Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 6/1 pp. 6-11
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Ba Shi Aiki
  • Batu da Ya fi Ceto Muhimmanci
  • Hulɗa da Mutane Masu Taurin Kai
  • Abin da Jehobah Ke Bukata Daga Mutanensa
  • Fahimtar Halayen Jehobah
  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Taƙaici Daga Littafin Fitowa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ka Yi Koyi da Bangaskiyar Musa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Kana “Ganin Wanda Ba Shi Ganuwa” Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 6/1 pp. 6-11

Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah

“Ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka.”—FITOWA 33:13.

1, 2. (a) Me ya sa Musa ya ɗauki matakin da ya ɗauka sa’ad da ya ga wani Bamasare na cutan wani Bayahude? (b) Domin ya cancanci yin hidimar Jehobah, menene Musa ke bukatar ya koya?

AN YI renon Musa a gidan Fir’auna, kuma an ilimantar da shi a hikimar manyan mutanen ƙasar Masar. Duk da haka, Musa ya fahimci cewa shi ba ɗan ƙasar Masar ba ne. Iyayensa Yahudawa ne. Sa’ad da ya kai shekara arba’in, ya tafi ya ziyarci ’yan’uwansa, Isra’ilawa. Sa’ad da ya ga wani Bamasare yana cutar wani Bayahude, Musa bai nuna son kai ba. Ya kashe Bamasaren. Musa ya zaɓi ya goyi bayan mutanen Jehobah kuma ya yi tunanin cewa Allah na amfani da shi domin ya ceci ’yan’uwansa. (Ayyukan Manzanni 7:21-25; Ibraniyawa 11:24, 25) Sa’ad da aka gane abin da ya faru, masarautan Masar suka ɗauki Musa ɗan tawaye, don haka, ya gudu don ya ceci ransa. (Fitowa 2:11-15) Idan Allah na so ya yi amfani da Musa, dole ne Musa ya fahimci hanyoyin Jehobah sosai. Musa zai iya koya kuwa?—Zabura 25:9.

2 Shekaru 40 da suka biyo baya, Musa ya yi rayuwar ɗan gudun hijira da kuma makiyayi. Maimakon ya yi fushi domin ’yan’uwansa Yahudawa sun ƙi shi, Musa ya yarda da abin da Allah ya ƙyale. Ko da yake shekaru da yawa sun wuce, Musa ya yarda Jehobah ya mulmula shi. Ba wai yana ɗaukaka kansa ba, amma a ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki na Allah, Musa ya rubuta: “Musa dai mai tawali’u ne ƙwarai, fiye da kowane mutum a duniya.” (Littafin Ƙidaya 12:3) Jehobah ya yi amfani da Musa a fitattun hanyoyi. Idan mu ma muka nemi tawali’u, Jehobah zai albarkace mu.—Zafaniya 2:3.

An Ba Shi Aiki

3, 4. (a) Wane aiki ne Jehobah ya ba Musa? (b) Wane taimako ne Musa ya samu?

3 Wata rana, wani mala’ika da ke wakiltan Jehobah ya yi wa Musa magana a kusa da Dutsen Horeb a hancin ƙasar da ya kutsa cikin tekun Sinai. Ya gaya wa Musa: “Na ga wahalar jama’ata waɗanda ke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu, don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci.” (Fitowa 3:2, 7, 8) A wannan lokacin, Allah na da aikin da zai ba Musa, amma dole ne ya yi shi a hanyar da Jehobah ke so.

4 Mala’ikan Jehobah ya ci gaba: “Zo, in aike ka wurin Fir’auna domin ka fito da jama’ata, wato Isra’ilawa, daga cikin Masar.” Amma Musa ya nuna shakka. A ganinsa, bai cancanta ba. Amma Jehobah ya ba shi tabbaci: “Zan kasance tare da kai.” (Fitowa 3:10-12) Jehobah ya ba Musa ikon yin mu’ujizai da za su ba da tabbacin cewa Allah ne ya aiko shi. Ɗan’uwan Musa, Haruna, shi ne zai zama kakakinsa. Kuma Jehobah zai koya musu abin da za su yi da abin da za su ce. (Fitowa 4:1-17) Musa zai yi wannan aikin cikin aminci kuwa?

5. Me ya sa halin Isra’ilawa ya zama ƙalubale ga Musa?

5 Da farko, dattawan Isra’ila sun gaskata Musa da Haruna. (Fitowa 4:29-31) Ba da daɗewa ba, “manyan Isra’ilawa” suka ɗora wa Musa da ɗan’uwansa laifin jawo musu “baƙin jini” a wurin Fir’auna da bayinsa. (Fitowa 5:19-21; 6:9) Sa’ad da Isra’ilawa suke barin ƙasar Masar, sun tsorata sa’ad da suka ga mayaƙan Masar sun tasa musu. Da suka ga Jar Teku a gabansu, kuma ga mayaƙa nan sun tasa musu, Isra’ilawa suka ga cewa sun faɗa cikin tarko, sai suka ɗora wa Musa laifi. Da kai ne, me za ka yi? Duk da cewa Isra’ilawa ba su da jiragen ruwa, a ƙarƙashin ja-gorar Jehobah, Musa ya gaya wa mutanen su kwashe kayansu su yi shirin tafiya. Bayan haka, Allah ya raba ruwan Jar Tekun biyu, sai ƙasar ta bushe domin Isra’ilawa su sami wurin bi.—Fitowa 14:1-22.

Batu da Ya fi Ceto Muhimmanci

6. Menene Jehobah ya nanata wa Musa sa’ad da ya aike shi?

6 Bayan ya gama ba Musa aikin, Jehobah ya nanata muhimmancin hurarren sunansa. Daraja sunan nan da kuma Wanda sunan ke wakilta na da muhimmanci. Sa’ad da Musa ya tambaye shi game da sunansa, Jehobah ya gaya masa: ‘Zan kasance abin da nake so.’ Bugu da ƙari, Musa zai gaya wa ’yan Isra’ila: “ ‘[Jehobah] Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Jehobah ya daɗa cewa: “Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai.” (Fitowa 3:13-15; NW ) Har yanzu, bayin Allah a dukan duniya, sun san shi ne kawai da sunan nan, Jehobah.—Ishaya 12:4, 5; 43:10-12.

7. Menene Allah ya umurci Musa ya yi duk da girman kan Fir’auna?

7 Sa’ad da suka bayyana a gaban Fir’auna, Musa da Haruna sun faɗi saƙonsu da sunan Jehobah. Amma Fir’auna cikin girman kai ya ce: “Wanene [Jehobah], har da zan ji maganarsa, in bar Isra’ilawa su tafi? Ai, ban san [Jehobah] ɗin nan ba, balle in bar Isra’ilawa su tafi.” (Fitowa 5:1, 2) Fir’auna ya nuna cewa shi mai taurin zuciya ne kuma mai ruɗi, duk da haka, Jehobah ya umurci Musa ya sanar da shi saƙonsa a kai a kai. (Fitowa 7:14-16, 20-23; 8:1, 2, 20) Musa ya ga cewa Fir’auna ya yi fushi. Za a sami wani sakamako mai kyau idan Musa ya ƙara zuwa wajensa kuwa? Isra’ila na ɗokin samun ceto. Fir’auna ya nace wa ƙin da ya yi. Da a ce kai ne, menene za ka yi?

8. Wane amfani ne aka samu daga yadda Jehobah ya bi da Fir’auna, kuma yaya waɗannan aukuwan ya kamata su shafe mu?

8 Musa ya sake idar wani saƙo, yana cewa: “Ni [Jehobah] Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama’ata domin su yi mini sujada.’ ” Kuma Allah ya ce masa: “Da ni kaina na miƙa dantsena na buge ka da jama’arka da annoba, ai, da an hallakar da ku a duniya ƙaƙaf. Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya.” (Fitowa 9:13-16) Domin abin da zai yi wa Fir’auna mai taurin zuciya, Jehobah ya ƙudurta yin amfani da ƙarfinsa domin hakan ya zama gargaɗi ga duk mai taka dokarsa. Wannan zai haɗa da Shaiɗan Iblis, wanda Yesu Kristi ya ƙira “mai mulkin duniyan nan.” (Yahaya 14:30; Romawa 9:17-24) Kamar yadda aka annabta, an daraja sunan Jehobah a dukan duniya. Domin tsawon jimrewarsa, Isra’ilawa da kuma mutane da yawa da suka bi su don bauta wa Jehobah sun sami ceto. (Fitowa 9:20, 21; 12:37, 38) Tun lokacin, yin shelar sunan Jehobah ya taimaka wa miliyoyin mutane su manne wa bauta ta gaskiya.

Hulɗa da Mutane Masu Taurin Kai

9. Ta yaya ne mutanen Musa suka nuna rashin daraja ga Jehobah?

9 Ibraniyawa sun san wannan hurarren suna. Musa ya yi amfani da wannan suna sa’ad da yake yi musu magana, amma ba su daraja mai wannan sunan ba. Ba da daɗewa ba bayan Jehobah ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar a hanya ta mu’ujiza, menene ya faru sa’ad da ba su sami ruwa mai daɗi ba? Sun yi wa Musa gunaguni. Bayan haka kuma sun yi gunaguni a kan abinci. Musa ya yi musu gargaɗi cewa ba shi ko Haruna suke yi wa gunaguni ba, amma Jehobah suke yi wa. (Fitowa 15:22-24; 16:2-12) A Dutsen Sinai, Jehobah ya bai wa Isra’ilawa Doka kuma ya nuna musu ayyuka masu ban mamaki. Amma bayan haka mutanen suka yi rashin biyayya suka yi ɗan maraƙin zinariya don su bauta masa kuma suka ce ‘idi ne ga Ubangiji.’—Fitowa 32:1-9.

10. Me ya sa roƙon da Musa ya yi da ke rubuce a Fitowa 33:13 ke da muhimmanci ga Kiristoci masu kula a yau?

10 Yaya Musa zai bi da mutanen da Jehobah da kansa ya kira masu taurin kai? Musa ya roƙi Jehobah: “Yanzu ina roƙonka idan na sami tagomashi a gare ka, ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka, in kuma sami tagomashi a wurinka.” (Fitowa 33:13) Wajen kula da Shaidun Jehobah na zamani, Kiristoci masu kula suna kiwon tumaki masu tawali’u. Duk da haka, su ma suna addu’a: “Ka koya mini al’amuranka, ya Ubangiji, ka sa su zama sanannu a gare ni.” (Zabura 25:4) Sanin hanyoyin Jehobah na taimaka wa masu kula su magance matsaloli a hanyar da ya jitu da Kalmar Allah da kuma mutuntakarsa.

Abin da Jehobah Ke Bukata Daga Mutanensa

11. Wane ja-gora ne Jehobah ya yi wa Musa, kuma me ya sa muke sha’awarsu?

11 Jehobah ya fayyace wa mutanensa abin da yake bukata a gare su a Dutsen Sinai. Bayan haka, Musa ya karɓi alluna biyu da ke dauke da rubutattun Dokoki Goma. Sa’ad da ya sauko daga kan dutsen, sai ya ga Isra’ilawa suna bauta wa ɗan maraƙi, ya kuwa harzuƙa, ya watsar da allunan kuma suka farfashe. Bayan haka, Jehobah ya sake ba shi Dokoki Goma a kan allunan da Musa ya sassaƙa. (Fitowa 32:19; 34:1) Waɗannan dokoki ba su taɓa canjawa ba tun lokacin da aka ba da su. Dole ne Musa ya aikata cikin jituwa da su. Allah kuma ya bayyana wa Musa ko wane mutum ne Shi, da haka, ya nuna wa Musa yadda zai bi da kansa a matsayin wakilin Jehobah. Kiristoci ba sa ƙarƙashin Dokar Musa, amma abubuwa da Jehobah ya gaya wa Musa suna ɗauke da mizanai da ba sa canjawa, kuma ana amfani da su a dukan fannonin bautar Jehobah. (Romawa 6:14; 13:8-10) Bari mu duba kaɗan daga ciki.

12. Ta yaya ne kishin Jehobah ya kamata ya shafi Isra’ila?

12 Ka bauta wa Jehobah shi kaɗai. Al’ummar Isra’ila na wurin sa’ad da Jehobah ya bayyana cewa shi kaɗai za a bauta wa. (Fitowa 20:2-5) Isra’ilawa sun ga isashen tabbaci da ya nuna cewa Jehobah shi ne Allah na gaskiya. (Maimaitawar Shari’a 4:33-35) Duk da abubuwa da wasu al’ummai suke yi, Jehobah ya fayyace wa mutanensa cewa ba zai yarda da kowane irin bautar gumaka ko sihiri ba. Ba da kansu ba je-ka-na-yi-ka ba ne kawai. Dukansu na bukatan su ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarsu, da dukan ransu, da kuma dukan ƙarfinsu. (Maimaitawar Shari’a 6:5, 6) Wannan zai haɗa da kalamansu, halayensu, da dukan fannonin rayuwansu. (Littafin Firistoci 20:27; 24:15, 16; 26:1) Yesu Kristi ya bayyana sarai cewa Jehobah na bukatan a bauta masa shi kaɗai.—Markus 12:28-30; Luka 4:8.

13. Me ya sa Isra’ila na bukatan yi wa Allah biyayya, kuma menene zai motsa mu mu yi masa biyayya? (Mai Hadishi 12:13)

13 Yin biyayya ga dokokin Jehobah. Mutanen Isra’ila na bukatan a tuna musu cewa sa’ad da suka yi alkawari da Jehobah, sun yi alkawarin yi masa biyayya. Sun more ’yanci, amma game da dokokin da Jehobah ya ba su, dole ne su yi biyayya. Hakan zai tabbatar da cewa suna ƙaunar Allah kuma su da ’ya’yansu za su amfana domin dukan dokokin Jehobah domin amfaninsu ne.—Fitowa 19:5-8; Maimaitawar Shari’a 5:27-33; 11:22, 23.

14. Ta yaya ne Jehobah ya nanata wa Isra’ilawa muhimmancin saka abubuwa na ruhaniya da farko?

14 Ka sa abubuwa na ruhaniya da farko. Al’ummar Isra’ila ba za ta yarda kula da abubuwa na jiki ya sha kan ayyuka na ruhaniya ba. Isra’ilawa ba za su duƙufa a kan biɗan abin duniya ba kawai. Jehobah ya keɓe lokaci mai tsarki kowane mako, lokacin da ake amfani da shi a bauta wa Allah na gaskiya kawai. (Fitowa 35:1-3; Littafin Ƙidaya 15:32-36) A kowace shekara, ana keɓe lokaci domin taro na musamman masu tsarki. (Littafin Firistoci 23:4-44) Wannan zai ba su zarafin tuna ayyuka masu girma na Jehobah, zai tuna musu hanyoyinsa, da kuma nuna godiya ga dukan nagartansa. Yayin da mutanen ke bauta wa Jehobah, tsoronsu na ibada da ƙauna za su ƙaru, kuma za a taimaka musu su yi tafiya a hanyoyinsa. (Maimaitawar Shari’a 10:12, 13) Mizanai masu kyau da ke cikin waɗannan umurnai, masu amfani ne ga bayin Jehobah a yau.—Ibraniyawa 10:24, 25.

Fahimtar Halayen Jehobah

15. (a) Me ya sa nuna godiya ga halayen Jehobah za su amfane Musa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu yi tunani sosai game da kowane hali na Jehobah?

15 Fahimtar halayen Jehobah zai taimaka wa Musa ya bi da mutanen. Fitowa 34:5-7 suka ce Allah ya wuce a gaban Musa yana cewa: “Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya. Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.” Ka ɗauki lokaci ka yi bimbini a kan kalaman nan. Ka tambayi kanka: ‘Menene ma’anar kowane hali? Ta yaya Jehobah ya nuna shi? Ta yaya ne Kiristoci masu kula za su iya nuna irin wannan halin? Ta yaya ne ya kamata halin ya shafi abubuwa da kowannenmu ke yi?’ Yi la’akari da waɗannan misalai ’yan kalilan.

16. Ta yaya za mu iya zurfafa ƙaunarmu ga jinƙai na Allah, kuma me ya sa yin haka na da muhimmanci?

16 Jehobah ‘Allah ne mai jinƙai, mai alheri.’ Idan kana da wannan majiya Insight on the Scriptures, ka karanta abin da ta ce a ƙarƙashin “jinƙai” (“Mercy”). Ko kuwa ka yi bincike a kan wannan batu ta yin amfani da Watch Tower Publications Index ko kuwa tsarin nan da ke cikin na’urar kwanfita Watchtower Library (CD-ROM).a Ka yi amfani da kundin yin bincike (concordance) domin neman nassosin da suka yi magana a kan jinƙai (mercy). Duk da cewa Jehobah na sauƙaƙa horo a wasu lokatai, jinƙansa ya haɗa da juyayi. Hakan na motsa Allah ya ɗauki mataki domin ya kawo wa mutanensa sauƙi. Domin tabbatar da haka, Allah ya yi wa Isra’ilawa tanadi na jiki da na ruhaniya a kan hanyarsu ta zuwa Ƙasar Alkawari. (Maimaitawar Shari’a 1:30-33; 8:4) Cikin jinƙai, Jehobah yana gafartawa sa’ad da aka yi kurakurai. Ya nuna jinƙai ga mutanensa na dā. Lallai ya kamata bayinsa na zamani su nuna juyayi ga juna!—Matiyu 9:13; 18:21-35.

17. Ta yaya ne fahimtarmu ta alherin Jehobah zai faɗaɗa bauta ta gaskiya?

17 Jinƙai na Jehobah ya haɗa da alheri. Yaya za ka iya kwatanta “alheri?” Ka gwada shi da nassosin da suka kwatanta Jehobah mai alheri. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa alherin da Jehobah ke nunawa ya haɗa da ƙauna da yake yi wa gajiyayyu da ke cikin mutanensa. (Fitowa 22:26, 27) A ƙasashe masu yawa, baƙi, da kuma wasu, suna iya samun kansu a yanayi mai ban tausayi. Sa’ad da yake koya wa mutanensa cewa kada su kasance da son kai kuma su nuna alheri ga irin waɗannan mutanen, Jehobah ya tuna musu cewa su ma baƙi ne dā a ƙasar Masar. (Maimaitawar Shari’a 24:17-22) Mu kuma fa mutanen Allah a yau? Alheri na haɗa kanmu kuma yana jawo wasu su bauta wa Jehobah.—Ayyukan Manzanni 10:34, 35; Wahayin Yahaya 7:9, 10.

18. Menene muka koya daga abin da Jehobah ya koya wa Isra’ilawa game da sha’anin mutanen wasu al’ummai?

18 Tausaya wa mutanen wasu al’ummai, bai kamata ya sha kan ƙaunar da Isra’ila ke yi wa Jehobah da kuma mizanansa na ɗabi’a ba. Da haka, an koyar da Isra’ilawa cewa kada su bi hanyoyin al’umman da ke kewaye da su, kada su bi addinansu da kuma rayuwarsu ta lalata. (Fitowa 34:11-16; Maimaitawar Shari’a 7:1-4) Wannan ya shafe mu a yau. Mu kasance mutane masu tsarki, kamar yadda Allahnmu Jehobah ke da tsarki.—1 Bitrus 1:15, 16.

19. Ta yaya ne fahimtar ra’ayin Jehobah game da zunubi zai kāre mutanensa?

19 Domin Musa ya fahimci hanyoyinsa, Jehobah ya fayyace masa cewa, ko da yake bai amince da zunubi ba, shi mai jinkirin fushi ne. Yana ba mutane lokaci su koyi abubuwa da yake bukata kuma su bi su. Idan aka tuba, Jehobah yana gafarta zunubi, amma ba zai kuɓutar da wanda ya yi mugun zunubi da ke bukatan horo ba. Ya gargaɗi Musa cewa abubuwa masu kyau ko marasa kyau da Isra’ilawa suka yi na iya shafan tsararraki na gaba. Nuna godiya ga hanyoyin Jehobah zai kāre mutanensa daga ɗora wa Allah laifi domin abubuwa da suka jawo wa kansu, ko kuwa su kammala cewa yana jinkiri.

20. Menene zai taimaka mana mu bi da ’yan’uwa masu bi da kuma waɗanda muka sadu da su a hidima yadda ya kamata?

20 Idan kana so ka ƙara zurfafa saninka game da Jehobah da hanyoyinsa, sai ka ci gaba da yin bincike kuma ka yi bimbini sa’ad da ka karanta Littafi Mai Tsarki. Ka duba kowane sashe na halin Jehobah a hankali. Cikin addu’a ka yi la’akari da yadda za ka iya yin koyi da Allah kuma rayuwarka ta yi daidai da manufarsa. Hakan zai kāre ka daga faɗawa tarko, ka bi da ’yan’uwa masu bi yadda ya kamata, kuma ka taimaka ma wasu su san Allahnmu mai girma kuma su ƙaunace shi.

[Hasiya]

a Shaidun Jehobah ne suka wallafa duka.

Menene Ka Koya?

• Me ya sa tawali’u ke da muhimmanci ga Musa, kuma me ya sa yake da muhimmanci a gare mu?

• Wane abu mai kyau aka cim ma ta wajen fuskantar Fir’auna da maganar Jehobah a kai a kai?

• Waɗanne muhimman mizanai ne aka koya wa Musa da suka shafe mu?

• Ta yaya za mu iya zurfafa fahimtarmu na halayen Jehobah?

[Hoto a shafi na 7]

Cikin aminci Musa ya gaya wa Fir’auna saƙon Jehobah

[Hoto a shafi na 9]

Jehobah ya gaya wa Musa abubuwa da yake bukata

[Hoto a shafi na 10]

Ka yi bimbini a kan halayen Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba