Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 18 p. 48-p. 49 par. 4
  • Bishiya Mai Cin Wuta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bishiya Mai Cin Wuta
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Kurmi Mai Cin Wuta
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Dalilin Da Ya Sa Musa Ya Gudu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 18 p. 48-p. 49 par. 4
Musa ya je kusa da bishiyar da ke ci da wuta

DARASI NA 18

Bishiya Mai Cin Wuta

Musa ya yi shekara 40 a ƙasar Midiya. Ya yi aure kuma ya haifi yara. Wata rana sa’ad da yake kiwon tumakinsa kusa da Dutsen Sinai, sai ya ga wani abin mamaki. Ya ga wata bishiya tana cin wuta amma ba ta ƙone ba. Sa’ad da Musa ya je kusa don ya ga abin da ya sa, sai ya ji wata murya ta ce: ‘Musa! Kada ka zo kusa. Ka cire takalmanka domin kana tsaye a wuri mai tsarki.’ Jehobah ne ya yi amfani da mala’ika don ya yi masa magana.

Musa ya ji tsoro sai ya rufe fuskarsa. Muryar ta ci gaba da cewa: ‘Na ga irin wahalar da Isra’ilawa suke sha. Zan cece su daga ƙasar Masar kuma zan kawo su cikin wata ƙasa mai kyau. Kai ne za ka yi musu ja-gora daga ƙasar Masar.’ Hakan ya ba Musa mamaki, ko ba haka ba?

Musa ya yi tambaya, ya ce: ‘Me zan faɗa idan mutanen suka ce wane ne ya aiko ni?’ Sai Allah ya ce: ‘Ka gaya musu cewa Jehobah, Allahn Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yakubu ne ya aiko ka.’ Musa ya ce: ‘Idan mutanen ba su yarda ba fa?’ Sai Jehobah ya yi wani abu da ya sa Musa ya tabbatar da cewa zai taimaka masa. Ya ce Musa ya jefa sandar da ke hannunsa a ƙasa. Sai sandar ta zama maciji. Sa’ad da Musa ya riƙe wutsiyar macijin, sai ya sake zama sanda. Jehobah ya ce: ‘Idan ka yi wannan abin mamaki, za su san cewa ni na aiko ka.’

Musa ya ce: ‘Ban iya magana ba sosai.’ Sai Jehobah ya yi masa alkawari cewa: ‘Zan gaya maka abin da za ka ce, kuma zan sa ɗan’uwanka Haruna ya taimaka maka.’ Da yake Musa ya san cewa Jehobah yana tare da shi, sai shi da matarsa da kuma yaransa suka koma ƙasar Masar.

“Kada hankalinku ya tashi a kan irin magana da za ku yi, ko kuwa abin da za ku faɗi: gama a cikin saʼan nan za a ba ku abin da za ku faɗi.”​—Matta 10:19

Tambayoyi: Mene ne Musa ya gani sa’ad da yake kiwon tumakinsa? Mene ne Jehobah yake so Musa ya yi?

Fitowa 3:1–4:20; Ayyukan Manzanni 7:​30-36

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba