Abin da Na Koya Daga Littafi Mai Tsarki
’YAN SHEKARA 3 ZUWA ƘASA
Ka duba dabbobin da ke kusa da jirgin Nuhu.
Waɗanne ne suke kuka moo, kuma waɗanne ke haushi?
Kowace dabba, gajere da dogo, Jirgin Nuhu ne ya cece su duka. Farawa 7:7-10; 8:15-17
UMURNI GA IYAYE
Ka sa yaronka ya nuna hoton:
Alade Bakan gizo Biri
Giwa Itace Jakin daji
Jirgin ruwa Kare Karen daji
Raƙumin daji Tunkiya Zaki
Ka kwaikwayi kukan waɗannan dabbobin:
Alade Biri Kare
Tunkiya Zaki