Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 4/15 pp. 8-12
  • Kana “Ganin Wanda Ba Shi Ganuwa” Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana “Ganin Wanda Ba Shi Ganuwa” Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “BAI JI TSORON HASALAR SARKI BA”
  • YA GASKATA DA ALKAWURAN ALLAH
  • ‘SUN HAYE TA TSAKIYAR JAR TEKU’
  • Ka Yi Koyi da Bangaskiyar Musa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Musa—Mutumi Ne Mai Bangaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Allah Ya Ceci ’Ya’yan Isra’ila
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 4/15 pp. 8-12

Kana “Ganin Wanda Ba Shi Ganuwa” Kuwa?

“Ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.”—IBRAN. 11:27.

TA YAYA “GANIN WANDA BA SHI GANUWA” ZAI . . .

  • taimaka maka ka sha kan tsoron ɗan Adam?

  • sa ka yi wa’azi da ƙwazo?

  • sa ka kasance da aminci a lokacin ƙunci mai girma?

1, 2. (a) Me ya sa kake ganin Musa yana cikin haɗari? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Me ya sa hasalar sarki ba ta sa Musa ya tsorata ba?

FIR’AUNA sarki ne mai iko sosai, kuma Masarawa suna bauta masa a matsayin alla. Wani littafi ya ce a wajen Masarawa, Fir’auna ya fi kowace halitta “hikima da kuma iko.” Fir’auna yakan sanya rawani mai siffar maciji da ke a shirye ya sari mutum. Me ya sa? Domin yana so a ji tsoronsa, kuma hakan ya riƙa tuna wa mutane cewa za a halaka magabtan sarki ba tare da ɓata lokaci ba. Ka yi tunanin yadda Musa ya ji sa’ad da Jehobah ya ce: “[Zan] aike ka wurin Fir’auna, domin ka fito da mutanena ’ya’yan Isra’ila daga cikin Masar.”—Fit. 3:10.

2 Musa ya tafi Masar kuma ya idar da saƙon Allah ga Fir’auna. A sakamakon haka, Fir’auna ya fusata sosai. Bayan da aka addabi ƙasar Masar da annoba guda tara, Fir’auna ya ja kunnen Musa da cewa: “Kada ka ƙara duban fuskata; gama ran da ka duba fuskata mutuwa za ka yi.” (Fit. 10:28) Kafin Musa ya bar wurin Fir’auna, ya annabta cewa ɗan farin sarkin zai mutu. (Fit. 11:4-8) A ƙarshe, Musa ya umurci Isra’ilawa cewa kowane iyali ya yanka akuya ko rago kuma su yayyafa jininsa a dogaran ƙofarsu. Rago dabba ne mai tsarki ga wani allahn Masarawa mai suna Ra. (Fit. 12:5-7) Wane mataki ne Fir’auna zai ɗauka? Musa bai ji tsoro ba. Me ya sa? Saboda bangaskiya, ya yi biyayya ga Jehobah kuma bai “ji tsoron hasalar sarki ba: gama ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.”—Karanta Ibraniyawa 11:27, 28.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna game da bangaskiyar da Musa ya yi ga “Wanda ba shi ganuwa”?

3 Shin kana da bangaskiya sosai da zai sa ka ga kamar kana ‘ganin Allah’? (Mat. 5:8) Yanzu za mu tattauna misalin Musa kuma hakan zai inganta bangaskiyarmu don mu iya ganin “Wanda ba shi ganuwa.” Ta yaya bangaskiyarsa ta taimaka masa ya sha kan tsoron ɗan Adam? Ta yaya ya nuna cewa ya gaskata da alkawuran Allah? Ta yaya ganin “Wanda ba shi ganuwa” ya ƙarfafa Musa a lokacin da shi da ’yan’uwansa suke cikin tsaka mai wuya?

“BAI JI TSORON HASALAR SARKI BA”

4. Wane irin tunani ne wataƙila mutane marasa bangaskiya suka yi sa’ad da Musa ya je gaban Fir’auna?

4 Mai yiwuwa waɗanda ba su da bangaskiya a lokacin sun ɗauka cewa Musa ƙwaro ne kawai a gaban Fir’auna. Kamar dai Fir’auna yana da iko ya yi abin da ya ga dama da Musa. Hakan ne ya sa Musa ya yi wa Jehobah tambayar nan: “Wāne ni har da zan tafi wurin Fir’auna, in fito da ’ya’yan Isra’ila daga cikin Masar kuma?” (Fit. 3:11) Shekaru 40 kafin wannan lokacin, Musa ya yi gudun hijira daga ƙasar Masar. Wataƙila ya yi tunani cewa, ‘Shin zai dace ne in koma Masar kuma in yi abin da zai ɓata ran sarkin?’

5, 6. Mene ne ya taimaki Musa ya kasance da tsoron Jehobah maimakon ya ji tsoron Fir’auna?

5 Kafin Musa ya koma Masar, Jehobah ya koya masa wani darasi mai muhimmanci. Daga baya, Musa ya rubuta wannan darasin a littafin Ayuba cewa: “Tsoron Ubangiji, shi ne hikima, rabuwa da mugunta kuma shi ne fahimi.” (Ayu. 28:28) Jehobah ya taimaka wa Musa ya ga bambancin da ke tsakanin ’yan Adam da kuma shi Allah Maɗaukaki don hakan ya sa Musa ya kasance da tsoron Ubangiji da kuma hikima. Ya tambayi Musa cewa: “Wanene ya yi bakin mutum? Wanene kuwa ya yi bebe, ko kurma, ko mai-gani, ko makaho? ba ni Ubangiji ba ne?”—Fit. 4:11.

6 Wane darasi ne Musa ya koya? Bai kamata ya ji tsoro ba domin Jehobah ne ya aike shi, kuma zai iya ba shi iko ya idar da saƙon Allah ga Fir’auna. Wannan ba shi ne karo na farko da bayin Allah suka faɗa cikin haɗari a ƙasar Masar ba. Wataƙila Musa ya tuna da yadda Jehobah ya kāre Ibrahim da Yusufu da kuma shi a zamanin su Fir’auna da suka gabaci wannan. Saboda haka, Fir’auna ba zai iya ja da Jehobah ba. (Far. 12:17-19; 41:14, 39-41; Fit. 1:22–2:10) Musa ya ba da gaskiya ga “Wanda ba shi ganuwa,” saboda haka ya bayyana a gaban Fir’auna kuma ya sanar da shi dukan abubuwan da Jehobah ya umurta.

7. Ta yaya bangaskiya ta kāre wata ’yar’uwa?

7 Bangaskiya ta kuma taimaka wa wata ’yar’uwa mai suna Ella ta sha kan tsoron ɗan Adam. A shekara ta 1949, Kwamitin Tsaro na ƙasar Estoniya, wato KGB sun kama ta, sun tuɓe mata kaya kuma wasu ’yan sanda matasa suka yi ta kallonta suna yi mata dariya. ’Yar’uwarmu ta ce: “Da farko wannan wulaƙancin ya dame ni sosai. Amma bayan na yi addu’a ga Jehobah, sai na sami kwanciyar hankali da kuma natsuwa.” Bayan haka, sun ƙulle ta a cikin wani ƙaramin ɗakin kurkuku kuma ta yi kwana uku a ciki. Ella ta ce: “’Yan sandan sun ce: ‘Za mu tabbatar cewa ba za a ƙara tuna da sunan nan Jehobah a ƙasar Estoniya ba! Za mu kai ki sansani sa’an nan a kai sauranku ƙasar Siberiya!’ Sai suka yi mata ba’a cewa, ‘Ina Jehobah ɗinki yake?’” Shin Ella ta ji tsoron mutane ne ko kuma ta dogara ga Jehobah? Sa’ad da suka tuhume ta, ta gaya musu da gaba gaɗi cewa: “Na yi tunani mai zurfi a kan batun nan kuma na gwammace in zauna a kurkuku da dangantaka mai kyau da Allah maimakon in yi abin da zai ɓata masa rai don in sami ’yanci.” Ella ta tabbata cewa Jehobah yana wanzuwa kamar mutanen da suke tsaye a gabanta. Ta kasance da aminci ga Jehobah domin tana da bangaskiya.

8, 9. (a) Mene ne rigakafin tsoron ɗan Adam? (b) Idan ka shiga yanayin da zai iya sa ka ji tsoron ɗan Adam, wane ne ya kamata ka tuna da shi?

8 Bangaskiya za ta taimaka maka ka sha kan tsoro. Idan hukuma ta yi ƙoƙarin hana ka bauta wa Allah, mai yiwuwa za ka iya ji kamar suna da iko su yi abin da suka ga dama da kai. Wataƙila ma ka yi irin wannan tunanin: ‘Shin zai dace in ci gaba da bauta wa Jehobah idan yin hakan zai jawo saɓani tsakanina da hukuma?’ Amma ka tuna cewa bangaskiya ita ce rigakafin tsoron ɗan Adam. (Karanta Misalai 29:25.) Jehobah ya ce bai kamata mu riƙa jin “tsoron mutum mai mutuwa, wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba.”—Isha. 51:12, 13, Littafi Mai Tsarki.

9 Ka riƙa tunawa da Ubanmu, wato Allah mai iko duka. Yana ganin dukan waɗanda suke shan wuya a hannun masu mulki marasa gaskiya, yana tausaya musu kuma yana taimakonsu. (Fit. 3:7-10) Ko da za ka bayyana imaninka a gaban hukuma ne, ‘kada hankalinka ya tashi a kan irin magana da za ka yi, ko kuwa abin da za ka faɗi: gama a cikin sa’an nan za a ba ka abin da za ka faɗi.’ (Mat. 10:18-20) Mahukunta da kuma ma’aikatan gwamnati ba za su iya ja da Jehobah ba. Idan ka ƙarfafa bangaskiyarka yanzu, za ka amince cewa Jehobah ya wanzu kuma yana ɗokin taimaka maka.

YA GASKATA DA ALKAWURAN ALLAH

10. (a) Mene ne Jehobah ya umurci Isra’ilawa su yi a watan Nisan na shekara ta 1513 kafin zamaninmu? (b) Me ya sa Musa ya bi umurnin Allah?

10 A watan Nisan na shekara ta 1513 kafin zamaninmu, Jehobah ya umurci Musa da Haruna su gaya wa Isra’ilawa cewa su zaɓi rago ko akuya mai koshin lafiya, su yanka shi kuma su yayyafa jininsa a dogaran ƙofarsu. (Fit. 12:3-7) Musa ya yi hakan kuwa? Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Ta wurin bangaskiya ya yi faska, da yayyafar jini, domin kada mai-halakan ɗan fari shi taɓa su.” (Ibran. 11:28) Musa ya san cewa Jehobah zai cika alkawuransa kuma ya kasance da bangaskiya cewa dukan ’ya’yan farin Masarawa za su mutu.

11. Me ya sa Musa ya gargaɗi Isra’ilawa?

11 ’Ya’yan Musa suna ƙasar Midiya wadda take da nisa daga ‘mai-halakar.’a (Fit. 18:1-6) Duk da haka, ya yi biyayya ga Jehobah kuma ya ba da umurni ga sauran iyalai da rayukan ’ya’yansu na fari ke cikin haɗari. Musa yana ƙaunar ’yan’uwansa kuma ya san cewa rayuka na cikin haɗari. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya ce Musa ya “kirayi dukan datiɓai na Isra’ila” nan da nan kuma ya ce masu, “ku ɗauki ’yan raguna gwargwadon iyalanku, ku yanka [domin; LMT] Faska.”—Fit. 12:21.

12. Wane saƙo mai muhimmanci ne Jehobah ya ce mu yi wa’azinsa?

12 Da taimakon mala’iku, mutanen Jehobah a yau suna yin wannan shelar: “Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja; gama sa’ar hukuncinsa ta zo: ku yi sujada ga wanda ya yi sama da duniya da teku da maɓulɓulan ruwaye.” (R. Yoh. 14:7) Yanzu ne ya kamata mu yi wannan shelar. Wajibi ne mu faɗakar da maƙwabtanmu su ware kansu daga Babila Babba, domin kada su “sha rabon annobanta.” (R. Yoh. 18:4) “Waɗansu tumaki” sun haɗa kai da shafaffun Kiristoci wajen roƙon mutane su yi ‘sulhu’ da Allah.—Yoh. 10:16; 2 Kor. 5:20.

13. Mene ne zai taimaka maka ka yi wa’azi da gaba gaɗi?

13 Muna da tabbaci cewa ‘sa’ar hukuncin’ ta kai. Mun kuma san cewa ya kamata mu yi wa’azi da gaggawa sosai kamar yadda Jehobah ya ce mu yi. A wani wahayi da aka saukar wa manzo Yohanna, ya ga “mala’ika huɗu suna tsaye a wajen ƙusurwoyi huɗu na duniya, suna riƙe da iskoki huɗu na duniya.” (R. Yoh. 7:1) Shin kana ganin waɗannan mala’ikun a shirye, suna gab da sako iskokin halaka na ƙunci mai girma bisa wannan duniyar? Idan kana da bangaskiya sosai, za ka kasance da tabbaci cewa waɗannan mala’ikun suna a shirye su yi hakan, kuma wannan zai sa ka yi wa’azi da ƙwazo.

14. Mene ne yake motsa mu mu faɗakar da miyagu don su ‘bar hanyarsu ta mugunta’?

14 Kiristoci na gaskiya a yau suna da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma begen rai na har abada. Amma mun san cewa hakkinmu ne mu faɗakar da miyagu don su ‘bar hanyarsu ta mugunta, su ceci ransu.’ (Karanta Ezekiyel 3:17-19.) Shin muna yin wa’azi ne kawai don mu guji ɗaukan alhaki? A’a. Muna ƙaunar Jehobah da kuma maƙwabtanmu. A almararsa ta Basamariye mai kirki, Yesu ya taimaka mana mu fahimci abin da kasancewa da ƙauna da kuma jin ƙai ya ƙunsa. Za mu iya tambayar kanmu, ‘Shin ina kamar Basamariyen ne ko kuwa ina kamar firist da Balawin ne? Shin ina a shirye in yi wa mutane wa’azi ko kuma ina neman hujja?’ (Luk 10:25-37) Idan mun gaskata da alkawuran Allah kuma muna ƙaunar maƙwabtanmu, za mu yi wa’azi da ƙwazo sosai kafin lokaci ya ƙure.

‘SUN HAYE TA TSAKIYAR JAR TEKU’

15. Me ya sa Isra’ilawa suka ji kamar babu mafita?

15 Bayan Isra’ilawa sun bar ƙasar Masar, bangaskiyar Musa ga “Wanda ba shi ganuwa” ta taimaka masa a lokacin da suka shiga yanayin da suke ganin babu mafita. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya’yan Isra’ila suka ta da idanunsu, sai ga Masarawa tafe bayansu da yaƙi suka tsorata ƙwarai: ’ya’yan Isra’ila kuwa suka ta da murya ga Ubangiji.” (Fit. 14:10-12) Shin Isra’ilawa sun shiga wannan yanayin cikin rashin sani ne? A’a. Jehobah ya gaya musu tun da wuri cewa: ‘Ni kuwa in taurara zuciyar Fir’auna, har za ya bi bayanku; zan kuwa ɗauki girma bisa Fir’auna, da dukan rundunarsa; Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.’ (Fit. 14:4) Duk da haka, Isra’ilawa sun nuna rashin bangaskiya. Abubuwan da suka gani kawai su ne Jar Teku da ke gabansu da karusan Fir’auna da ke binsu da kuma makiyayi ɗan shekara 80 da ke ja-gorarsu. Sun ɗauka cewa babu mafita.

16. Ta yaya bangaskiya ta taimaka wa Musa a Jar Teku?

16 Duk da haka, Musa bai ji tsoro ba. Me ya sa? Domin bangaskiyarsa ta taimaka masa ya ga abin da ya fi teku da kuma rundunar Fir’auna, wato “ceton Ubangiji.” Ya san cewa Jehobah zai yi yaƙi a madadin Isra’ilawa. (Karanta Fitowa 14:13, 14.) Bangaskiyar Musa ta ƙarfafa bayin Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta wurin bangaskiya suka haye ta tsakiyar Jan teku, sai ka ce ta sandarariyar ƙasa: Masarawa kuwa da suka yi ƙoƙari su yi haka nan suka dulmaya.” (Ibran. 11:29) Bayan wannan lamarin, “mutanen kuwa suka ji tsoron Ubangiji: suka ba da gaskiya ga Ubangiji kuma, da bawansa Musa.”—Fit. 14:31.

17. Wace aukuwa ce a nan gaba za ta gwada bangaskiyarmu?

17 Ba da daɗewa ba, za mu shiga mawuyacin lokaci. Sa’ad da aka kammala ƙunci mai girma, gwamnatocin wannan duniyar za su halaka dukan ƙungiyoyin addinai da suka fi mu yawa da kuma iko. (R. Yoh. 17:16) Jehobah ya annabta cewa yanayinmu zai zama kamar na “ƙasan nan wanda ta ke a fili, . . . dukansu ba garu, ba kātāko, ba ƙyamare.” (Ezek. 38:10-12, 14-16) Waɗanda ba su gaskata da Jehobah ba za su ɗauka cewa ba mu da mafita. Mene ne za ka yi?

18. Mene ne zai taimaka mana mu kasance da aminci a lokacin ƙunci mai girma?

18 Bai kamata mu ji tsoro ba. Me ya sa? Domin Jehobah ya annabta cewa za a kai wa bayinsa hari, amma zai cece su. Ya ce: “A ran nan, sa’anda Gog ya zo yaƙi da ƙasar Isra’ila, in ji Ubangiji Yahweh, sai hasalata za ta kawo har ƙafar hancina. Gama cikin kishina da wutar fushina na yi magana.” (Ezek. 38:18-23) Allah zai halaka dukan ƙungiyoyi da kuma mutanen da suke so su yi wa bayinsa lahani. Idan ka kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai kāre ka a “babbar rana mai-ban razana ta Ubangiji,” za ka “ga ceton Ubangiji” kuma za ka kasance da aminci.—Joel 2:31, 32.

19. (a) Shin Jehobah da Musa suna da dangantaka mai kyau kuwa? Ka bayyana. (b) Wace albarka ce za ka samu idan kana tunawa da Jehobah a dukan al’amuranka?

19 Ka shirya don waɗannan aukuwan tun yanzu ta wajen ci gaba da ‘jimrewa, kamar kana ganin wanda ba shi ganuwa’! Ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah ta wajen yin nazari da kuma addu’a kullum. Musa ya kasance da irin wannan dangantakar da Jehobah kuma Jehobah ya yi amfani da shi sosai, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ya san Musa “ido da ido.” (K. Sha 34:10) Musa fitaccen annabi ne. Idan ka kasance da bangaskiya, kai ma za ka iya kusantar Jehobah sosai, har ka ga kamar kana ganinsa. Kalmar Allah ta ce idan kana tunawa da Jehobah “a cikin dukan al’amuranka,” zai “daidaita hanyoyinka.”—Mis. 3:6.

a Jehobah ya aiko mala’iku su karkashe ’ya’yan farin Masarawa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba