Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 3/1 p. 6
  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Yi Koyi da Bangaskiyar Musa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Bishiya Mai Cin Wuta
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Musa—Mutumi Ne Mai Bangaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 3/1 p. 6

Musa Mutumi Ne Mai Ƙauna

MECE CE ƘAUNA?

Ƙauna ta ƙunshi son mutane daga zuciya. Mutum mai ƙauna yakan nuna hakan ta yadda yake bi da mutane ko da yin hakan zai bukaci sadaukar da kansa.

TA YAYA MUSA YA NUNA ƘAUNA?

Musa ya nuna cewa yana ƙaunar Allah. Ta yaya? Ka tuna da abin da aka rubuta a 1 Yohanna 5:3: “Gama ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa.” Musa ya yi rayuwar da ta jitu da wannan ƙa’idar. Musa ya yi dukan ayyukan da Allah ya umurce shi, da masu sauƙi da masu wuya. Alal misali, sa’ad da Allah ya gaya masa ya miƙa sandarsa a kan Jan Teku, Musa ya yi biyayya. Kuma sa’ad da Allah gaya masa ya idar da umurnansa ga Fir’auna Musa bai ƙi ba. Hakika, Musa ya yi dukan abubuwan da Allah ya gaya masa. “Hakanan Musa ya yi: bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umurce shi, haka ya yi.”—Fitowa 40:16.

Musa ya ƙaunace ’yan’uwansa Isra’ilawa. Mutanen sun riƙa kawo damuwarsu wurin Musa domin sun gane cewa Jehobah ne ya naɗa shi ya ja-gorance su. Mun karanta cewa: “Mutane kuwa suna tsaye a wurin Musa tun safiya har maraice.” (Fitowa 18:13-16) Ka yi tunanin irin gajiyar da Musa ya ji sa’ad da yake sauraron mutanen nan yayin da suke gaya masa damuwarsu daga safiya har yamma. Duk da haka, Musa ya yi farin cikin taimaka wa mutanen domin yana ƙaunar su.

Gaba da sauraron su kawai, Musa ya yi wa mutanen da yake ƙauna addu’a. Har ma ya yi ma waɗanda suka yi masa laifi addu’a! Alal misali, sa’ad da Miriam, ’yar’uwar Musa ta yi masa gunaguni, Jehobah ya sa ta kamu da kuturta. Maimakon ya yi murna cewa an hukunta Miriam, nan da nan Musa ya yi roƙo a madadinta kuma ya yi addu’a ga Allah cewa: “Ka warkadda ita, ya Allah, ina roƙonka.” (Littafin Lissafi 12:13) In ban da ƙauna, mene ne zai sa Musa ya yi irin wannan roƙon ba tare da son kai ba?

WAƊANNE DARUSSA NE ZA MU KOYA?

Za mu iya bin misalin Musa ta wajen yin ƙoƙari sosai don mu ƙaunaci Allah. Irin wannan ƙaunar za ta sa mu yi biyayya da dokokinsa “da zuciya ɗaya.” (Romawa 6:17) Idan mun yi wa Jehobah biyayya da dukan zuciyarmu, za mu faranta masa rai. (Misalai 27:11) Mu ma da kanmu za mu amfana. Hakan gaskiya ne domin idan muna bauta wa Allah cikin ƙauna, ba kawai za mu riƙa yin abubuwa da suka dace ba, amma za mu ji daɗin yin waɗannan abubuwan.—Zabura 100:2.

Wata hanya kuma da za mu yi koyi da Musa ita ce kasancewa da irin ƙauna da za ta sa mu sadaukar da kanmu. Sa’ad da abokanmu ko danginmu suka zo su gaya mana abin da ke damun su, ƙauna za ta sa mu (1) saurare su sosai; (2) yi ƙoƙari mu fahimci yadda suke ji; da kuma (3) nuna musu cewa mun damu da su.

Kamar Musa, za mu iya yin addu’a a madadin waɗanda muke ƙauna. A wasu lokatai, muna iya baƙin ciki idan ba mu da ƙarfin taimakonsu sa’ad da suka gaya mana matsalolinsu. Da baƙin ciki, muna ma iya gaya musu: “Ka yi haƙuri cewa iyakacin abin da zan iya yi maka shi ne addu’a.” Amma ka tuna: “Addu’ar mai-adalci tana da iko dayawa cikin aikinta.” (Yaƙub 5:16) Addu’o’inmu suna iya sa Jehobah ya taimaka wa mutumin, ko da bai so yin hakan a lokacin ba. Hakika, babu wani abin da za mu yi wa ’yan’uwanmu da zai fi addu’a muhimmanci, ko ba haka ba?a

Shin, ba ka ganin akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya daga Musa? Ko da yake Musa mutum ne kamar mu, ya kafa mana babban misali a batun bangaskiya da tawali’u da ƙauna. Yayin da muke ƙoƙarin bin misalin Musa sau da kafa, za mu ƙara amfanar kanmu da kuma wasu.—Romawa 15:4.

a Idan muna son Allah ya ji addu’o’inmu, dole mu yi iya ƙoƙarinmu don mu bi ƙa’idodinsa. Don ƙarin bayani, ka karanta babi na 17 a cikin littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba