Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali
Yadda Za A Sake Amincewa da Juna
Stevea: “Ban taɓa tsammanin cewa Jodi za ta yi zina ba. Hakan ya sa na ƙasa amincewa da ita. Sai da na kai zuciya nesa kafin na gafarta mata.”
Jodi: “Na fahimci dalilin da ya sa Steve ya daina amincewa da ni. Sai da aka yi shekaru da yawa kafin Steve ya amince cewa na yi nadamar abin da na aikata.”
LITTAFI MAI TSARKI ya ba waɗanda abokin aurensu ya yi zina zaɓin kashe auren ko a’a.b (Matta 19:9) Steve, wanda aka yi maganarsa a baya, ya tsai da shawara cewa ba zai kashe aurensa ba. Shi da matarsa sun tsai da shawarar za su ci gaba da zama tare. Amma, daga baya sun fahimci cewa zaman aure a irin wannan yanayin bai da sauƙi. Me ya sa? Kamar yadda kalaminsu ya nuna, cin amana da Jodi ta yi ya sa mijinta ya daina amincewa da ita. Tun da amincewa da juna yana da muhimmanci sosai a zaman aure, wajibi ne su yi iya ƙoƙarinsu su sake amincewa da juna.
Idan kai da matarka kuna ƙoƙarin ku ceci aurenku bayan wani mummunar abu ya faru kamar zina, babu shakka kuna da jan aiki a gabanku. Zai yi muku wuya sosai a watannin farko bayan kun san abin da ya faru. Amma za ku iya yin nasara! Yaya za ku iya sake amincewa da juna? Shawarar da ke Littafi Mai Tsarki za ta iya taimakawa. Ku yi la’akari da shawarwari guda huɗu da ke gaba.
1 Ku Gaya Wa Junanku Gaskiya. Manzo Bulus ya rubuta: ‘Sai ku riƙa faɗin . . . gaskiya, kuna kawar da ƙarya.’ (Afisawa 4:25) Yin ƙarya, ƙin faɗin gaskiya tsantsa, har da ƙin yin magana gabaki ɗaya a kan batun suna sa a daina amincewa da juna. Kuna bukatar ku fito fili ku gaya wa junanku gaskiya.
Da farko, baƙin ciki yana iya hana ku tattauna batun. Amma, da wucewar lokaci kuna bukatar ku tattauna abin da ya faru dalla-dalla. Kuna iya tsai da shawara cewa ba za ku tattauna abin da ya faru gwari-gwari ba, amma ƙin yin magana a kan batun gaba ɗaya ba hikima ba ce. Jodi, wadda aka yi ƙaulinta ɗazu ta ce: “Da farko, yin magana game da batun ya yi mini wuya sosai kuma ya sa ni ƙyamar kaina. Abu ne da na yi nadama sosai a kai kuma ina son in mance da shi gaba ɗaya.” Amma wannan matakin ya jawo matsaloli. Me ya sa? Steve ya ce: “Domin Jodi ba ta so ta yi magana game da batun, hakan ya sa na ci gaba da zarginta.” Sa’ad da take magana bayan ta tuna abin da ya faru, ta yarda cewa, “Ƙin yin magana game da batun ya hana mu warware matsalar.”
Babu shakka, tattaunawa batun zai sa baƙin ciki. Debbie, wadda maigidanta Paul, ya yi zina da sakatariyarsa, ta ce: “Na yi tambayoyi da yawa. Ta yaya? Me ya sa? Taɗin me suka yi da ya kai ga hakan? Na yi baƙin ciki sosai, ina yawan tunani a kan batun kuma bayan wasu makonni, na ci gaba da yin tambayoyi.” Paul ya ce: “A wasu lokatai, ni da Debbie mukan yi gardama sosai. Amma muna ba juna haƙuri daga baya. Irin waɗannan tattaunawar ta sa mun kusaci juna.”
Ta yaya za ku iya rage gardama a lokacin da kuke tattaunawa? Ki tuna cewa ainihin muradinki shi ne ki koyi darasi daga abin da ya faru kuma ki ƙarfafa aurenki ba wai ki rama abin da mijinki ya yi miki ba. Alal misali, bayan Chul Soo ya yi zina, shi da matarsa, Mi Young sun bincika yanayin dangantakarsu don su gano abin da ya kai ga hakan. Chul Soo ya ce: “Na gano cewa na mai da hankali sosai ga abubuwan da suka shafe ni. Na damu sosai da faranta wa wasu rai da kuma yin abin da suke son in yi musu. Na mai da hankali sosai ga wasu mutane, kuma ina ba su lokacina. Saboda haka, ba na cika zama da matata.” Hakan ya sa Chul Soo da Mi Young suka yi canjin da ya taimaka musu su ƙarfafa aurensu da wucewar lokaci.
KU GWADA WANNAN: Idan kai ne ka ci amanar matarka, ka amince cewa ka yi laifi, kuma kada ka ɗora wa matarka laifi. Idan ke ce aka ci amanarki, kada ki daka wa mijinki tsawa ko kuma ki gaya masa baƙar magana. Ta wajen guje wa irin wannan halin, za ki ƙarfafa mijinki ya ci gaba da tattaunawa da ke a fili.—Afisawa 4:31.
2 Ku Ba Junanku Haɗin Kai. “Gwamma biyu da ɗaya,” in ji Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? “Domin suna da arziki cikin aikinsu. Gama idan sun fāɗi, ɗaya za ya ɗaga ɗan’uwansa.” (Mai-Wa’azi 4:9, 10) Wannan ƙa’idar tana da amfani sa’ad da kuke ƙoƙarin sake amincewa da juna.
Ku biyun kuna iya ƙoƙartawa ku magance abin da ya jawo hakan don ku sake amincewa da juna. Amma ya kamata ku biyun ku yi aiki tare wajen ceto aurenku. Matsalolin za su daɗa muni idan kowa yana ta kansa a ƙoƙarin da kuke yi na magance su. Kuna bukatar ku zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya wajen magance wannan matsalar.
Abin da Jodi da Steve suka gano ke nan. Jodi ta ce: “Ko da yake hakan ya ɗauki lokaci, amma ni da mijina mun haɗa kanmu wajen kyautata dangantakarmu. Na ƙudura cewa ba zan sake ɓata masa rai ba. Kuma ko da yake Steve ya yi baƙin ciki sosai, ya ƙudurta cewa ba zai raba aurenmu ba. Kowace rana, ina neman yadda zan tabbatar masa da amincina, shi kuma ya ci gaba da nuna mini ƙauna. Ina masa godiya kullum.”
KU GWADA WANNAN: Ku haɗa kanku don ku sake amincewa da juna a matsayin ma’aurata.
3 Ka Gyara Halinka. Bayan Yesu ya yi wa masu sauraronsa gargaɗi game da zina, sai ya ce: “Kuma idan idonka na dama yana sa ka yi tuntuɓe, ka cire shi, ka yar.” (Matta 5:27-29) Idan kai ne ka ci amanar matarka, ka yi tunanin wasu ayyuka da halayen da za ka daina don ka ƙarfafa aurenka.
Hakika, kana bukatar ka daina sha’ani da wadda ka yi zina da ita.c (Misalai 6:32; 1 Korintiyawa 15:33) Paul wanda aka ambata ɗazu, ya canja lokacinsa na aiki da lambar wayarsa don ya daina cuɗanya kwata-kwata da matar da ya yi zina da ita. Duk da haka, ƙoƙarinsa ya ci tura. Paul ya bar wurin da yake yin aiki don matarsa ta sake amincewa da shi. Ya kuma daina yin amfani da wayarsa sai na matarsa kaɗai. Kwalliyar ta biya kuɗin sabulu kuwa? Matarsa Debbie ta ce: “Shekara shida ke nan da wannan abin ya faru, kuma nakan damu cewa matar za ta neme shi. Amma yanzu na amince cewa Paul ba zai sake yin hakan ba.”
Idan kai ne ka ci amana, kana bukatar ka canja halinka. Alal misali, a ce kai mai yin kwarkwasa ne, ko kuma ka cika tunanin yin soyayya da wasu mata. A wannan yanayin, ka “tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa.” Ka sauya tsohon hali da sabon halin da zai sa matarka ta sake amincewa da kai. (Kolosiyawa 3:9, 10) Yadda aka yi renonka yana sa ya yi maka wuya ne ka nuna ƙauna? Ko da hakan ya yi maka wuya da farko, ka riƙa nuna wa matarka cewa kana ƙaunarta kuma ka tabbatar mata da hakan. Sa’ad da Steve ya tuna abin da ya faru, ya ce: “Jodi tana nuna mini ƙauna sosai, kuma tana yawan cewa ‘Ina son ka.’”
Ya kamata ka riƙa gaya wa matarka dukan abubuwan da kake yi a kowace rana. Mi Young wadda aka ambata ɗazu, ta ce: “Chul Soo yana gaya mini duk wani abin da ya faru a kullum, har ma da abubuwan da ba su da muhimmanci, don ya nuna mini cewa ba ya ɓoye mini kome.”
KU GWADA WANNAN: Ku tambayi juna abubuwan da za ku yi domin ku sake amincewa da juna. Ku rubuta su sa’an nan ku yi ƙoƙari ku bi abin da kuka rubuta. Ƙari ga abubuwan da kuka saba yi, ku soma yin wasu abubuwan da za ku iya jin daɗin yi tare.
4 Kana Iya Mance Dā Idan Lokaci Ya Yi. Kada ka yi hanzarin kammala cewa lokaci ya yi da za ku fara rayuwa kamar babu abin da ya faru. Misalai 21:5 ta ba da wannan gargaɗi: “Kowane mai-garaje wajen tsiya ya ke nufa.” Yana iya ɗaukan lokaci, wataƙila ma har shekaru kafin ku sake amincewa da juna.
Idan ke ce aka ci amanarki, ki kai zuciya nesa don ki samu isashen lokacin gafartawa. Mi Young ta tuna cewa: “A dā ina ganin cewa bai kamata mace ta ƙi gafarta wa mijinta ba, idan ya ci amanarta. Ban ga dalilin da zai sa ta riƙa yin fushi har na dogon lokaci ba. Amma, sa’ad da maigidana ya ci amanata ne na fahimci dalilin da ya sa gafartawa take da wuya.” Yana ɗaukan lokaci kafin a gafarta gaba ɗaya kuma a sake amincewa da juna.
Mai Wa’azi 3:1-3 ta ce akwai “lokacin warkaswa.” Da farko kana iya ganin kamar ƙin tattauna batun da matarka zai fi alheri. Amma idan ka ci gaba da haka, matarka ba za ta sake amincewa da kai ba. Don ku sake amincewa da juna, ki gafarta wa mijinki, kuma ki nuna hakan ta wajen gaya masa abin da kike tunani da kuma yadda kike ji. Za ki ma iya ƙarfafa mijinki ya gaya miki abin da ke sa shi farin ciki da kuma damuwa.
Kada ki yi tunanin abubuwan da za su daɗa sa ki baƙin ciki. Ki ƙoƙarta ki daina fushi. (Afisawa 4:32) Yin tunani a kan misalin da Allah ya kafa zai iya taimaka miki. Ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da mutanensa, Isra’ilawa na dā, suka daina bauta masa. Jehobah ya misalta kansa da mijin da matarsa ta ci amanarsa. (Irmiya 3:8, 9; 9:2) Amma ‘bai yi nukura har abada ba.’ (Irmiya 3:12) A lokacin da mutanensa suka tuba kuma suka dawo wurinsa, ya gafarta musu.
A ƙarshe, sa’ad da ke da mijinki kuka gamsu cewa kun yi canjin da ya kamata, za ku sake amincewa da juna sosai. A lokacin, maimakon ku damu da gyara aurenku kawai, za ku mai da hankali ga cim ma wasu maƙasudai tare. Ku duba nasarar da kuka yi. Duk da haka, kada ku yi sakaci. Ku daidaita ƙananan matsalolin da za su iya tasowa, kuma ku tabbatar da alkawarin da kuka yi wa juna.—Galatiyawa 6:9.
KU GWADA WANNAN: Maimakon ku yi ƙoƙarin mai da aurenku kamar yadda yake a dā, ku gwada ƙulla dangantakar da ta fi ta dā ƙarfi.
Za Ku Iya Yin Nasara
Idan a wasu lokuta kuna shakkar ko za ku yi nasara, ku tuna wannan: Allah ne Tushen aure. (Matta 19:4-6) Saboda haka, da taimakonsa za ku iya yin nasara a aurenku. Dukan ma’aurata da aka ambata a sama sun yi amfani da shawara mai kyau da ke Littafi Mai Tsarki kuma sun ceci aurensu.
Shekaru 20 ke nan tun da Steve da matarsa Jodi suka sami wannan matsalar a aurensu. Steve ya kwatanta abubuwan da suka yi don su daidaita aurensu da waɗannan kalmomi: “Sa’ad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah ne muka yi canji mafi muhimmanci. Taimakon da muka samu ya amfane mu sosai. Hakan ya taimaka mana mu jimre lokatan nan masu wuya.” Jodi ta ce: “Ina godiya sosai cewa mun jure wannan lokaci mafi wuya. Ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare, da kuma yin amfani da abin da muka koya, muna jin daɗin aurenmu sosai yanzu.”
[Hasiya]
a An canja sunayen.
b Don samun taimako wajen tsai da shawara a kan wannan batun, ka duba Awake! na 22 ga watan Afrilu 1999, shafi na 6, da kuma Awake! na 8 ga Agusta, 1995, shafuffuka na 10 da 11, na Turanci.
c Idan babu yadda za ka yi ka daina ganin wadda ka yi zina da ita (kamar a wajen aiki), idan ya zama dole, duk wani batun da za ku tattauna kada ya wuce na aiki. Ka yi duk wani abin da za ka yi da ita a gaban mutane kuma da sanin matarka.
KA TAMBAYI KANKA . . .
▪ Waɗanne dalilai ne suka sa na so in ceci aurenmu duk da cin amanar da mijina ya yi?
▪ Waɗanne halaye masu kyau ne kike gani daga mijinki?
▪ A lokacin da ni da mijina muke fita zance, ta yaya ne na nuna masa cewa ina ƙaunarsa, kuma yaya zan iya sake yin haka a yanzu?