Ka Yi Koyi da Bangaskiyar Musa
“Ta wurin bangaskiya Musa, sa’anda ya yi girma, ya ƙi yarda a ce da shi ɗan ɗiyar Fir’auna.”—IBRAN. 11:24.
1, 2. (a) Wace shawara ce Musa ya yanke sa’ad da yake shekara 40? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Me ya sa Musa ya yarda a wulaƙanta shi tare da mutanen Allah?
MUSA ya san abin da zai iya mora a ƙasa Masar. Ya ga manyan gidaje masu kyau na mawadatan ƙasar. Shi ɗan gidan sarki ne kuma an koya masa “dukan hikimar Masarawa.” Wataƙila hakan ya haɗa da fasaha da ilimin taurari da lissafi da kuma kimiyya. (A. M. 7:22) Da Musa ya sami arziki da iko da kuma gata da wasu Masarawa ba za su taɓa samu ba!
2 Duk da haka, sa’ad da Musa yake shekara 40, ya yanke shawarar da ta ba wa masarautan Masar da suka yi renonsa mamaki. Bai so ya yi rayuwa a matsayin talaka a ƙasar Masar ba. Maimakon haka, ya yarda ya kasance tare da bayi! Me ya sa? Don Musa yana da bangaskiya. (Karanta Ibraniyawa 11:24-26.) Da yake Musa mai bangaskiya ne, ya ƙi ya yi kwaɗayin abubuwan da ke kewaye da shi. Ya ba da gaskiya ga Jehobah “Wanda ba shi ganuwa,” kuma ya gaskata cewa zai cika alkawuransa.—Ibran. 11:27.
3. Waɗanne tambayoyi uku ne za mu amsa a wannan talifi?
3 Mu ma bai kamata mu riƙa kwaɗayin abubuwan da ke kewaye da mu ba. Wajibi ne mu kasance “waɗanda su ke da bangaskiya.” (Ibran. 10:38, 39) Don mu ƙarfafa bangaskiyarmu, bari mu bincika abin da aka rubuta game da Musa a littafin Ibraniyawa 11:24-26. Yayin da muke bincikawa, mu yi ƙoƙarin ba da amsa ga tambayoyin da ke gaba: Ta yaya bangaskiyar Musa ta sa ya ƙi bin sha’awoyin jiki? Ta yaya bangaskiya ta sa ya daraja aikin da Allah ya ba shi? Kuma me ya sa Musa ya yi “sauraron sakamakon”?
YA ƘI BIN SHA’AWOYIN JIKI
4. Mene ne Musa ya fahimta game da “daɗin nishatsin zunubi”?
4 Musa ya gane cewa “daɗin nishatsin zunubi” na ɗan lokaci ne domin shi mai bangaskiya ne. Wasu za su iya kasance da ra’ayi dabam. Me ya sa? Domin sun ga ƙasar Masar da ke cike da sihiri da bautar gumaka sosai ta zama mai mulkin duniya, amma mutanen Jehobah suna shan wahala a matsayin bayi! Duk da haka, Musa ya san cewa Allah zai iya canja abubuwa. Duk da yake sun mai da hankali ga bin sha’awoyin jiki, amma Musa ya gaskata cewa za a halaka miyagu. Saboda haka, bai yarda ‘daɗin nishatsin zunubi na ’yan kwanaki’ ya zama masa jaraba ba.
5. Mene ne zai taimaka mana mu guje wa ‘daɗin nishatsin zunubi na ’yan kwanaki’?
5 Ta yaya za mu iya guje wa ‘daɗin nishatsin zunubi na ’yan kwanaki’? Bangaskiyarmu za ta taimaka mana mu ga cewa ‘duniya tana wucewa, duk da sha’awatata.’ (1 Yoh. 2:15-17) Ka yi bimbini a kan abin da zai faru da masu zunubi da suka ƙi tuba. Suna “wurare masu santsi,” yayin da suka zo “mummunan ƙarshe!” (Zab. 73:18, 19, Littafi Mai Tsarki) Yayin da kake fuskantar jarabar yin zunubi, ya kamata ka yi wannan tambaya, ‘Mene ne nake so ya faru da ni a nan gaba?’
6. (a) Me ya sa Musa ya ƙi “yarda a ce da shi ɗan ɗiyar Fir’auna”? (b) Me ya sa kake gani cewa Musa ya yanke shawara mai kyau?
6 Bangaskiyar Musa ta shafi aikin da ya zaɓa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta wurin bangaskiya Musa, sa’anda ya yi girma, ya ƙi yarda a ce da shi ɗan ɗiyar Fir’auna.” (Ibran. 11:24) Musa bai yi tunani cewa zai iya zama babba a fādar sarki kuma ya ci gaba da bauta wa Allah ba, sa’an nan sai ya yi amfani da dukiyarsa da kuma ikonsa wajen taimaka wa ’yan’uwansa Isra’ilawa. Maimakon haka, ya ƙudura niyyar ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsa da ransa da kuma ƙarfinsa. (K. Sha 6:5) Shawarar da Musa ya yanke ta kāre shi daga wahala. Daga baya, Isra’ilawa sun kwashi dukiyoyi da yawa na Masarawa da Musa ya yi banza da su. (Fit. 12:35, 36) An ci nasara a kan Fir’auna sa’ad da aka halaka shi. (Zab. 136:15) Musa kuma fa? Allah ya yi amfani da shi wajen yi wa Isra’ilawa ja-gora kuma sun sami ceto. Babu shakka, rayuwar Musa ta kasance da ma’ana sosai.
7. (a) Me ya sa ya kamata mu yi tanadi don rayuwa ta har abada kamar yadda littafin Matta 6:19-21 ya nuna? (b) Ka ba da labarin da ya nuna bambancin yin tanadi don rayuwa ta ɗan lokaci da kuma ta har abada.
7 Idan kai matashi ne mai bauta wa Jehobah, ta yaya bangaskiya za ta taimaka maka ka zaɓi sana’a? Zai dace ka yi tanadi don nan gaba. Ka ba da gaskiya ga alkawuran Allah kuma ka ‘tara wa kanka’ ko kuma ka yi tanadi don rayuwa ta har abada ba ta ɗan lokaci ba. (Karanta Matta 6:19-21.) Wannan ita ce shawarar da wata mai suna Sophie da take sana’ar rawa ta yi. Kamfanonin rawa dabam-dabam a ƙasar Amirka sun yi alkawarin biya mata kuɗin makaranta da kuma ba ta wani babban matsayi a kamfaninsu. Ta ce: “Yadda mutane suka so ni ya burge ni sosai.” Har ta ce tana gani kamar ta fi sauran tsararta masu rawa matsayi, amma ba ta yi farin ciki ba. Daga baya, Sophie ta kalli bidiyon nan Young People Ask—What Will I Do With My Life? Kuma ta ce, “Na fahimci cewa na sami ci gaba kuma mutane sun so ni don na bi sha’awar duniya maimakon in bauta wa Jehobah da dukan zuciyata.” Ta ci gaba da cewa, “Na yi addu’a ga Allah cikin natsuwa kuma na daina sana’ar rawar.” Yaya take ji game da shawarar da ta yi? Ta ce: “Ba na da-na-sani cewa na daina sana’ata ta dā. A yau, ina cike da farin ciki ƙwarai. Ina hidimar majagaba tare da mijina. Mu ba sanannu ba ne kuma ba masu kuɗi ba. Amma Jehobah yana tare da mu, muna da ɗaliban Littafi Mai Tsarki, kuma mun kafa wa kanmu maƙasudai da suke faranta masa rai. Ba na yin nadama ko kaɗan.”
8. Wace shawarar Littafi Mai Tsarki ce za ta taimaka wa matashi ya san abin da ya kamata ya yi da rayuwarsa?
8 Jehobah ya san abin da ya fi dacewa da kai. Musa ya ce: “Ina abin da Ubangiji Allahnka ke biɗa gareka, sai dai ka ji tsoron Ubangiji Allahnka, ka yi tafiya cikin dukan tafarkunsa, ka ƙaunace shi, ka bauta wa Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, ka kiyaye dokokin Ubangiji, da farillansa, waɗanda na umurce ka yau domin lafiyar kanka?” (K. Sha 10:12, 13) Yayin da kake matashi, ka zaɓi sana’a da za ta taimaka maka ka ƙaunaci Jehobah kuma ka bauta masa “da dukan zuciyarka, da dukan ranka.” Za ka iya kasancewa da tabbaci cewa sakamakon irin wannan rayuwar domin “lafiyar kanka” ne.
YA DARAJA AIKIN DA ALLAH YA BA SHI
9. Ka bayyana dalilin da mai yiwuwa ya sa ya yi wa Musa wuya ya yi aikin da Allah ya ba shi.
9 Musa ya ɗauki “zargi domin Kristi” a matsayin ‘wadata mafi girma bisa ga dukiyar Masar.’ (Ibran. 11:26) An naɗa Musa a matsayin “Kristi” ko kuma “Shafaffe.” Hakan yana nufin cewa Jehobah ya zaɓe shi don ya ja-goranci Isra’ilawa daga ƙasar Masar. Musa ya san cewa yin wannan aikin zai yi wuya kuma zai fuskanci “zargi” ko kuma hamayya. Da farko, wani Ba’isra’ile ya yi wa Musa ba’a kuma ya ce: “Wa ya sanya ka shugaba da alƙali a bisanmu?” (Fit. 2:13, 14) Daga baya, Musa ma ya tambayi Jehobah cewa: “Ƙaƙa Fir’auna fa za ya ji ni?” (Fit. 6:12) Musa ya yi addu’a ga Jehobah kuma hakan ya shirya shi don hamayyar da zai fuskanta. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Musa ya cim ma wannan aiki mai wuya?
10. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Musa ya cika aikinsa?
10 Na farko, Jehobah ya ce wa Musa: “Zan kasance tare da kai.” (Fit. 3:12) Na biyu, Jehobah ya sa Musa ya kasance da gaba gaɗi ta wajen bayyana masa sashe ɗaya na ma’anar sunansa sa’ad da ya ce: “Zan Zama Abin da Nake So In Zama.”a (Fit. 3:14, NW) Na uku, ya ba wa Musa ikon yin mu’ujizai da suka tabbatar cewa Allah ne ya aike shi. (Fit. 4:2-5) Na huɗu, Allah ya sa Haruna ya zama kakakin Musa da kuma abokin aikinsa don ya iya cika aikin da Allah ya ba shi. (Fit. 4:14-16) A ƙarshen rayuwarsa, Musa ya tabbata cewa Allah yana tanadar wa bayinsa abubuwan da suke bukata don su cika duk wani aikin da ya ba su kuma ya gaya wa Joshua: “Ubangiji ne za ya tafi gabanka; shi zauna tare da kai, ba za ya bar ka ba, ba kuwa za ya yashe ka ba: kada ka ji tsoro, kada ka razana.”—K. Sha 31:8.
11. Me ya sa Musa ya daraja aikinsa sosai?
11 Da taimakon Jehobah, Musa ya daraja aiki mai wuya da Allah ya ba shi fiye da “dukiyar Masar.” Balle ma, babu aikin da ya kai yi wa Allah hidima muhimmanci. Ƙari ga haka, kasancewa wanda Allah ya naɗa ya ja-goranci Isra’ila ya fi zama yarima a ƙasar Masar daraja sosai. Allah ya albarkaci Musa saboda hali mai kyau da ya nuna. Ya mori dangantaka ta kud da kud da Jehobah da kuma gatan nuna iko “mai girma” yayin da ya ja-goranci Isra’ilawa zuwa Ƙasar Alkawari.—K. Sha 34:10-12.
12. Waɗanne ayyuka ne Jehobah ya ba mu da ya kamata mu daraja?
12 Hakazalika, Allah ya ba mu aiki. Jehobah ya yi amfani da Ɗansa don ya ba mu aikin yin wa’azin bishara, kamar yadda ya ba manzo Bulus da kuma wasu. (Karanta 1 Timotawus 1:12-14.) Dukanmu muna da gatan yaɗa bishara. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Wasu suna hidima ta cikakken lokaci. ’Yan’uwa da suka manyanta suna hidima a cikin ikilisiya a matsayin bayi masu hidima da kuma dattawa. Amma ’yan’uwanmu da ba shaidu ba da kuma wasu za su iya yi mana hamayya saboda ayyukan da muke yi a ƙungiyar Jehobah. (Mat. 10:34-37) Idan hamayyarsu ta sa ka sanyin gwiwa, za ka soma tunani ko sadaukarwa da ka yi tana da amfani ko kuma ka ɗauka cewa ba za ka iya cika hidimarka ba. Idan hakan ya faru da kai, ta yaya bangaskiya za ta taimaka maka ka daure?
13. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu cika hidimarmu?
13 Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka kuma ka yi imani cewa zai yi hakan. Ka gaya masa abubuwan da ke ci maka tuwo a ƙwarya. Jehobah ne ya ba ka aikin kuma zai taimake ka ka yi nasara. Ta yaya? Kamar yadda ya taimaka wa Musa. Na farko, Jehobah ya ce “ni ƙarfafa ka: ni taimake ka, i, ni riƙe ka da hannun dama na adalcina.” (Isha. 41:10) Na biyu, ya tabbatar da kai cewa zai cika alkawuransa sa’ad da ya ce: “Na faɗi, zan kuwa sa shi tabbata; na ƙudurta, zan kuwa aika.” (Isha. 46:11) Na uku, Jehobah ya tanadar maka da “mafificin girman iko” don ka cika hidimarka. (2 Kor. 4:7) Na huɗu, tanadar maka da ’yan’uwa masu bi a faɗin duniya da suke “ƙarfafa” da kuma “inganta juna” don ka jimre a aikin da ya ba ka. (1 Tas. 5:11, LMT) Yayin da Jehobah yake tanadar maka da abubuwan da kake bukata don ka cika hidimarka, bangaskiyarka za ta ƙara inganci kuma za ka daraja gatan da ya ba ka fiye da duk wani abin duniya.
‘YA SAURARI SAKAMAKON’
14. Me ya sa Musa ya tabbata cewa Allah zai albarkace shi?
14 Musa ya ‘saurari sakamakon.’ (Ibran. 11:26) Ko da yake akwai abubuwa da yawa game da nan gaba da Musa bai sani ba, amma ya tsai da shawarwari bisa ɗan bayani da ya sani. Musa ya kasance da tabbaci kamar kakansa Ibrahim cewa Jehobah zai iya ta da matattu. (Luk 20:37, 38; Ibran. 11:17-19) Musa ya tabbata da alkawuran Allah saboda haka, bai ɗauka cewa shekaru 40 da ya yi a cikin daji ɓata lokaci ba ne. Musa bai san yadda Allah zai cika alkawuransa ba, duk da haka yana da bangaskiya cewa Allah zai albarkace shi.
15, 16. (a) Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga ladar da Allah zai ba mu? (b) Waɗanne albarka ne kake ɗokin morewa a ƙarƙashin Mulkin Allah?
15 Shin kana begen samun “sakamakon” ko kuma ladar da Allah zai ba ka? Muna kamar Musa domin ba mu da cikakken bayani game da yadda Allah zai cika alkawuransa. Alal misali, ‘ba mu san lokacin’ da ƙunci mai girma zai soma ba. (Mar. 13:32, 33) Duk da haka, mun sami bayani game da aljanna fiye da Musa. Jehobah ya bayyana mana yadda rayuwa za ta kasance a ƙarƙashin Mulkinsa kuma za mu iya “sauraron” ko kuma kwatanta aljannar a zuciyarmu. Sanin yadda rayuwa za ta kasance a aljanna zai sa mu saka Mulkin kan gaba a rayuwarmu. Ta yaya? Ka yi la’akari da wannan: Za ka sayi gida idan ba ka da isashen bayani game da gidan ne? A’a! Hakazalika, ba za mu ɓata lokacinmu da ƙarfinmu wajen biɗar abin da babu tabbas ba. Ya kamata bangaskiyarmu ta sa mu hangi yadda rayuwa za ta kasance a ƙarƙashin Mulkin Allah.
16 Mene ne zai taimaka maka ka fahimci yadda rayuwa za ta kasance a Mulki Allah? Ka ga kanka kana rayuwa a cikin Aljanna. Alal misali, sa’ad da kake karanta labarin bayin Allah da suka rayu a dā, ka yi tunanin irin tambayar da za ka yi musu sa’ad da suka tashi daga mutuwa. Ka yi tunanin irin tambayoyin da za su yi maka game da rayuwarka a kwanaki na ƙarshe. Ka yi tunanin yadda za ka yi farin ciki sosai sa’ad da ka haɗu da kakan-kakanninka kuma a koya musu dukan abun da Allah ya yi musu. Ka ga irin farin cikin da za ka yi yayin da kake sanin halayen dabbobin daji da yawa da suke zama cikin lumana a aljanna. Ka yi bimbini a kan yadda za ka kusaci Jehobah yayin da kake zama kamili da hankali.
17. Ta yaya tunani game da ladar da Allah zai ba mu zai taimaka mana a yau?
17 Yin tunani game da ladar da Allah zai ba mu zai taimaka mana mu jure, mu kasance da farin ciki kuma mu tsai shawarwarin da za su sa mu yi rayuwa har abada. Bulus ya rubuta wa ’yan’uwansa Kiristoci shafaffu cewa: “Idan muna kafa bege ga abin da ba mu gani ba, sa’annan da haƙuri mu ke sauraronsa.” (Rom. 8:25) Wannan ayar ta shafi dukan waɗanda ke da begen rayuwa har abada. Ko da yake ba mu sami ladarmu tukuna ba, amma muna “sauraronsa” da haƙuri don muna da bangaskiya sosai. Kamar Musa, ba ma ganin mun ɓata lokaci muna bauta wa Jehobah. Mun tabbata cewa “al’amuran da ake gani na zamani ne; amma al’amuran da ba su ganuwa madawwama ne.”—Karanta 2 Korintiyawa 4:16-18.
18, 19. (a) Me ya sa ya zama wajibi mu dage don mu kasance da bangaskiya sosai? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
18 Bangaskiyarmu tana sa mu ga “tabbacin al’amuran da ba a gani ba tukuna.” (Ibran. 11:1) Mutumin da bai da dangantaka da Allah bai san amfanin bauta wa Jehobah ba. A wajensa, wannan gatan “wauta” ne. (1 Kor. 2:14) Muna da begen da mutanen duniya ba za su fahimta ba, wato begen yin rayuwa har abada da shaida lokacin da za a yi tashin matattu. Yawancin mutane a yau sun ɗauka cewa wa’azin da muke yi shirme ne kamar yadda wasu mutane a zamanin Bulus suka yi masa kallon jahili “mai-surutu.”—A. M. 17:18.
19 Da yake muna rayuwa cikin mutanen da ba su da imani, wajibi ne mu dage don mu kasance da bangaskiya sosai. Ka roƙi Jehobah don “kada bangaskiyarka ta kāsa.” (Luk 22:32) Kamar Musa, ka yi tunanin sakamakon da ke tattare da yin zunubi da gatan bauta wa Jehobah da kuma begen yin rayuwa har abada. Shin waɗannan ne duka abubuwan da za mu iya koya daga Musa? A’a. A talifin da ke gaba, za mu tattauna yadda bangaskiya ta sa Musa ya ga “wanda ba shi ganuwa.”—Ibran. 11:27.
a Wani masani na Littafi Mai Tsarki ya rubuta game da Fitowa 3:14 cewa: “Ba abin da zai hana Allah cika nufinsa . . . Wannan sunan [Jehobah] shi ne kāriyar Isra’ila, wato abin ke tanadar musu da bege da kuma ƙarfafa.”