Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali
Ku Manne wa Wa’adin da Kuka Ɗauka a Aurenku
Ta ce: “Na lura cewa mai gidana Micheal ya daina sake mana jiki da ni da yaranmu.a Halinsa ya canja bayan da muka saka Intane a gida, kuma na lura cewa wataƙila yana kallon batsa a kwamfuta. Wata rana daddare bayan da yaranmu sun shiga barci, na tambaye shi game da abin da yake yi, sai ya amince cewa yana kallon batsa ne a Intane. Na yi fushi sosai kuma na yi baƙin ciki. Ban taɓa tsammanin cewa hakan zai faru da ni ba. Hakan ya sa ban amince da shi kuma ba. Bugu da ƙari, wani abokin aikina ya soma nuna cewa yana sha’awa ta.”
Ya ce: “Wata rana matata, Maria ta ga wani hoto da na sa a kwamfutarmu kuma ta tambaye ne game da hoton. Ta yi fushi sosai sa’ad da na faɗi gaskiya cewa ina kallon batsa a kai a kai. Na ji kunya sosai kuma na kasance mai laifi. Ina tsammanin cewa ƙarshen aurenmu ke nan.”
MENENE kake gani ya faru da dangantakar Michael da Maria? Za ka iya ga kamar kallon batsa ne ainihin matsalar Michael. Amma Micheal ya fahimci cewa wannan alama ce da ta nuna cewa da babban matsala a aurensu, wato, ba su manne wa wa’adi da suka ɗauka ba.b Sa’ad da Micheal da Maria suka yi aure, suna tsammanin cewa za su ci gaba da ƙaunar juna kuma za su yi farin cikin yin abubuwa tare. Kamar ma’aurata da yawa, ba da daɗewa ba wa’adin da suka ɗauka a aure ya yi sanyi, sai suka daina sha’awar juna.
Kana ganin cewa ƙaunar da ke tsakaninka da matarka ta yi sanyi da shigewar lokaci? Za ka so ƙaunar ta yi ƙarfi kamar dā? Idan haka ne, kana bukatar ka san amsar waɗannan tambayoyi guda uku: Mecece ma’anar manne wa wa’adi da kuka ɗauka a aurenku? Waɗanne abubuwa ne za su iya sa wa’adin da kuka ɗauka ya yi sanyi? Kuma menene za ka yi don ka ƙarfafa wa’adin da ka ɗauka ga abokiyar aurenka?
Menene Wa’adi?
Yaya za ka bayyana ma’anar wa’adi a aure? Wasu za su ce yin hakan ya ƙunshi kasancewa da hakki. Alal misali, ma’aurata suna iya manne wa wa’adin da suka ɗauka a aurensu saboda yaransu ko kuma saboda hakkin da suke da shi a gaban Allah, Wanda ya ƙafa aure. (Farawa 2:22-24) Babu shakka, irin waɗannan muradin suna da kyau kuma za su taimaki ma’aurata su magance matsala a aurensu. Amma idan suna so su yi farin ciki, ya kamata ma’aurata su nuna cewa suna ƙaunar juna sosai.
Jehobah Allah ya tsara aure ya sa ma’aurata farin ciki da gamsuwa. Ya shirya namiji ya yi ‘murna da matarsa’ mace kuma ta ƙaunaci mijinta kuma ta sani cewa yana ƙaunarta kamar yadda yake ƙaunar kansa. (Misalai 5:18; Afisawa 5:28) Ya kamata ma’aurata su gaskata da juna, idan suna so dangantakarsu ta yi ƙarfi. Abin muhimmanci ma, suna bukatar su ƙafa dangantaka na dindindin. Sa’ad da miji da mata suka yi ƙoƙari don su amince da juna kuma suka zama abokane na kud da kud, wa’adi da suka ɗauka a aurensu zai yi ƙarfi. Za su ƙafa dangantaka da Littafi Mai Tsarki ya kwatanta cewa su biyu za su zama kamar “nama ɗaya.”—Matta 19:5.
Za a iya kwatanta wa’adi da kwaɓi da yake sa bulo ya yi ƙarfi. Ana yin kwaɓi da ƙasa, siminti da kuma ruwa. Hakazalika, wa’adi ya ƙunshi hakki, aminci, da kuma dangantaka. Menene zai iya sa dangantakar ta yi sanyi?
Waɗanne Ƙalubale Ne Za a Iya Fuskanta?
Wa’adi yana bukatar aiki sosai da kuma saɗaukar da kai. Yana bukatar ka saɗaukar da kanka don abokiyar aurenka. Amma, kasancewa da ra’ayin saɗaukar da kai don a samu lada ya zama gama gari a yau, har wasu ma suna ganin cewa ya dace. Amma ka tambayi kanka, ‘Mutane masu son kai nawa ne na ga suna farin ciki a aure?’ Amsar ita ce, mutane kaɗan ne, Idan akwai. Me ya sa? Mutum mai son kai ba zai riƙe wa’adi a aure ba idan ana bukatar saɗaukar da kai, musamman ma idan babu lada da zai ko zata samu nan da nan don abin da ya ko ta yi. Idan ba wa’adi, dangantaka ba za ta yi kyau ba, komin ƙarfin soyayyar ma’auratan da farko.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa aure aiki ne sosai. Ya ce “amma mai-amre yana tattalin abin da ke na duniya, yadda za shi gami matatasa,” kuma “amrarriya tana tattalin abin da ke na duniya, yadda za ta gami mijinta.” (1 Korinthiyawa 7:33, 34) Abin baƙin ciki, ko ma’aurata da suke saɗaukar da kai ba sa daraja irin saɗaukar da kai da abokiyar aurensu take yi. Idan ma’aurata suka ƙi su daraja juna, aurensu zai iya kawo musu “wahala a cikin jiki” sosai fiye da yadda ya kamata.—1 Korinthiyawa 7:28.
Idan kana so aurenka ya yi nasara a lokacin matsala kuma ya yi ƙarfi a lokacin jin daɗi, ya kamata ka ɗauki dangantakarka ya zama na dindindin. Ta yaya za ka iya kasance da irin wannan ra’ayi, kuma yaya za ka iya ƙarfafa abokiyar aurenka ta riƙe wa’adinta gare ka?
Yadda Za a Ƙarfafa Wa’adi
Abu mafi muhimmanci shi ne a yi amfani da shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ta yin haka, za ka ‘amfani kanka’ da abokiyar aurenka. (Ishaya 48:17) Ka yi la’akari da abubuwa guda biyu da za ka iya yi.
1. Ka sa aurenka ya zama mafi muhimmanci. Manzo Bulus ya rubuta, “ku gwada mafifitan al’amura.” (Filibbiyawa 1:10) A gaban Allah yadda mata da miji suke bi da juna yana da muhimmanci. Allah zai girmama namijin da yake ɗaukaka matarsa. Kuma macen da take daraja mijinta tana da “tamani mai-girma a gaban Allah.”—1 Bitrus 3:1-4, 7.
Menene muhimmancin aurenka a gare ka? Hakika, idan abu na da muhimmanci, za ka mai da hankali sosai a kai. Ka tambayi kanka: ‘A watanni da suka wuce, awa nawa ne na keɓe don in kasance da abokiyar aurena? Waɗanne abubuwa ne na yi don in tabbatar wa abokiyar aurena cewa har yanzu mu abokai ne sosai?’ Idan baka kula da abokiyar aurenka yadda ya kamata ba, zai yi wuya ta yarda cewa kana riƙe wa’adin aurenka.
Abokiyar aurenka tana ɗaukarka mutum mai cika wa’adin aurensa ne kuwa? Ta yaya za ka iya sanin hakan?
KA GWADA WANNAN: Ka rubuta waɗannan abubuwa a cikin ’yar littafi: kuɗi, aiki, aure, nishaɗi, da kuma abokai. Yanzu ka lissafa su bisa ga abin da kake ganin shi ne ya fi muhimmanci ga abokiyar aurenka. Ka sa ita ma ta rubuta game da kai. Idan kun gama, ka yi musanyar abin da ka rubuta da ita. Idan abokiyar aurenka ta lura cewa ba ka mai da hankali sosai ga aurenka, ku tattauna canje-canjen da ya kamata ku yi don ku ƙarfafa wa’adin ku ga juna. Kuma ka tambayi kanka, ‘Menene ya kamata na yi don in riƙa yin sha’awar abubuwan da suke da muhimmanci ga abokiyar aurena?’
2. Ka guji kowace irin zina. Yesu Kristi ya ce: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Matta 5:28) Idan mutum ya yi zina, ya lalata dangantakar aure, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce zina ce tushen kisan aure. (Matta 5:32) Amma, kalmar Yesu da aka yi ƙaulinsa a baya ya nuna cewa mugun sha’awa za ta iya kasancewa a zuciya da daɗewa kafin mutum ya yi zina. Kasancewa da irin wannan mugun sha’awar a zuciya kaɗai ma, cin amana ce.
Don ka riƙe wa’adinka a aure, ka yi alkawari cewa ba za ka kalli batsa ba. Ko da menene mutane da yawa za su ce, batsa yana lalata aure. Ka lura da yadda wata mata ta faɗi ra’ayinta game halin kallon batsa da maigidanta yake da shi: “Maigidana ya ce wai kallon batsa yana sa soyayyar mu ta yi daɗi. Hakan ya sa na ji kamar ba ni da amfani, wato, ban ishe shi ba. Idan yana kallon batsa, sai in yi ta kuka har in yi barci.” Za ka ce wannan mutumin yana ƙarfafa wa’adin aurensa ne ko kuma yana lalata shi ne? Kana tsammanin cewa abin da yake yi zai sa matarsa ta riƙe wa’adin aurenta kuwa? Yana bi da ita kamar abokiyarsa na kud da kud kuwa?
Ayuba mutum mai aminci ya nuna wa’adin da ya yi game da aurensa kuma ga Allahnsa, sa’ad da ya yi ‘wa’adi da idanunsa.’ Ya ƙudurta cewa ba zai yi “sha’awar budurwa” ba. (Ayuba 31:1) Ta yaya za ka iya yin koyi da Ayuba?
Ƙari ga guje wa batsa, ya kamata ka kiyaye zuciyarka daga kafa dangantakar da ba ta dace ba da macen da ba matarka ba. Hakika, mutane da yawa suna ganin cewa yin kwarkwasa da macen da ba matarka ba, ba zai lalata aure ba. Amma Allah ya yi gargaɗi: “Zuciya ta fi komi rikici, ciwuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta?” (Irmiya 17:9) Zuciyarka tana ruɗinka? Ka tambayi kanka: ‘Wanene na fi mai da wa hankali, matata ko kuma wata da ba matata ba? Wanene na ke soma gaya wa abin albishiri, matata ko kuma wata da ba matata ba? Idan matata ta ce ka in mai da hankali ga dangantaka ta da mata, menene zan yi? Zan yi fushi, ko kuma cikin farin ciki zan yi gyara?’
KA GWADA WANNAN: Idan ka ga cewa kana yin kusa da wadda ba matarka ba, ka rage yin tarayya da ita, sai dai da dalili, tarayya da ita ta kasance a abubuwa masu muhimmanci ba na abokantaka ba. Kada ka yi tunani cewa waccan ta fi matarka. Maimakon haka, ka mai da hankali ga halayen matarka masu kyau. (Misalai 31:29) Ka tuna da dalilin da ya sa ka soma son matarka. Ka tambayi kanka, ‘Da gaske matata ta rasa waɗannan halayen ne, ko kuma na daina lura da su ne?’
Ka Ɗauki Mataki
Michael da Maria da aka ambata a baya sun nemi shawara game da yadda za su magance matsalarsu. Hakika, neman shawara ita ce abu na farko. Ta wurin fahimtar cewa suna da matsala kuma suka nemi taimako, Micheal da Maria sun nuna cewa suna da wa’adi a aurensu, kuma suna so su yi ƙoƙari sosai don su yi nasara.
Ko da aurenka yana yin nasara ko kuma yana cikin matsala, ya kamata abokiyar aurenka ta san cewa kana riƙe wa’adinka don auren ya yi nasara. Ka yi dukan abubuwan da ya kamata don ka tabbatar wa matarka hakan. Ka yarda za ka yi haka?
[Hasiya]
a An canja sunayen.
b Ko da yake wannan misalin game da namiji ne da yake kallon batsa, mace da take yin haka ma tana nuna rashin wa’adi a aure.
KA TAMBAYI KANKA . . .
▪ Waɗanne ayyuka ne zan rage yin su don in mai da wa matata hankali sosai?
▪ Menene zan yi don in tabbatar wa matata cewa ina riƙe wa’adi a aurenmu?
[Hotunan da ke shafi na 16]
Ka maida wa matarka hankali sosai
[Hotunan da ke shafi na 17]
Kwarkwasa yana somawa daga zuciya