Musa Mutumi Ne Mai Bangaskiya
MECE CE BANGASKIYA?
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bangaskiya ta ƙunshi gaskatawa da wani abu bisa ga ƙwararren tabbaci. Mutumin da yake da bangaskiya ga Allah ya tabbata cewa Allah zai cika dukan alkawuransa.
TA YAYA MUSA YA NUNA BANGASKIYA?
Musa ya yi abubuwan da suka nuna cewa ya gaskata da alkawuran Allah. (Farawa 22:15-18) Ya sami damar yin rayuwar jin daɗi a Masar, amma ya ƙi da wannan damar domin ya ‘gwammace a wulakance shi tare da mutanen Allah, da ya ji daɗin yin zunubi na ’yan kwanaki.’ (Ibraniyawa 11:25) Shin, Musa ya yi garaje ne sa’ad da ya ɗauki wannan matakin? A’a, domin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Musa ya ‘jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.’ (Ibraniyawa 11:27) Musa bai yi da-na-sani don matakan da ya ɗauka ba ko kaɗan!
Musa ya taimaki wasu su kasance da bangaskiya ga Allah. Ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Isra’ilawa suka iske kansu tsakanin rundunar Fir’auna da Jan Teku kuma suka ɗauka cewa babu mafita. Isra’ilawan suka firgita domin suna ganin lallai-lallai, za su halaka, kuma hakan ya sa sun yi kuka ga Jehobah da kuma Musa. Mene ne Musa ya yi?
Wataƙila Musa bai san cewa Allah yana gab da raba Jan Teku don Isra’ilawa su wuce kuma su tsira ba. Amma, Musa ya kasance da gaba gaɗi cewa Allah zai yi wani abu don ya kāre mutanensa. Kuma Musa yana son ’yan’uwansa Isra’ilawa ma su kasance da wannan tabbacin. Mun karanta cewa: “Musa ya ce ma mutanen, Kada ku ji tsoro, ku tsaya kurum, ku ga ceton Ubangiji, wanda za ya yi maku yau.” (Fitowa 14:13) Shin, Musa ya cim ma burin taimaka wa ’yan’uwansa su kasance da bangaskiya ne? E. Mun sami tabbacin hakan domin Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da Musa da kuma Isra’ilawa cewa: ‘Ta wurin bangaskiya suka haye ta tsakiyar Jan teku, sai ka ce ta sandarariyar ƙasa.’ (Ibraniyawa 11:29) Bangaskiyar Musa ta taimaka masa da dukan waɗanda suka fahimci cewa kasancewa da bangaskiya abu ne mai hikima.
WAƊANNE DARUSSA NE ZA MU KOYA?
Za mu iya yin koyi da Musa ta wajen ɗaukan matakan da suka nuna cewa mun gaskata da alkawuran Allah. Alal misali, Allah ya yi alkawari cewa zai tanadar mana da abubuwa da muke bukata idan muka ɗauki bautarsa da muhimmanci fiye da kome. (Matta 6:33) A gaskiya, yin hakan yana da wuya domin biɗar abubuwan duniya ya zama ruwan dare a yau. Amma muna da tabbaci cewa idan mun yi iya ƙoƙarinmu don kada wani abu ya raba mana hankali daga bautar Jehobah, Allah zai tanadar mana da dukan abubuwa da muke bukata. Ya yi mana alkawari: “Daɗai ba ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba.”—Ibraniyawa 13:5.
Ƙari ga haka, za mu iya taimaka ma wasu su inganta bangaskiyarsu. Alal misali, iyaye za su iya taimaka wa ’ya’yansu su kasance da bangaskiya sosai ga Jehobah. Iyaye suna bukatar su koya wa yaransu tun suna ƙanana cewa Allah ya wanzu kuma shi ne yake tanadar mana da doka game da nagarta da mugunta. Amma gaba da hakan, iyaye suna bukatar su tabbata cewa yaransu sun gaskata cewa bin ƙa’idodin Jehobah yana da amfani sosai. (Ishaya 48:17, 18) Iyaye suna ba wa yaransu baiwa mai tamani sa’ad da suka taimaka musu su gaskata cewa Allah ya wanzu “kuma shi mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.”—Ibraniyawa 11:6.