Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Irmiya
BALA’IN da Irmiya ya sanar zai sami mutanensa na da ban tsoro. Za a ƙone haikali mai girma da ake amfani da shi fiye da ƙarnuka uku ƙurmus. Birnin Urushalima da ƙasar Yahuda za su zama kango, za a kwashe mazaunansu zuwa bauta. Wannan da wasu shelar hukunci suna cikin littafi na biyu mafi girma a cikin Littafi Mai Tsarki, wato littafin Irmiya. Littafin ya kuma ba da labarin abin da Irmiya da kansa ya fuskanta a hidimar da ya yi da aminci na shekara 67. An shirya labarin da ke cikin littafin bisa jigo ne, ba yadda suka faru ba.
Me ya sa yake da muhimmanci mu bincika littafin Irmiya? Domin annabce-annabcensa da suka cika sun ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah da yake shi ne mai cika alkawuransa. (Ishaya 55:10, 11) Aikin annabi Irmiya da halin da mutanen suka nuna ga saƙonsa ya yi daidai da zamaninmu. (1 Korinthiyawa 10:11) Ƙari ga haka, labarin yadda Jehobah ya bi da mutanensa ya nuna halayensa kuma ya kamata hakan ya shafe mu sosai.—Ibraniyawa 4:12.
“MUTANENA SUN AIKA MUGUNTA BIYU”
(Irmiya 1:1–20:18)
Irmiya ya zama annabi a shekara ta 13 na sarautar Josiah, sarkin Yahuda, wato shekara 40 kafin a halaka Urushalima a shekara ta 607 K.Z. (Irmiya 1:1, 2) Shelar da aka yi a sauran shekaru 18 na sarautar Josiah ta fallasa muguntar Yahuda kuma ta furta hukuncin Jehobah a kanta. Jehobah ya sanar: “Zan kuma maida Urushalima tullai, . . . in maida biranen Yahuda kangaye, babu mazauni a ciki.” (Irmiya 9:11) Me ya sa? “Gama mutanena sun aika mugunta biyu” in ji shi.—Irmiya 2:13.
Saƙon ya kuma haɗa da maidowar raguwar mutanen da suka tuba. (Irmiya 3:14-18; 12:14, 15; 16:14-21) Amma, mutanen ba su yi na’am da saƙon manzon ba. Wani “waziri a cikin gidan Ubangiji” ya bugi Irmiya kuma ya saka shi cikin turu har gari ya waye.—Irmiya 20:1-3.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1:11, 12—Me ya sa aka kwatanta yadda Jehobah yake kiyaye maganarsa da “sandar itacen almond”? Itacen almond (wato ɓaure) na cikin itatuwa na farko da ke yin fure a rani. A alamance, Jehobah yana “tashi da wuri” ya aiki annabawansa su yi wa mutanensa kashedi game da hukuncinsa kuma yana ‘kiyaye maganarsa’ har ta cika.—Irmiya 7:25.
2:10, 11—Me ya sa ayyukan Isra’ilawa marasa aminci bai dace ba? Ko da al’ummai arna da ke yammacin Kittim da gabashin Kedar suna iya kawo allolin wasu al’ummai su haɗa da nasu, Isra’ilawa ba su canja allolinsu da na baƙi ba. Amma Isra’ilawa sun yasar da Jehobah, suna ɗaukaka gumaka marar rai maimakon Allah mai rai.
3:11-22; 11:10-12, 17—Me ya sa Irmiya ya haɗa masarautar ƙabilu goma ta arewa a cikin saƙonsa na hukunci, duk da cewa an mallaki Samariya a shekara ta 740 K.Z.? Ya yi haka ne domin halakar Urushalima a shekara ta 607 K.Z., ta nuna cewa Jehobah ya hukunta dukan al’ummar Isra’ila, ba Yahuda kaɗai ba. (Ezekiel 9:9, 10) Domin annabawan Allah sun ci gaba da ambata Isra’ilawa a cikin saƙonsu na maidowa bayan faɗuwar masarautar kabilu goma, hakan ya nuna cewa Urushalima tana wakiltar Yahuda da kuma masarautar kabilu goma na Isra’ila.
4:3, 4—Menene ma’anar wannan umurni? Yahudawa marasa aminci suna bukatar su shirya, su sauƙaƙa da kuma tsabtace zuciyarsu. Za su cire “lobar” zuciyarsu, wato, su kawar da tunani, tsotsuwar zuciya, da kuma muradi marar tsabta. (Irmiya 9:25, 26; Ayukan Manzanni 7:51) Suna bukatar su canja salon rayuwarsu, wato su daina yin mugunta su soma yin abin da zai kawo albarkar Allah.
4:10; 15:18—A wane azanci ne Jehobah ya ruɗi mutanensa masu taurin kai? A zamanin Irmiya, da akwai annabawa da suke “ƙaryan annabci.” (Irmiya 5:31; 20:6; 23:16, 17, 25-28, 32) Jehobah bai hana su yin shelar saƙo mai ruɗu ba.
16:16—Menene ake nufi da Jehobah zai ‘aika a yi kiran masuna dayawa’ da kuma “mafarauta dayawa”? Wannan mai yiwuwa yana nufin aika da rundunar magabta don su nemi Yahudawa marasa aminci waɗanda Jehobah zai zartar da hukuncinsa a kansu. Amma, domin abin da Irmiya 16:15 ta ce, ayar na iya nufin neman Isra’ilawa da suka tuba.
20:7—Ta yaya ne Jehobah ya yi amfani da ‘ƙarfinsa’ a kan Irmiya kuma ya ruɗe shi? Domin yana fuskantar rashin so, ƙi, da tsanantawa sa’ad da yake shelar hukuncin Jehobah, mai yiwuwa Irmiya ya ji cewa ba shi da ƙarfin ci gaba da aikin. Amma, Jehobah ya yi amfani da ƙarfinsa a kan irin wannan nufi, kuma ya ba Irmiya ikon ci gaba da aikin. Jehobah ya ruɗi Irmiya ta yin amfani da shi ya cim ma abin da annabin ya ji ba zai iya yi ba.
Darussa Dominmu:
1:8. Wani lokaci Jehobah yana ’yantar da mutanensa daga tsanantawa, wataƙila ta yin amfani da alƙalai da ba sa wariya, ta wajen canja ma’aikata masu zafin hali ya sa masu sauƙin kai, ko kuma ya ba masu bauta masa ƙarfin da za su jimre.—1 Korinthiyawa 10:13.
2:13, 18. Isra’ilawa marasa aminci sun yi abubuwa biyu marar kyau. Sun bar Jehobah, wanda shi ne tabbataccen tushe na albarka, ja-gora da kāriya. Kuma sun haƙa wa kansu randunan ruwa ta alama ta wurin neman haɗa kai da Masar da Assuriya. A zamaninmu, barin Allah na gaskiya don ilimin falsafa da hasashe da kuma siyasa na duniya zai zama kamar sake “maɓulɓular ruwaye masu-rai” ne da “randuna hudaddu.”
6:16. Jehobah ya gargaɗi mutanensa masu tawaye su dakata su bincika kansu, su koma “hanyoyi” na kakanninsu masu aminci. Bai kamata mu bincika kanmu lokaci lokaci mu ga ko muna tafiya a hanyar da Jehobah yake son mu bi ba ne ?
7:1-15. Dogara ga haikali da kuma ɗaukansa kamar wani maganin samun kāriya, bai ceci Yahudawan ba. Ya kamata mu yi tafiya bisa ga bangaskiya ba bisa ga gani ba.—2 Korinthiyawa 5:7.
15:16, 17. Kamar Irmiya za mu iya tsayayya wa sanyin gwiwa. Za mu iya yin hakan ta wurin jin daɗin yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ta wajen ɗaukaka sunan Jehobah a hidima, da kuma guje wa mugun abokai.
17:1, 2. Zunuban mutanen Yahuda ya sa hadayunsu ya zama abin da ke ɓata wa Jehobah rai. Rashin tsabta na ɗabi’a zai sa ba za a amince da hadayunmu ba.
17:5-8. Za mu dogara ga ’yan adam da kuma ƙungiyoyi idan sun aikata cikin jituwa da nufin Allah da ƙa’idodinsa. Idan ya zo ga batun ceto da tabbatacciyar salama da kuma kwanciyar rai, ya kamata mu dogara ga Jehobah kaɗai.—Zabura 146:3.
20:8-11. Bai kamata mu bar wariya, hamayya, ko tsanantawa su rage himmarmu na aikin wa’azi na Mulki ba.—Yaƙub 5:10, 11.
“SARAYADDA KANKU ƘARƘASHIN KARIYAR SARKIN BABILA”
(Irmiya 21:1–51:64)
Irmiya ya furta hukunci a kan sarakunan Yahuda huɗu na ƙarshe da annabawan ƙarya, da mugun makiyaya da kuma lalatattun firistoci. Sa’ad da yake kwatanta raguwar mutane masu aminci da ɓaure masu kyau, Jehobah ya ce: “Da alheri zan duddube su.” (Irmiya 24:5, 6) Annabce-annabce uku a sura ta 25 sun taƙaita hukunci da aka bayyana a surori na gaba.
Firistoci da annabawa sun yi ƙulli don su kashe Irmiya. Irmiya ya faɗi cewa dole ne su zama bayin sarkin Babila. Irmiya ya gaya wa Sarki Zedekiah: “Sarayadda kanku ƙarƙashin karkiyar sarkin Babila.” (Irmiya 27:12) Amma, “wanda ya watsadda Isra’ila za ya tattaro shi.” (Irmiya 31:10) Shi ya sa, aka yi wa Rekabawa alkawari. Aka saka Irmiya “cikin anguwar matsara.” (Irmiya 37:21) An halaka Urushalima, kuma aka ɗauke yawancin mazaunan zuwa bauta. Irmiya da sakatarensa, Baruk suna cikin waɗanda aka bari a baya. Duk da gargaɗin da Irmiya ya yi kada su yi hakan, mutanen da suka tsorata sun gudu zuwa Masar. Surori 46 zuwa 51 sun faɗi saƙon da Irmiya ya bayar game da al’ummai.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
22:30—Wannan dokar ta kawar da ikon Yesu Kristi ne na hawan kursiyin Dauda? (Matta 1:1, 11) A’a. Dokar ta hana tsaran Jehoiakim daga zama “bisa kursiyin Dauda . . . cikin Yahuda.” Yesu zai yi sarauta daga sama, ba daga kursiyi cikin Yahuda ba.
23:33—Menene “Kaya na Ubangiji”? A zamanin Irmiya, shela mai muhimmanci da annabin ya furta game da halakar Urushalima kaya ne mai nauyi ga mutanensa. Jehobah zai kawar da mutanen da suka ƙi yin na’am ga saƙon, da yake su kaya ne a gare shi. Hakanan ma, saƙo na Nassi game da halakar Kiristendam mai zuwa kaya ne a gare su, kuma mutanen da ba su saurari saƙon ba kaya ne mai nauyi ga Allah.
31:33—Yaya ake rubuta shari’ar Allah a cikin zuciya? Idan mutum yana son shari’ar Allah sosai da ya sa yake son yin nufin Jehobah, ana iya cewa an rubuta shari’ar Allah a zuciyarsa.
32:10-15—Menene dalilin rubuta takarda shari’a biyu game da yarjejeniya ɗaya? Ana barin ɗaya a buɗe don a riƙa bincikawa. Ɗayan da aka rufe don ta tabbatar da gaskiyar ɗayan ne da ke buɗe. Irmiya ya kafa mana misali ta wurin bin mizanan doka sa’ad da ake sha’ani da dangi da ɗan’uwa mai bi.
33:23, 24—Waɗanne ‘ƙabilu biyu’ ne ake magana a nan? Ƙabila ta farko ita ce iyalin sarauta ta zuriyar Sarki Dauda, ta biyu kuma iyalin firist ta zuriyar Haruna ce. Da yake an halaka Urushalima da haikalin Jehobah, kamar dai Jehobah ya ƙi waɗannan iyalai biyu kuma ba zai yi sarauta bisa duniya ko kuma a soma bautansa a wajen kuma ba.
46:22—Me ya sa aka kamanta muryar Masar da na maciji? Wannan na iya nufin kunyantar da Masar da aka yi domin bala’in da ta sha. Wannan kwatancin ya nuna cewa aikin banza ne alamar macijin da Fir’auna na Masar suke sakawa a kambinsu domin wai su sami kāriya daga allah na maciji mai suna Uatchit.
Darussa Dominmu:
21:8, 9; 38:19. Kafin a halaka Urushalima, Jehobah ya yi wa mazaunan Urushalima da suka ƙi tuba da suka cancanci su mutu tanadin zaɓen da za su yi. Hakika, “jinƙansa yana da girma.”—2 Samuila 24:14; Zabura 119:156.
31:34. Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa Jehobah ba ya tuna zunuban da ya yafe, kuma ya aikata da shi nan gaba!
38:7-13; 39:15-18. Jehobah ba ya mantawa da hidimarmu na aminci, da ya haɗa da “yi wa tsarkaka hidima.”—Ibraniyawa 6:10.
45:4, 5. Yadda yake a kwanaki na ƙarshe na zamanin Yahuda, “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamanin ba lokaci ba ne na neman “manyan abu” kamar arziki, matsayi, ko kuma abin duniya.—2 Timothawus 3:1; 1 Yohanna 2:17.
AN ƘONE URUSHALIMA
(Irmiya 52:1-34)
A shekara ta 607 K.Z., Zedekiah yana shekara ta 11 na sarautarsa. Sarki Nebukadnezzar na Babila ya kewaye Urushalima tun watanni 18 da suka wuce. A rana ta bakwai a cikin wata na biyar cikin shekara goma sha tara na sarautar Nebukadnezzar, Nebuzaradan shugaban matsara “ya zo” Urushalima. (2 Sarakuna 25:8) Wataƙila daga sansaninsa da ke gaban ganuwar birnin, Nebuzaradan ya bincika yanayin kuma ya shirya abin da zai yi. Kwana uku bayan haka, a cikin rana ta goma ga watan, “ya zo” ko kuma ya shiga Urushalima. Kuma ya ƙone birnin.—Irmiya 52:12, 13.
Irmiya ya ba da bayani dalla-dalla game da faɗuwar Urushalima. Kwatancinsa ya ba da dalilin makoki. Wannan kwatancin yana cikin littafin Littafi Mai Tsarki na gaba, wato, littafin Makoki.
[Hoto a shafi na 1]
Shelar Irmiya ta haɗa da hukuncin Jehobah a kan Urushalima
[Hoto a shafi na 1]
Ta yaya Jehobah ya yi amfani da ‘ƙarfinsa’ a kan Irmiya”?
[Hoto a shafi na 1]
“Kamar ’ya’yan ɓauren nan masu-kyau, haka zan kula da kwason Yahuda.”—Irmiya 24:5.