Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 pp. 24-25
  • Irmiya Bai Ja da Baya Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Irmiya Bai Ja da Baya Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Irmiya Ya Ki Ya Daina Yin Magana Game da Jehobah
    Ku Koyar da Yaranku
  • Ka Yi Gaba Gaɗi Irin Na Irmiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehobah Ya Aiki Irmiya Ya Yi Wa’azi
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Darussa Daga Littafin Irmiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 pp. 24-25

Ku Koyar Da Yaranku

Irmiya Bai Ja da Baya Ba

KA TAƁA yin sanyin gwiwa sai ka ji kamar ka ja da baya?—a Mutane da yawa suna yin hakan. Matashi Irmiya ma ya yi hakan. Amma dai, bai sa abubuwan da wasu suka ce ko kuma suka yi ya sa shi ya ja da baya ba. Bari mu yi magana game da yadda Irmiya ya zama mutum na musamman ga Allah, amma duk da haka shi ma ya ji kamar ya ja da baya.

Kafin a haifi Irmiya, Allahn gaskiya, Jehobah, ya zaɓe shi ya zama annabi don ya ja kunnen mutanen cewa ba sa bauta wa Allah. Ka san abin da Irmiya ya gaya wa Jehobah shekaru da yawa bayan haka?— “Ni ba ni iya magana: gama ni yaro ne.”

Yaya kake tsammani Jehobah ya ba da amsa ga Irmiya?— Da juyayi amma cikin iko, ya ce: ‘Kada ka ce, Ni yaro ne; gama za ka tafi wurin dukan wanda zan aike ka gareshi, iyakacin abin da zan umurce ka kuma za ka faɗi. Kada ka ji tsoronsu.’ Don me? “Gama ina tare da kai domin in cece ka,” Jehobah ya ce.—Irmiya 1:4-8.

Duk da haka, kamar yadda aka bayyana ɗazun, Irmiya ya yi sanyin gwiwa daga baya. Hakan ya faru ne domin an yi masa ba’a don yana bauta wa Allah. Ya ce: “Na zama abin dariya dukan yini, kowa yana yi mini ba’a.” Saboda haka ya yanke shawara ya ja da baya. Sai ya ce: ‘Ba ni ambaton [Jehobah], ba ni ƙara faɗin magana cikin sunansa.’ Amma ya ja da baya da gaske kuwa?

Irmiya ya ce, ‘cikin zuciyata na ji kamar wuta mai-ƙonewa a kulle cikin ƙasusuwana, na gaji kuma da haƙuri, na kasa jimrewa.’ (Irmiya 20:7-9) Ko da a wasu lokatai Irmiya yana jin tsoro, amma ƙaunarsa ga Jehobah ba za ta sa ya ja da baya ba. Bari mu ga yadda aka kāre Irmiya don bai ja da baya ba.

Jehobah ya gaya wa Irmiya ya gargaɗi mutanen cewa zai halaka Urushalima idan ba su canja halayensu ba. Sa’ad da Irmiya ya ba da gargaɗin, mutanen suka yi fushi sai suka ce: “Wannan mutum ya kamata shi mutu.” Amma, Irmiya ya roƙe su su “yi biyayya da muryar Ubangiji.” Sai ya ce: ‘Idan kun kashe ni, kun kashe mara-laifi: gama hakika Ubangiji ya aiko ni gareku.’ Kun san abin da ya faru?—

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’annan su hakimai da dukan jama’a suka faɗa wa firistoci da annabawa: suka ce, Mutumin nan ba shi da laifin da ya isa mutuwa ba; gama ya yi mana magana cikin sunan Ubangiji Allahnmu.” Don Irmiya bai ƙyale tsoro ya sa ya ja da baya ba, sai Jehobah ya kāre shi. Yanzu bari mu ga abin da ya faru da Uriah, wani annabin Jehobah, wanda ya aikata a hanya dabam.

Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Uriah ya yi annabci game da Urushalima da magana irin ta Irmiya.’ Amma sa’ad da Sarki Jehoiakim ya yi fushi sosai da Uriah, ka san abin da Uriah ya yi kuwa?— Ya ji tsoro, ya daina yin nufin Allah, sai ya gudu zuwa ƙasar Masar. Sai sarkin ya aiki mazaje su neme shi a wurin kuma su dawo da shi. Sa’ad da suka yi hakan, ka san abin da mugun sarkin ya yi?— Ya kashe Uriah da takobi!—Irmiya 26:8-24.

Me ya sa za ka ce Jehobah ya kāre Irmiya amma bai kāre Uriah ba?— Babu shakka, Irmiya ya ji tsoro, kamar Uriah, amma Irmiya bai daina bauta wa Jehobah ba kuma bai gudu ba. Bai ja da baya ba. Wane darassi ne kake gani za mu iya koya daga misalin Irmiya?— Wasu lokatai zai iya kasance da wuya mu yi biyayya da umurnin Allah, amma ya kamata mu dinga dogara da kuma yin biyayya da shi.

[Hasiya]

a Idan kana karatun ne da yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata kuma ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.

Tambayoyi:

○ Wane aiki ne Allah ya zaɓar wa Irmiya?

○ Me ya sa Irmiya ya so ya ja da baya?

○ Me ya sa aka kāre Irmiya, amma ba a kāre Uriah ba?

○ Menene ka koya daga misalin Irmiya?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba