Maganar Jehovah Rayayyiya Ce
Taƙaici Daga Littafin Fitowa
LABARI na gaske ne game da ceton waɗanda aka tilasta musu “su yi ta aiki mai tsanani.” (Fitowa 1:13) Labari ne kuma mai daɗi game da haihuwar wata al’umma. Akwai mu’ujizai na ban mamaki, tsarin dokoki masu kyau, da kuma ginin mazauni, duk suna cikin abubuwa masu kyau da ke cikinsa. Hakika, abin da littafin Fitowa cikin Littafi Mai Tsarki ke ɗauke da shi ke nan.
Annabi Musa Ba’ibrane ne ya rubuta, Fitowa ta faɗi abin da Isra’ilawa suka shaida na shekaru 145—daga mutuwar Yusufu a shekara ta 1657 K.Z. zuwa lokacin da aka gama ginin mazauni a shekara ta 1512 K.Z. Duk da haka, abin da ke ciki ba tarihi kawai ba ne. Kalmar Allah ce, ko kuwa saƙo, ga dukan ’yan Adam. “Rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki” ne kuma. (Ibraniyawa 4:12) Saboda haka, Fitowa tana da muhimmiyar ma’ana a gare mu.
“ALLAH KUWA YA JI NISHINSU”
(Fitowa 1:1–4:31)
Zuriyar Yakubu da suke zama a Masar suka ƙaru sosai har ya sa sarki ya tsananta musu su zama bayi. Har Fir’auna ya ce a kashe dukan yara maza na Isra’ilawa. Wani jariri Musa ɗan wata uku ya tsira, wanda ’yar Fir’auna ta ɗauke shi. Ko da yake an yi renonsa a gidan sarki, da ya kai shekara 40 Musa ya zaɓi ya yi tarayya da mutanensa kuma ya kashe wani Bamasare. (Ayyukan Manzanni 7:23, 24) Ya tsere zuwa Midiya saboda ana nemansa. Ya yi aure a wajen kuma ya zama makiyayi. A wani daji da ke cin wuta, Jehovah ya umurci Musa ya koma Masar ya yi wa Isra’ilawa ja-gora su fita daga bauta. Aka naɗa Haruna ɗan’uwansa ya zama kakakinsa.
An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:
3:1—Yetro wane irin firist ne? A lokatan ubanni kowane shugaban iyali ne firist na iyalinsa. Yetro shugaban iyali ne na ƙabilan Madayanawa. Tun da yake Madayanawa zuriyar Ibrahim ce ta wurin Ketura, ƙila suna bauta wa Jehovah.—Farawa 25:1, 2.
4:11—A wane azanci ne Jehovah ‘ya yi bebe, da kurma, da kuma makaho’? Ko da yake a wani lokaci Jehovah yakan sa mutum ya makanta ko kuma ya zama bebe, ba shi yake jawo dukan irin wannan naƙasa ba. (Farawa 19:11; Luka 1:20–22, 62–64) Sakamakon zunubi da aka gāda ne. (Ayuba 14:4; Romawa 5:12) Tun da yake Allah ya ƙyale irin wannan yanayi, za a iya cewa shi ne yake ‘sa’ mutum ya zama bebe, kurma, ko kuma makaho.
4:16—Ta yaya Musa ya “zama kamar Allah” ga Haruna? Musa wakilin Allah ne. Shi ya sa Musa ya zama “kamar Allah” ga Haruna da ya zama wakilin Musa wajen magana.
Darussa da Za Mu Koya:
1:7, 14. Jehovah ya goya wa mutanensa baya sa’ad da ake tsananta musu a Masar. Haka kuma yake kiyaye Shaidunsa na zamanin nan, har idan suna fuskantar tsanani mai yawa ma.
1:17–21. Jehovah yana tuna da mu yana ‘mana alheri.’—Nehemiya 13:31.
3:7–10. Jehovah yana jin kukan mutanensa.
3:14. Jehovah yana cika ƙudurinsa babu fasawa. Saboda haka, za mu tabbata cewa zai cika begenmu na Littafi Mai Tsarki.
4:10, 13. Musa ba shi da gaba gaɗi sam cewa zai iya magana har bayan Allah ya tabbatar masa cewa zai toƙara masa, ya ce Allah ya aiki wani dabam ya yi magana da Fir’auna. Duk da haka, Jehovah ya yi amfani da Musa ya ba shi hikima da ƙarfi da yake bukata ya cika aikinsa. Maimakon jin ba mu cancanta ba, bari mu dogara ga Jehovah kuma mu cika aikinmu na wa’azi da koyarwa da aminci.—Matiyu 24:14; 28:19, 20.
MU’UJIZAI NA BAN MAMAKI SUN KAWO CETO
(Fitowa 5:1–15:21)
Musa da Haruna suka zo gaban Fir’auna suna neman izinin Isra’ilawa su tafi su yi wa Jehovah idi a cikin daji. Masaraucin Masar don reni ya ƙi. Jehovah ya yi amfani da Musa ya zubo masa annoba bi da bi. Bayan annoba ta goma ce Fir’auna ya yarda wa Isra’ilawa su tafi. Bai jima ba, shi da rundunarsa suka soma binsu a guje. Amma Jehovah ya buɗe hanyar tsira ta wurin Bahar don ya ceci mutanensa. Masarawa da suke binsu suka rasa rayukansu sa’ad da Bahar ta komo kansu.
An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:
6:3—Ta yaya ya zama cewa Allah bai sanar da sunansa ga Ibrahim, Ishaƙu, da Yakubu ba? Waɗannan ubannin iyali sun yi amfani da sunan Allah kuma sun sami alkawura daga Jehovah. Duk da haka, ba su sani ko kuma shaida wani abu da ke nuna cewa Jehovah ne yake sa waɗannan alkawuran su cika ba.—Farawa 12:1, 2; 15:7, 13–16; 26:24; 28:10–15.
7:1—Ta yaya Musa ya zama kamar “Allah ga Fir’auna”? Allah ya ba wa Musa ƙarfi da kuma iko a kan Fir’auna. Shi ya sa ba ya bukatar ya ji tsoron sarkin ba.
7:22—Daga ina Masarawa masu sihiri suka sami ruwa da bai zama jini ba? Wataƙila sun yi amfani da ruwa da suka ɗebo kafin a mai da ruwan Kogin Nilu jini. Za a kuma iya samun ruwa da babu jini ta wajen tona gefen Kogin Nilu.—Fitowa 7:24.
8:26, 27—Me ya sa Musa ya ce hadayun Isra’ilawa sa zama “haramu ne ga Masarawa”? Ana bauta wa dabbobi da yawa a Masar. Saboda haka, yadda Musa ya ambaci yin hadaya ya daɗa wa naciyarsa rinjaya cewa a ƙyale Isra’ilawa su je su yi wa Jehovah hadaya.
12:29—Su waɗannene ’yan farin? ’Yan farin ’yan maza ne kawai. (Littafin Ƙidaya 3:40–51) Ba a kashe Fir’auna da shi kansa ɗan fari ne ba. Yana da nasa iyali. Ba shugaban iyali ne zai mutu ba amma ɗan farin ne zai mutu saboda annoba ta goma.
12:40—Shekaru nawa ne Isra’ilawa suka yi a ƙasar Masar? Shekaru 430 da aka ambata a nan ya haɗa da lokaci da ’ya’yan Isra’ila suka yi a ‘ƙasar Masar da kuma ƙasar Kan’ana.’ (Hasiya na Reference Bible) Ibrahim shekararsa 75 ne da ya ƙetare Kogin Yufiretis a shekara ta 1943 K.Z., a kan hanyarsa zuwa Kan’ana. (Farawa 12:4) Daga lokacin zuwa lokacin da Yakubu ɗan shekara 130 ya shiga Masar, shekaru 215 ne. (Farawa 21:5; 25:26; 47:9) Wannan yana nufin cewa daga baya Isra’ilawa sun sake yin shekaru 215 a Masar.
15:8—Ruwa da ya “daskare” a Bahar ruwan ƙanƙara ne? Aikatau na Ibrananci da aka fassara “daskare” yana nufin ya yi kauri. An yi amfani da shi game da madara ma. Shi ya sa ruwa da ya daskare ba lalle ne ya zama ƙanƙara ba. Idan “iskar gabas mai ƙarfi” da aka ambata a Fitowa 14:12 ta yi sanyi da za ta iya daskare ruwan, da wasu majiya sun yi nazarinsa kuma sun ga yawan sanyin. Tun da yake babu wani abin da ake gani da ya riƙe ruwan, kamar ruwan ya daskare ne, ko kuma ya yi kauri.
Darussa da Za Mu Koya:
7:14–12:30. Annoba Goman ba tsautsayi ba ne. An annabta su ne kuma sun auku daidai yadda aka nuna. Yadda aka bayyana su ya nuna yadda Mahalicci yake da iko a kan ruwa, hasken rana, ƙwari, dabbobi, da kuma mutane! Annobar kuma sun nuna yadda Allah yake zaɓe kafin ya kawo masifa a kan magabtansa kuma ya kāre masu bauta masa.
11:2; 12:36. Jehovah yana albarkace mutanensa. Yana tabbatar da cewa an ba Isra’ilawa hakkinsu na aiki a Masar. Sun shiga ƙasar mutane ’yantattu, ba waɗanda aka ci a yaƙi ba.
14:30. Za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehovah zai ceci masu bauta masa daga “matsananciyar wahala.”—Matiyu 24:20–22; Wahayin Yahaya 7:9, 14.
JEHOVAH YA KAFA AL’UMMA TA TSARINSA
(Fitowa 15:22–40:38)
Wata uku bayan an cece su daga Masar, Isra’ilawa suka taru a ƙasan Dutsen Sinai. A wajen aka ba su Dokoki Goma da kuma wasu dokoki, suka ɗaura alkawari da Jehovah, kuma suka zama al’umma ta tsarinsa. Musa ya yi kwanaki 40 a kan dutse ana yi masa koyarwa game da bauta ta gaskiya da kuma ginin mazaunin Jehovah, wato ƙaramin haikali. A lokacin kuma Isra’ilawa suka ƙera kuma suka soma bauta wa ɗan maraƙin zinariya. Musa yana saukowa sai ya ga wannan, ya fusata ya fashe alluna biyu da Allah ya ba shi. Bayan da aka yi wa masu laifin horon da ya dace, ya komo kan dutse don ya sake karɓo allunan. Bayan da Musa ya dawo, aka soma ginin mazauni. A ƙarshen shekara ta farko na ’yancin Isra’ilawa, an gama wannan babban mazauni da dukan adonsa da kuma tsarin. Sai Jehovah ya cika mazaunin da ɗaukakarsa.
An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:
20:5—Ta yaya Jehovah yake “hukunta ’ya’ya” tsararraki na nan gaba? Sa’ad da yaro ya kai mutum, a kan hukunta kowanne domin halinsa da kuma laifinsa. Amma sa’ad da al’ummar Isra’ila ta shiga bautar gumaka, ta sha wahalar wannan har tsararraki da yawa. Isra’ilawa masu aminci ma sun shaida sakamakon rashin aminci na al’ummar, wannan ya sa ya kasance musu da wuya su ci gaba da aminci.
23:19; 34:26—Mecece manufar umurnin nan kada a dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa? Dafa ɗan akuya (ko wata dabba) cikin madarar uwarsa an ce al’adar arna ce cewa ta hakan za su sami ruwan sama. Ban da haka ma, madarar uwa ce ake amfani da ita don ciyar da ’ya’yanta, idan aka dafa ’ya’yan ciki, butulci ne. Wannan dokar ta taimake mutanen Allah su ga bukatar su nuna juyayi.
23:20–23 (Litafi Mai-Tsarki)—Wane mala’ika ne aka ambata a nan, kuma ta yaya sunan Jehovah yake “cikinsa”? Mai yiwuwa Yesu ne mala’ikan kafin ya zama mutum. An yi amfani da shi ya yi wa Isra’ilawa ja-gora zuwa Ƙasar Alkawari. (1 Korantiyawa 10:1–4) Sunan Jehovah yana “cikinsa” yana nufin cewa Yesu ne musamman ya ɗaukaka kuma ya tsarkake sunan Ubansa.
32:1–8, 25–35—Me ya sa ba a hori Haruna domin ƙera ɗan maraƙin ba? Haruna bai amince da bautar gunkin ba. Daga baya, ya bi Lawiyawa suka tsaya gefen Allah kuma suka yi tsayayya gāba da waɗanda suka ƙi Musa. Bayan da aka halaka masu laifin, Musa ya tunasar da mutanen cewa sun yi zunubi sosai, wannan yana nuna cewa ban da Haruna da akwai wasu kuma da suka sami jinƙan Jehovah.
33:11, 20—Ta yaya Allah ya yi magana da Musa “baki da baki”? Wannan furci yana nufin abokai biyu ne da suke taɗi da kyau. Musa ya yi magana da wakilin Allah kuma ya karɓi umurni daga wurin Jehovah ta wurinsa. Amma Musa bai ga Jehovah ba, da yake ‘babu wanda yake ganin Allah ya rayu.’ Jehovah bai yi magana da Musa da bakinsa ba. An ba da Doka “ta wurin mala’iku ne, ta hannun matsakanci,” in ji Galatiyawa 3:19.
Darussa da Za Mu Koya:
15:25; 16:12. Jehovah yana yi wa mutanensa tanadi.
18:21. Dole maza da aka zaɓa su sami hakki cikin ikilisiyar Kirista su ma su inganta, masu tsoron Allah, amintattu, kuma marasa son kai.
20:1–23:33. Jehovah ne mai ba da Doka mafi girma. Sa’ad da Isra’ilawa suka yi biyayya, dokokinsa suna taimakonsu su bauta masa da kyau kuma sun yi farin cikin yin haka. Jehovah yana da ƙungiya ta tsarinsa a yau. Haɗa kai da ita tana kawo mana farin ciki da kuma kwanciyar rai.
Muhimmiyar Ma’ana a Gare Mu
Menene littafin Fitowa ta bayyana game da Jehovah? Tana wakilta shi Mai Tanadi da kyau, Mai Ceto da babu na biyunsa, Mai Cika nufe-nufensa. Shi ne Allah na ƙungiya da take tsarinsa.
Sa’ad da kake karatun Littafi Mai Tsarki naka na mako don shirya taron Makarantar Hidima ta Tsarin Allah, lalle za ka motsa game da abin da ka koya daga Fitowa. Sa’ad da ka bincika abin da ke sashe na “An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi,” za ka ƙara samun fahimi game da wasu wurare na Nassosi. Kalamin da ke ƙarƙashin “Darussa da Za Mu Koya” za su nuna maka yadda za ka amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki na mako.