Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 p. 20
  • Menene Jehobah Yake Bukata a Gare Mu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Jehobah Yake Bukata a Gare Mu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • “Kaunar Allah Ke Nan”
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Kaunar da Ke Tsakaninmu da Allah Za Ta Kasance Har Abada
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Jehobah Yana Son Ka Yi Masa Biyayya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 p. 20

Ka Kusaci Allah

Menene Jehobah Yake Bukata a Gare Mu?

Kubawar Shari’a 10:12, 13

YANKE shawarar yin biyayya ko ƙin yin biyayya, bai da sauƙi a yawancin lokaci. Shugaba matsananci zai tilasta wa waɗanda suke ƙarƙashinsa su yi masa biyayya ne kawai ba da son ransu ba. Amma, masu bauta wa Jehobah Allah, suna yi masa biyayya ne da son rai. Me ya sa? Don amsa tambayar, bari mu bincika kalaman Musa da ke Kubawar Shari’a 10:12, 13.a

Sa’ad da yake bayyana farillan Allah, Musa ya yi wata tambaya mai muhimmanci: “Menene Jehobah Allahnku ke so a gare ku?” (Aya ta 12) Allah yana da ikon ya sa mu yi duk wani abin da yake so. Gama, shi ne Ubangiji Mai Ikon Mallaka, Tushen rai kuma Mai kiyaye ta. (Zabura 36:9; Ishaya 33:22) Jehobah yana da ikon ya ce mu yi masa biyayya. Duk da haka, ba ya tilasta wa mutane su yi masa biyayya. Menene yake bukata a gare mu? Yana son mu yi ‘biyayya daga zuciya.’—Romawa 6:17.

Menene zai iya motsa mu mu yi wa Allah biyayya da son rai? Musa ya bayyana abu guda, sa’ad ya ce: “Ka ji tsoron Ubangiji Allahnka.”b (Aya ta 12) Wannan ba mugun jin tsoron sakamako marar kyau ba ne, amma, tsoro ne na daraja Allah da hanyoyinsa. Idan muna jin tsoron Allah sosai, za mu guji ɓata masa rai.

Menene ya kamata ya zama ainihin muradinmu na yi wa Allah biyayya? Musa ya bayyana: “Ka ƙaunace shi [Jehobah], ka bauta ma Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka.” (Aya ta 12) Ƙaunar Allah ya ƙunshi fiye da yadda muke ji. Wani littafin bincike ya bayyana cewa: “Aikatau na Ibrananci na kalmar nan ji yana kuma nufin matakan da aka ɗauka a sakamakon hakan.” Wannan littafin ya kuma ce a ƙaunaci Allah yana nufin “nuna ƙauna” a gare shi. A wani sassa kuma, idan muna ƙaunar Allah da gaske, za mu aikata a hanyoyin da muka san cewa za su faranta masa rai.—Misalai 27:11.

Yaya zurfin biyayyarmu ga Allah ya kamata ya zama? Musa ya ce: ‘Ka yi tafiya cikin dukan tafarkun [Allah].’ (Aya ta 12) Jehobah yana son mu yi dukan abin da yake bukata a gare mu. Irin wannan cikakkiyar biyayya za ta kasance da sakamako marar kyau ne a gare mu? Hakan ba zai yiwu ba.

Yin biyayya da son rai zai kawo albarka. Musa ya rubuta: “Ka kiyaye dokokin . . . waɗanda na umurce ka yau domin lafiyar kanka.” (Aya ta 13) Babu shakka, dukan dokar Jehobah, dukan abubuwan da ya ce mu yi, don amfaninmu ne. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya ce, “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Saboda haka, ya ba da irin waɗannan dokokin ne domin za su amfane mu. (Ishaya 48:17) Yin dukan abin da Jehobah ya ce mu yi zai kāre mu daga takaici yanzu kuma zai kai ga albarka marar iyaka a ƙarƙashin sarautar Mulkinsa.c

Yin biyayya ko a’a, idan ya zo ga abin da Jehobah yake bukata a gare mu, akwai zaɓi guda ne kawai mafi kyau. Cikakken biyayya da son rai shi ne mafi kyau. Irin wannan amintaccen tafarki yana jawo mu kusa da Jehobah, Allah mai ƙauna wanda yake son abin da ya fi dacewa a gare mu a kowane lokaci.

[Hasiya]

a Ko da yake kalaman Musa sun shafi Isra’ilawa na zamanin dā ne, amma mizanin ya shafi dukan waɗanda suke son su faranta wa Allah rai a yau.—Romawa 15:4.

b A cikin littafin Kubawar Shari’a gabaki ɗaya, Musa ya bayyana cewa ya kamata tsoron Allah ya zama mizanin da ke yi wa bayin Allah ja-gora.—Kubawar Shari’a 4:10; 6:13, 24; 8:6; 13:4; 31:12, 13.

c Don ƙarin bayani, ka duba babi na 3, “Menene Allah Ya Nufa ga Duniya?,” a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba