Ka Kusaci Allah
“Ranka Zai . . . Durƙusa a Kaina”
TAWALI’U hali ne da kowa yake so. Muna son yin sha’ani da masu tawali’u. Abin baƙin ciki shi ne, samun mutane masu tawali’u a yau yana da wuya, musamman a tsakanin masu iko. Amma Jehoba fa, Mai iko bisa sararin samaniya? Shi mai tawali’u ne? Bari mu bincika abin da annabi Irmiya ya ce a Makoki 3:20, 21, NW: “Babu shakka, ranka zai tuna da ni kuma ya durƙusa a kaina. Zan tuna da hakan a zuciyata. Shi ya sa zan yi zaman jira.”
Irmiya ya rubuta littafin Makoki ne sa’ad da Isra’ilawa suke cikin matsala. Ya ga wani abin da ya sa shi baƙin ciki sosai. Babiloniyawa sun halaka Urushalima, ƙasar da yake so sosai. Wannan annabin da ke cike da baƙin ciki ya san cewa Isra’ilawa sun cancanci hukuncin nan da Allah ya yi musu saboda zunubansu. Irmiya yana da bege kuwa? Shin yana tunani ne cewa Jehobah ba ya ganin waɗanda suka tuba kuma ya cece su ne? Dubi yadda Irmiya ya yi magana a madadin mutanensa.
Ko da yake yawancin mutanen suna cikin baƙin ciki, Irmiya yana cike da bege. Ya yi kuka ga Jehobah yana cewa: “Babu shakka, rankaa [Jehobah da kansa] zai tuna da ni kuma ya durƙusa a kaina.” (Aya ta 20, NW) Irmiya bai yi shakkar abin da Jehobah ya ce ba. Ya san cewa Jehobah ba zai manta da shi da mutanensa da suka tuba ba. To, mene ne Allah mai iko duka zai yi?—Ru’ya ta Yohanna 15:3.
Irmiya yana da tabbaci cewa Jehobah zai yarda ya “durƙusa” domin waɗanda suka tuba da gaske. Wata fassara na Littafi Mai Tsarki ta ce: “Ka tuna, kuma ka sunkuya mini.” Waɗannan kalmomin sun taimaka mana mu ga cewa Jehobah mai juyayi ne. Jehobah “Maɗaukaki bisa dukan duniya,” zai sunkuya don ya ɗaga waɗanda suke bauta masa don ya fid da su daga mummunar yanayin da suke ciki kuma zai nuna musu rahama. (Zabura 83:18) Wannan begen ya ƙarfafa Irmiya. Annabin nan mai aminci ya ƙudurta cewa zai jira har sai lokacin da Jehobah ya ƙayyade ya ceto mutanensa da suka tuba.—Aya 21.
Kalmomin nan da Irmiya ya rubuta sun koya mana abubuwa biyu game da Jehobah. Na farko, yana da tawali’u. (Psalm 18:35, NW) Ko da yake “mafifici ne shi cikin iko,” a shirye Jehobah yake ya taimaka mana sa’ad da muke baƙin ciki, wato, zai durƙusa a alamance don ya kusace mu. (Ayuba 37:23; Zabura 113:5-7) Hakan yana da ban ƙarfafa, ko ba haka ba? Na biyu, Jehobah yana da rahama; yana da ‘hanzarin gafarta wa’ masu zunubi da suka tuba kuma yana nuna musu rahama. (Zabura 86:5) Halayen nan guda biyu, tawali’u da rahama, suna da alaƙa da juna.
Muna godiya cewa Jehobah ya bambanta da sarakuna ’yan Adam, waɗanda ba su da tausayi kuma suna da taurin kai saboda fahariya! Za ka so ka ƙara sanin wannan Allahn mai tawali’u wanda yana shirye ya ‘sunkuya’ don ya fid da masu bauta masa daga cikin baƙin ciki domin su kasance da bege?
[Hasiya]
a Marubuta na dā sun canja wannan ayar zuwa “raina,” kamar tana magana ne game da Irmiya. Sun yarda cewa bai kamata a ce da Allah rai ne ba, domin rai kalma ce wadda Littafi Mai Tsarki yake amfani da ita idan yana magana game da halittun Allah a duniya. Amma sau da yawa, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Allah a hanyar da ’yan Adam za su fahimce shi.
[Bayanin da ke shafi na 22]
A shirye Jehobah yake ya taimaka mana sa’ad da muke baƙin ciki