’
18, 19. Me ya sa yanzu ba lokacin yin sanyin gwiwa ba ne?
18 Har ila rukunin masu tsaro ba su gama aikinsu ba. (Karanta Irmiya 1:17-19.) Abin farin ciki ne cewa shafaffu da suka rage suna tsayawa da ƙarfi, kamar “umudi na ƙarfe” da “birni mai ganuwa”! Sun ‘ɗaure gindinsu da gaskiya’ da yake sun ƙyale Kalmar Allah ta ƙarfafa su har sai sun gama aikin da aka ba su. (Afis. 6:14) Da irin wannan ƙudurin, waɗanda suke cikin taro mai girma suna tallafa wa rukuni na Irmiya wajen yin aikin da Allah ya ba su.
19 Yanzu ba lokaci ba ne da za mu daina ƙwazo a aikin Mulki amma mu yi la’akari da ma’anar Irmiya 12:5. (Karanta.) Dukanmu muna fuskantar gwajin da ya wajaba mu jimre. Za a iya gwada waɗannan gwaje-gwaje na bangaskiya da “masu-ƙafa” da dole za mu yi gudu tare da su. Amma, da yake “ƙunci mai-girma” yana gabatowa, dole ne mu san cewa matsaloli za su ƙaru. (Mat. 24:21) Za a iya kwatanta fama da matsaloli mafi wuya da ke nan gaba da yin tsere “da dawakai.” Don mutum ya ci gaba da yin tsere da dawakai, zai bukaci jimiri sosai. Saboda haka, yana da amfani mu jimre gwaje-gwajen da muke fuskanta a yanzu, wanda zai iya shirya mu mu jimre waɗanda za su faru a nan gaba.
20. Mene ne ka ƙuduri aniyar yi?
20 Dukanmu za mu iya yin koyi da Irmiya kuma mu yi nasara a idar da aikinmu na yin wa’azi! Halaye kamar su ƙauna, gaba gaɗi, da farin ciki sun motsa Irmiya ya yi hidimarsa da aminci na tsawon shekaru 67. Kyakkyawar itacen almond ta tuna mana cewa Jehobah zai ci gaba da ‘yin tsaro’ game da kalmarsa domin ya cika ta. Muna da dalili mai kyau na yin hakan. Irmiya ya ci gaba da ‘yin tsaro,’ mu ma za mu iya yin hakan.
Ka Tuna?
• Ta yaya ƙauna ta taimaki Irmiya ya ci gaba da ‘yin tsaro’ ga aikinsa?
• Me ya sa muke bukatar gaba gaɗi da Allah yake ba da?
• Mene ne ya taimaki Irmiya ya ci gaba da farin ciki?
• Me ya sa muke bukatar mu ci gaba da ‘yin tsaro’?
[Hotuna da ke shari na 31]
Za ka ci gaba da yin wa’azi duk da hamayya?