Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 6/1 p. 8-p. 10 par. 8
  • Darussa Daga Littafin Makoki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Makoki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘IDANUNA SUN DUSHE DOMIN HAWAYE’
  • (Makoki 1:1–2:22)
  • “KADA KA TOSHE KUNNENKA DAGA JIN LUMFASHINA”
  • (Makoki 3:1–5:22)
  • Ka Dogara ga Jehobah
  • “Ranka Zai . . . Durƙusa a Kaina”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Darussa Daga Littafin Irmiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Yi Gaba Gaɗi Irin Na Irmiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 6/1 p. 8-p. 10 par. 8

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Makoki

ANNABI Irmiya ya ga cikar saƙon hukuncin da ya furta na shekara 40. Yaya annabin ya ji sa’ad da ya ga halakar birnin da yake so? Sa’ad da yake gabatar da littafin Makoki, fassarar Septuagint na Helenanci ya ce: “Irmiya ya zauna ya yi kuka kuma ya yi makoki bisa Urushalima.” An rubuta littafin a shekara ta 607 K.Z., jim kaɗan da yi wa Urushalima kwanton ɓauna na watanni 18 kuma daga baya aka halaka ta, saboda haka littafin Makoki ya nuna baƙin cikin Irmiya sarai. (Irmiya 52:3-5, 12-14) Babu wani birni a tarihi da makokinta ke da ban tausayi sosai kamar Urushalima.

Littafin Makoki ya ƙunshi tarin littattafan waƙoƙi biyar. Littattafai huɗu na farko makoki ne; na biyar kuma roƙo ne ko kuma addu’a. A yare na asali, waƙoƙi huɗu na farko harufa ne, ayoyin bi da bi sun soma da harafi dabam ta tsarin harufa na Ibrananci guda 22. Ko da yake waƙa ta biyar tana da ayoyi 22 don ta yi daidai da adadin harufan Ibrananci, ba a tsara ta bisa harufa ba.—Makoki 5:10.

‘IDANUNA SUN DUSHE DOMIN HAWAYE’

(Makoki 1:1–2:22)

“Ga birni da ta ke cike da mutane a dā, tana zaman kewa babu kowa! Ta zama gwauruwa! Mai-girma a dā cikin al’ummai, sarauniya a cikin ƙasashe, Tana biya gandu!” Da waɗannan kalmomin ne annabi Irmiya ya soma makoki game da Urushalima. Da yake ba da dalilin wannan bala’in, annabin ya ce: “Ubangiji ya wahalshe ta domin yawan laifinta.”—Makoki 1:1, 5.

Da yake an kwatanta ta da gwauruwar da mijinta da kuma yaranta suka rasu, Urushalima ta yi tambaya: “Akwai baƙinciki irin nawa”? Ta yi wa Allah addu’a game da magabtanta: “Bari dukan muguntassu ta bayana a gabanka: Ka yi masu kuma, kamar yadda ka yi mani sabada dukan laifofina. Gama ajiyar zuciyata dayawa su ke, raina kuwa duk ya yi suwu.”—Makoki 1:12, 22.

Cike da baƙin ciki, Irmiya ya ce: “A cikin fushi mai-ƙuna [Jehobah] ya datse kowane ƙafo na Isra’ila; Ya kawasda hannunsa na dama sa’anda aka fuskanta abokin gāba: Kamar wuta mai-ci ya ƙone Yaƙub sarai, wuta mai-cin dukan abin da ke kusa da ita.” Da yake nuna yawan baƙin cikinsa, annabin ya yi makoki: ‘Idanuna sun dushe domin hawaye, duk na ruɗe a cikina, Hantata ta zuba a ƙasa.’ Masu wucewa ma sun yi mamaki, suna cewa: “Birni ke nan da mutane suka ce da ita, Kāmili ga jamāli? Abin farinciki ga dukan duniya?”—Makoki 2:3, 11, 15.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:15—Ta yaya Jehobah ya “tattaka budurwa ɗiyar Yahuda, sai ka ce cikin matsewar ruwan anab”? Da suka halaka birnin da aka kwatanta da budurwa, Babiloniyawa sun zubar da jini da yawa da aka kwatanta da matsewar ruwan inabi. Jehobah ya annabta wannan kuma ya ƙyale hakan ya faru, da haka za a iya cewa ya ‘tattaka wurin matsewar ruwan anab.’

2:1—Ta yaya aka ‘jefo da jamalin Isra’ila har ƙasa’? Tun da “sammai suna da nisa da duniya,” ana kwatanta kunyatar da abubuwa da aka ɗaukaka da ‘jefo da [su daga sama] har ƙasa.’ Sa’ad da aka halaka Urushalima kuma Yahuda ta zama kango, an tattaka “jamalin Isra’ila” wato, ɗaukaka da ikon da take morewa sa’ad da Jehobah yake yi mata albarka.—Ishaya 55:9.

2:1, 6—Menene ‘matashin sawun’ Jehobah da kuma ‘shimgensa’? Mai zabura ya rera waƙa: “Za mu shiga cikin mazaunansa: Mu yi sujada gun matakin sawunsa.” (Zabura 132:7) Saboda haka, “matashin” Makoki 2:1 na nuni ga gidan bauta na Jehobah, ko kuma haikalinsa. Babiloniyawa sun “ƙone gidan Ubangiji” kamar shinge, ko kuma bukka da ke cikin lambu.—Irmiya 52:12, 13.

2:17—Wace ‘magana’ ce Jehobah ya cika game da Urushalima? Wannan na nuni ga Leviticus 26:17, wadda ta ce: “Zan kuma kafa fuskata gāba da ku; za ku sha bugu a hannun abokan gābanku: maƙiyanku za su mallake ku; za ku gudu babu mai-binku.”

Darussa Dominmu:

1:1-9. Urushalima ta yi kuka sosai daddare, kuma hawayenta na zuba a kan kumatunta. Birnin ya zama kango, kuma firistocinta suna ajiyar zuciya. Budurwoyinta suna makoki, ita kuma da kanta tana baƙin ciki ƙwarai. Me ya sa? Domin Urushalima ta yi zunubi mai tsanani. Har rashin tsabtarta ya bayyana a tufafinta. Sakamakon aika laifi shi ne hawaye, ajiyar zuciya, makoki, da kuma baƙin ciki ba farin ciki ba.

1:18. Jehobah koyaushe yana nuna adalci sa’ad da yake horon waɗanda suka yi laifi.

2:20. An yi wa Isra’ilawa kashedi cewa idan ba su saurari muryar Jehobah ba, za su fuskanci bala’i wanda ya ƙunshi cin ‘naman ’ya’yansu maza da mata.’ (Kubawar Shari’a 28:15, 45, 53) Ba shi da kyau mu zaɓi tafarkin yi wa Allah rashin biyayya!

“KADA KA TOSHE KUNNENKA DAGA JIN LUMFASHINA”

(Makoki 3:1–5:22)

A Makoki sura 3, an kira al’ummar Isra’ila “mutumin.” Duk da cewa yana fuskantar wahala, wannan mutumin ya rera: “Ubangiji yana da alheri ga waɗanda ke sauraronsa, ga ran wanda ke biɗassa.” Sa’ad da yake addu’a ga Allah na gaskiya, ya yi roƙo: “Kā ji muryata; kada ka toshe kunnenka daga jin lumfashina, da jin kukata kuma.” Da yake roƙon Jehobah ya mai da hankali ga zargin magabtan, ya ce: “Za ka sāka masu sakaiya, ya Ubangiji, gwalgwadon aikin hannunsu.”—Makoki 3:1, 25, 56, 64.

Irmiya ya faɗi yadda yake ji game da sakamakon mugun hari da aka kai wa Urushalima na watanni 18 kuma ya yi makoki: “Alhakin laifin ɗiyar jama’ata ya fi alhakin zunubin Sodom, Wadda aka kaɓantadda ita farap, ba kuwa wanda ya sa mata hannu ba.” Irmiya ya ci gaba: “Gwamma waɗanda takobi ya kashe su da waɗanda aka kashe su da yunwa; Gama su suna shacewa, sokakku ne domin rashin anfanin ƙasa.”—Makoki 4:6, 9.

Waƙa ta biyar ta kwatanta mazaunan Urushalima suna magana. Sun ce: “Ya Ubangiji ka tuna da abin da ya same mu: Ka duba, ka ga zargin da a ke yi mana.” Sa’ad da suke furta wahalarsu, sun yi roƙo: “Ya Ubangiji, kai ka dawama sarki har abada: Al’arshenka daga zamani zuwa zamani ne. Ka maishe mu wurinka, ya Ubangiji, mu kuma mu a juya: Ka sabonta kwanukanmu kamar dā.”—Makoki 5:19, 21.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

3:16—Menene wannan furcin yake nufi: “Ya karya mani haƙorana da yan tsakuwai”? Wata majiya ta ce: “Sa’ad da suke kan hanyarsu zuwa bauta, an tilasta wa Yahudawa su gasa burodinsu a rami da aka haƙa a ƙasa, da haka burodinsu ya haɗu da yashi.” Cin irin wannan burodi yana iya karya haƙorin mutum.

4:3, 10—Me ya sa Irmiya ya kwatanta ‘ɗiyar jama’arsa’ da “jiminai cikin jeji”? Jimina “tana ƙarfin zuciya da ’ya’yanta, sai ka ce ba nata ba ne,” in ji Ayuba 39:16. Alal misali, bayan ta ƙyanƙyashe ƙwan, tsuntsuwar sai ta kama hanyarta da sauran tsuntsayen, sai na mijin ya ɗauki hakkin kula da ’ya’yan. Menene yake faruwa sa’ad da suka fuskanci haɗari? Duka tsuntsayen sai su gudu daga sheƙarsu su bar ’ya’yansu. Sa’ad da Babila ta kai wa Urushalima hari, an yi yunwa sosai da ya sa uwaye da ya kamata su ji tausayin yaransu suka zama azzalumai, kamar jiminai a cikin jeji. Wannan dabam yake da yadda dila take kula da ’ya’yanta sosai.

5:7—Jehobah yana kama mutane da alhaki don zunuban kakaninsu ne? A’a, Jehobah ba ya horon mutane kai tsaye don zunuban kakaninsu. “Kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Romawa 14:12) Amma tsara ta gaba suna iya shan wahala don sakamakon laifi da ya kasance na dogon lokaci. Alal misali, da yake Isra’ila ta dā ta koma ga bautar gunki, wannan ya sa ya kasance da wuya Isra’ilawa masu aminci ta gaba su manne wa tafarkin adalci.—Fitowa 20:5.

Darussa Dominmu:

3:8, 43, 44. Sa’ad da masifa ta faɗa wa Urushalima, Jehobah ya ƙi ya saurari kukan neman taimako na mazaunan birnin. Me ya sa? Domin mutanen sun yi rashin biyayya, kuma ba su tuba ba. Idan muna son Jehobah ya amsa addu’armu, dole ne mu yi masa biyayya.—Misalai 28:9.

3:20. Ana ɗaukaka Jehobah “Maɗaukaki bisa dukan duniya” da ya sa yake ƙasƙantar da kansa domin “ya duba abubuwan da ke cikin sama da duniya.” (Zabura 83:18; 113:6) Duk da haka, Irmiya ya san cewa Maɗaukaki yana shirye ya ƙasƙantar da kansa ya ga yanayin mutanen don ya ƙarfafa su. Muna farin ciki cewa Allah na gaskiya da ya fi ƙarfi da hikima mai tawali’u ne!

3:21-26, 28-33. Ta yaya za mu jimre wa wahala mai tsanani? Irmiya ya gaya mana. Kada mu manta cewa Jehobah mai yawan alheri ne da jinƙai. Ya kamata mu tuna cewa rai da muke da shi ya isa ya sa mu kasance da bege kuma muna bukatar mu yi haƙuri kuma mu jira, ba tare da yin gunaguni ba ga Jehobah idan za mu sami ceto. Bugu da ƙari, ya kamata mu “sa bakin[mu] cikin ƙura” wato, mu jimre wa gwaji, mu fahimci cewa da dalili mai kyau ne Allah yake ƙyale abu ya faru.

3:27. Fuskantar gwajin bangaskiya a lokacin ƙuruciya na iya nufin jimre wa wahala da kuma ba’a. Amma “abu mai-kyau ne ga mutum shi sha wuya tun yana yaro.” Me ya sa? Domin koyan jimre wa wahala tun mutum yana yaro yana shirya shi ya bi da ƙalubale idan ya girma.

3:39-42. Yin “gunaguni” sa’ad da muke shan wahala don zunubanmu ba shi da kyau. Maimakon yin gunaguni game da girban sakamakon laifinmu, “bari mu yi bincike mu auna al’amuranmu, mu sāke juyawa wajen Ubangiji.” Yana da kyau mu tuba mu daidaita al’amuranmu.

Ka Dogara ga Jehobah

Littafin Makoki ya bayyana yadda Jehobah ya ɗauki Urushalima da ƙasar Yahuda bayan da Babiloniyawa suka ƙone birnin kuma suka sa ƙasar ta zama kango. Zunuban mutanen da aka rubuta a ciki ya nuna cewa, a ra’ayin Jehobah, mutanen sun sha wahala ne domin zunubansu. Hurarrun waƙoƙin wannan littafin sun ƙunshi kalmomin da suka nuna bege ga Jehobah da kuma sha’awar koma wa bin tafarki da ya dace. Ko da yake wannan ba son zuciya na yawancin mutane a zamanin Irmiya ba ne, sun nuna ra’ayin Irmiya da na raguwar mutane da suka tuba.

Abubuwan da Jehobah ya ce game da yanayin Urushalima kamar yadda aka rubuta a littafin Makoki ya koya mana darussa biyu masu muhimmanci. Na farko, halakar Urushalima da kangon Yahuda ya ƙarfafa mu mu yi biyayya ga Jehobah kuma gargaɗi ne a garemu kada mu yi banza da nufin Allah. (1 Korinthiyawa 10:11) Darassi na biyu daga misalin Irmiya ne. (Romawa 15:4) Har a yanayi da kamar babu bege, annabin wanda ya yi makoki sosai ya dogara ga Jehobah don ceto. Yana da muhimmanci mu dogara ga Jehobah da Kalmarsa kuma mu sa ya zama madogararmu!—Ibraniyawa 4:12.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba