Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • my labari na 30
  • Kurmi Mai Cin Wuta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kurmi Mai Cin Wuta
  • Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Bishiya Mai Cin Wuta
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Dalilin Da Ya Sa Musa Ya Gudu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
my labari na 30

LABARI NA 30

Kurmi Mai Cin Wuta

MUSA ya yi dogon kiwo har dutsen Horeb domin ya nemi ciyayi ga tumakinsa. A nan sai ya ga kurmi yana cin wuta, amma ba ya ƙonewa!

‘Wannan abin mamaki ne,’ ya yi tunani. ‘Bari in ɗan ratsa in gani.’ Da ya yi kusa, sai murya ta yi masa magana a cikin kurmi, tana cewa: ‘Kada ka yi kusa. Ka tuɓe takalmanka, domin kana tsaye ne a wuri mai tsarki.’ Allah ne yake magana ta bakin mala’ika, saboda haka, Musa ya rufe fuskarsa.

Sai Allah ya ce: ‘Na ga wahalar mutanena a ƙasar Masar. Saboda haka, ina so in ’yantar da su, kuma kai zan aika ka ja-goranci mutanena su fita daga ƙasar Masar.’ Jehobah zai kawo mutanensa zuwa kyakkyawar ƙasar Kan’ana.

Amma Musa ya ce: ‘Ni ba kome ba ne. Ta yaya zan yi haka? Amma a ce na tafi. Isra’ilawa za su ce mini, “Wanene ya aiko ka?” To me zan gaya musu?’

‘Haka za ka faɗa musu,’ in ji Allah. ‘“JEHOBAH Allahn Ibrahim, Allahn Ishaku da kuma Allahn Yakubu ne ya aiko ni wurinku.”’ Sai kuma Jehobah ya daɗa cewa: ‘Sunana ke nan har abada.’

‘Idan kuma ba su yarda da abin da na ce ba fa sa’ad da na ce da su kai ka aiko ni,’ Musa ya amsa.

‘Me ka ke riƙe da shi a hannunka?’ Allah ya tambaye shi.

Musa ya amsa: ‘Sanda ne.’

‘Ka jefar a ƙasa,’ in ji Allah. Sa’ad da Musa ya jefar, sai sandan ya zama maciji. Sai Jehobah kuma ya yi wa Musa wata mu’ujiza. Ya gaya masa: ‘ka saka hannunka cikin rigarka.’ Musa ya saka, sa’ad da ya fito da hannunsa waje, ya zama fari fat! Hannunsa ya zama kamar mai muguwar cutar nan da ake kira kuturta. Sai kuma Jehobah ya ba Musa ikon ya yi mu’ujiza ta uku. A ƙarshe ya ce: ‘Idan ka yi waɗannan mu’ujizai Isra’ilawa za su gaskata cewa ni ne na aiko ka.’

Bayan wannan sai Musa ya koma gida ya cewa Jethro: “Don Allah bari in koma in ga yadda ’yan’uwana suke a ƙasar Masar.” Sai Jethro ya yi ban kwana da Musa, Musa ya fara tafiyarsa zuwa ƙasar Masar.

Fitowa 3:1-22; 4:1-20.

Tambayoyi na Nazari

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba