Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 7/1 pp. 18-21
  • Jehobah Yana Son Ka Yi Masa Biyayya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Son Ka Yi Masa Biyayya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Biyayya “ta Fi Hadaya”
  • Wani Misali da Gargaɗi Ne
  • Ka Yi Biyayya a Dukan Abubuwa
  • Biyayyar da Ake Yi Domin Ƙauna
  • Yin “Biyayya ta Fi Hadaya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Sarki Na Farko a Isra’ila
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Saul, Sarkin Isra’ila Na Farko
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Biyayya—Muhimmin Darasi ne na Yarantaka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 7/1 pp. 18-21

Jehobah Yana Son Ka Yi Masa Biyayya

“Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata.”—MISALAI 27:11.

1. Wane irin hali ne ya cika al’umma a yau?

NEMAN ’yanci da rashin biyayya sun cika duniya a yau. Manzo Bulus ya bayyana dalilin haka a wasiƙarsa zuwa Kiristocin da ke Afisa: “Ku kuma ya rayadda ku, yayinda ku ke matattu ta wurin laifofinku da zunubanku, inda ku ke tafiya a dā bisa ga zamanin wannan duniya, ƙarƙashin sarkin ikon sararin sama, ruhun da ke aikawa yanzu a cikin ’ya’yan kangara.” (Afisawa 2:1, 2) Hakika, kana iya cewa Shaiɗan Iblis, “sarkin ikon sararin sama,” ya shafa wa dukan duniya halin rashin biyayya. Ya yi hakan a ƙarni na farko, kuma ya ci gaba da yin haka sosai tun lokacin da aka kore shi daga sama kafin Yaƙin Duniya na Ɗaya.—Ru’ya ta Yohanna 12:9.

2, 3. Waɗanne dalilai muke da su da za su sa mu yi wa Jehobah biyayya?

2 Mu Kiristoci mun san cewa Jehobah yana bukatar cikakkiyar biyayyarmu domin shi ne Mahaliccinmu, Mai Kiyaye ranmu, Mai ikon Mallaka, kuma Mai Cetonmu. (Zabura 148:5, 6; Ayukan Manzanni 4:24; Kolossiyawa 1:13; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Isra’ilawa na zamanin Musa sun san cewa Jehobah ne Mai ba da Rai kuma Mai Cetonsu. Saboda haka, Musa ya ce musu: “Ku kiyaye ku aika fa kamar yadda Ubangiji Allahnku ya umurce ku.” (Kubawar Shari’a 5:32) Hakika, Jehobah ya cancanci su yi masa biyayya. Amma, nan da nan suka yi rashin biyayya ga Allahnsu.

3 Menene muhimmancin biyayyarmu ga Mahaliccin duka duniya? Allah ya ce annabi Sama’ila ya gaya wa Sarki Saul cewa: “Biyayya ta fi hadaya.” (1 Samuila 15:22, 23) Me ya sa?

Yadda Biyayya “ta Fi Hadaya”

4. Ta yaya ne za mu iya ba Jehobah wani abu?

4 Domin shi ne Mahalicci, Jehobah ne yake da duka abin duniya da muke da shi. Idan haka ne, akwai abin da za mu iya ba shi kuwa? Hakika, muna iya ba shi wani abu mai tamani. Menene abin? Muna iya samun amsar a cikin umurnin da ke gaba: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” (Misalai 27:11) Muna iya ba Allah biyayyarmu. Ko da yake yanayinmu da tushenmu sun bambanta, idan muka yi biyayya, kowanenmu zai iya ba da amsa ga mugun hasashen da Shaiɗan Iblis ya yi cewa mutane ba za su kasance da aminci ga Allah a lokacin wahala ba. Wannan gata ne mai girma!

5. Ta yaya ne rashin biyayya yake shafan Mahalicci? Ka kwatanta.

5 Allah ya damu da irin shawarwarin da muke yi. Idan muka yi rashin biyayya, hakan na shafan shi. Ta yaya? Ransa na ɓaci idan ya ga mutum yana bin tafarki marar kyau. (Zabura 78:40, 41) A ce wani mai ciwon sukari ya ƙi cin abincin da aka ce ya ci kuma ya ci gaba da cin wanda aka ce kada ci. Yaya likitansa zai ji? Mun tabbata cewa Jehobah ba ya jin daɗi sa’ad da mutane suka yi masa rashin biyayya, domin ya san sakamakon ƙin abubuwan da ya ce a yi don a rayu.

6. Menene zai taimaka mana mu yi biyayya ga Allah?

6 Menene zai taimaka wa kowanenmu ya yi biyayya? Ya dace kowanenmu ya roƙi Allah ya ba shi “zuciya mai [biyayya],” kamar yadda Sarki Sulemanu ya yi. Ya yi roƙo a ba shi irin wannan zuciyar domin ya “raba tsakanin nagarta da mugunta” don ya yi wa ’yan’uwansa Isra’ilawa shari’a. (1 Sarakuna 3:9) Muna bukatar “zuciya mai [biyayya]” idan muna son mu raba tsakanin nagarta da mugunta a duniyar da take cike da rashin biyayya. Allah ya ba mu Kalmarsa, littattafan da za su taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki, taron Kiristoci, da kuma dattawa masu kula na ikilisiya saboda mu sami “zuciya mai [biyayya].” Muna amfani da waɗannan tanadodin a hanyoyi masu kyau kuwa?

7. Me ya sa Jehobah ya nanata biyayya fiye da hadayu?

7 Game da wannan, ka tuna cewa a dā Jehobah ya bayyana wa mutanensa na dā cewa biyayya ta fi hadayun dabbobi muhimmanci. (Misalai 21:3, 27; Hosea 6:6; Matta 12:7) Me ya sa haka, tun da yake Jehobah ne ya umurci mutanensa su yi masa irin waɗannan hadayun? Amma, menene muradin mai yin hadayar? Yana yi ne don ya faranta wa Allah rai? Ko kuwa yana yi ne kawai? Idan da gaske wanda ke bauta yana son ya faranta wa Allah rai, zai yi iya ƙoƙarinsa ya yi biyayya ga duka dokokin Allah. Allah ba ya bukatar hadayun dabbobi, amma biyayyarmu ita ce abu mai tamani da za mu iya ba shi.

Wani Misali da Gargaɗi Ne

8. Me ya sa Allah ya ƙi Saul a matsayin sarki?

8 Labarin Sarki Saul da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna muhimmancin yin biyayya. Saul ya soma sarautarsa ne a matsayin mutum mai tawali’u yana ‘ganin kansa ƙanƙani.’ Bayan wani ɗan lokaci, fahariya da tunanin ƙarya suka soma yi wa shawarwarinsa ja-gora. (1 Samuila 10:21, 22; 15:17) Akwai lokacin da Saul zai je ya yaƙi ’yan Filistiya. Sama’ila ya gaya wa sarkin ya jira shi ya zo ya yi hadaya ga Jehobah kuma ya yi masa ƙarin bayani. Amma, Sama’ila bai zo da wuri ba, kuma mutanen suka soma watsewa. Da ganin haka, sai Saul “ya miƙa hadaya ta ƙonawa.” Jehobah bai ji daɗin haka ba. Sa’ad da Sama’ila ya iso, sarkin ya ba da hujjar rashin biyayyarsa, yana cewa domin Sama’ila ya ƙi zuwa da wuri, shi ya sa ya ‘tilasta wa’ kansa ya yi hadaya don ya sami tagomashin Jehobah. Ga Sarki Saul, yin hadaya ya fi muhimmanci fiye da yin biyayya ga umurnin da aka ba shi na jiran Sama’ila ya zo ya yi hadaya. Sama’ila ya ce masa: “Ka yi aikin wauta: ba ka kiyaye umurnin Ubangiji Allahnka ba, wanda ya umurce ka.” Rashin biyayya ga Jehobah ya sa Saul ya yi rashin sarautarsa.—1 Samuila 10:8; 13:5-13.

9. Ta yaya ne Saul ya nuna halin rashin biyayya ga Allah?

9 Sarkin ya koyi darassi daga abin da ya faru kuwa? A’a! Bayan wani lokaci, Jehobah ya umurci Saul ya hallaka al’ummar Amalek, wadda ta kai wa Isra’ila hari haka nan ba dalili. An ce Saul ya kashe har da dabbobi. Ya yi biyayya ta wajen hallaka ‘Amalekawa, tun daga Havilah har zuwa Shur.’ Sa’ad da Sama’ila ya zo ya same shi, sarkin ya yi murna sosai saboda nasarar da ya samu kuma ya ce: “Albarka gareka daga wurin Ubangiji: na cika umurnin Ubangiji.” Akasin umurnai da aka ba su, Saul da mutanensa sun ƙi su kashe Sarki Agag da kuma “mafiya kyau daga cikin tumaki da shanu, da kiyayayyu, da yan raguna, da dukan kyawawan abu.” Sarki Saul ya ba da hujjar rashin biyayyarsa sa’ad da ya ce: “Jama’a suka keɓe mafiya kyau daga cikin tumaki da shanu, domin a yi hadaya ga Ubangiji Allahnka.”—1 Samuila 15:1-15.

10. Wane darassi ne Saul ya ƙi ya koya?

10 Bayan haka, Sama’ila ya ce wa Saul: “Ubangiji yana murna dayawa da hadayu na ƙonawa da sacrifices kuma, kamar yadda ya ke murna da biyayya ga muryar Ubangiji? Ka lura, biyayya ta fi hadaya, jin magana kuma ya fi kitsen raguna.” (1 Samuila 15:22) Tun da yake Jehobah ya ƙudurta cewa za a hallaka waɗannan dabbobin, ba za su dace da hadayu ba.

Ka Yi Biyayya a Dukan Abubuwa

11, 12. (a) Yaya ne Jehobah yake ɗaukan ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na faranta masa rai a bautarmu? (b) Ta yaya ne mutum zai iya ruɗar kansa ta wajen yin tunanin cewa yana yin nufin Allah amma rashin biyayya yake yi?

11 Jehobah yana farin cikin ganin amintattun bayinsa sun kasance da aminci duk da tsanantawa, suna wa’azin Mulki duk da rashin son saƙon da mutane suke nunawa, kuma suna halartar taron Kirista duk da matsin da suke fuskanta na neman abin duniya! Biyayyarmu a waɗannan fasalolin rayuwarmu na ruhaniya suna sa shi farin ciki! Ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na bauta wa Jehobah suna da tamani a wurinsa idan muka yi su cikin ƙauna. Mutane suna iya yin banza da jan aikin da muke yi, amma Allah yana lura da abin da muke yi kuma ba zai manta da su ba.—Matta 6:4.

12 Idan muna son mu faranta wa Allah rai sosai, dole ne mu yi biyayya a duka fasalolin rayuwarmu. Kada mu ruɗi kanmu ta wajen yin tunanin cewa muna iya kauce wa wasu farillan Allah tun da yake muna bauta ma shi. Alal misali, mutum yana iya ruɗar kansa ta wajen yin tunanin cewa idan yana cika wasu farillai na bauta, yana iya guje wa horon yin lalata, ko kuwa yin wasu zunubi masu tsanani. Wannan kuskure ne!—Galatiyawa 6:7, 8.

13. Ta yaya za a iya gwada biyayyarmu ga Jehobah a ɓoye?

13 Saboda haka, muna iya tambayar kanmu, ‘Ina yin biyayya ga Jehobah a ayyukana na yau da kullum, har ma a batutuwa na ɓoye?’ Yesu ya ce: “Wanda ya ke da aminci cikin ƙanƙanin abu mai-aminci ne cikin mai yawa: kuma wanda ba shi da gaskiya cikin ƙanƙanin abu ba, mara-gaskiya ne cikin mai-yawa.” (Luka 16:10) Muna ‘tafiya cikin kamalar zuciya,’ har ma a cikin ‘gidanmu,’ inda wasu ba za su iya ganin mu ba? (Zabura 101:2) Hakika, ana iya gwada amincinmu sa’ad da muke cikin gida. A yawancin ƙasashe inda kwamfuta ta zama kayan gida, yana da sauƙi mutum ya ga hotunan batsa. A ’yan shekarun da suka shige, mutum ba zai iya ganin irin waɗannan hotunan idan bai je inda ake gabatar da nishaɗi na lalata ba. Bari mu tuna da abin da Yesu ya ce: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” Shin, za mu iya ƙin kallon hotunan batsa? (Matta 5:28; Ayuba 31:1, 9, 10; Zabura 119:37; Misalai 6:24, 25; Afisawa 5:3-5) Tashoshin talabijin da suke ɗauke da mugunta fa? Mun yarda da Allahnmu, wanda ransa ba ya son “mai-son zalunci”? (Zabura 11:5) Mugun shan giya a ɓoye fa? Littafi Mai Tsarki ya haramta yin maye, kuma ya gargaɗi Kiristoci su guje wa yawan shan “ruwan anab.”—Titus 2:3; Luka 21:34, 35; 1 Timothawus 3:3.

14. Ta waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna biyayyarmu ga Allah a batutuwan da suka shafi kuɗi?

14 Wani ɓangare kuma da ya kamata mu kasance a faɗake shi ne a batun kuɗi. Alal misali, za mu saka hannu a hanyar samun kuɗi na dare ɗaya mai kama da zamba? Muna jin bin hanyoyin da ba sa bisa doka don mu guje wa biyan haraji? Ko kuwa, muna bin dokar da ta ce “Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu”?—Romawa 13:7; LMT.

Biyayyar da Ake Yi Domin Ƙauna

15. Me ya sa kake yin biyayya ga dokokin Jehobah?

15 Yin biyayya ga dokokin Allah yana kawo albarka. Alal misali, muna iya guje wa wasu cututtuka ta wajen guje wa shan taba, lalata, da kuma daraja tsarkakar jini. Bugu da ƙari, ta wajen yin rayuwa da ta jitu da gaskiyar Littafi Mai Tsarki, za mu iya amfana a tattalin arziki, yadda muke bi da mutane, ko a rayuwar iyalinmu. (Ishaya 48:17) Irin waɗannan amfanin ana iya ɗaukansu albarkar da ake samu idan aka bi dokokin Allah. Duk da haka, ainihin dalilin da ya sa muke yin biyayya ga Jehobah shi ne domin muna ƙaunarsa. Ba ma bauta wa Allah don son kai. (Ayuba 1:9-11; 2:4, 5) Allah ya ba mu ’yancin zaɓar wanda za mu yi wa biyayya. Mun zaɓi mu yi wa Jehobah biyayya domin muna son mu faranta masa rai kuma domin muna son mu yi abin da ya dace.—Romawa 6:16, 17; 1 Yohanna 5:3.

16, 17. (a) Ta yaya ne Yesu ya yi biyayya ga Allah a cikin ƙauna? (b) Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu?

16 Yesu ya kafa misali mai kyau ta wajen yin biyayya ga Jehobah domin yana ƙaunarsa. (Yohanna 8:28, 29) Sa’ad da yake duniya, Yesu ‘ya koyi biyayya ta wurin wahalar da ya sha.’ (Ibraniyawa 5:8, 9) Ta yaya? Yesu “ya ƙasƙantadda kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa, i, har mutuwa ta giciye.” (Filibbiyawa 2:7, 8) Ko da yake Yesu ya yi biyayya a sama, an gwada biyayyarsa a duniya. Mun tabbata cewa Yesu ya cancanta ƙwarai ta kowace hanya ya zama Babban Firist na ’yan’uwansa na ruhaniya da kuma sauran mutanen da suka yi imani da shi.—Ibraniyawa 4:15; 1 Yohanna 2:1, 2.

17 Mu kuma fa? Muna iya yin koyi da Yesu ta wajen mai da yin biyayya ga yin nufin Allah abu na farko a rayuwarmu. (1 Bitrus 2:21) Muna iya samun gamsuwa idan ƙaunar da muke yi wa Allah ta motsa mu mu yi abin da Jehobah ya umurta, har ma a lokacin da aka matsa mana ko aka gwada mu mu yi abin da bai ce ba. (Romawa 7:18-20) Wannan ya haɗa da son yin biyayya ga umurnin da muke samu daga waɗanda suke yin ja-gora a bauta ta gaskiya, duk da cewa su ajizai ne. (Ibraniyawa 13:17) Yin biyayya ga dokokin Allah a rayuwarmu yana da tamani a wurin Jehobah.

18, 19. Cikakkiyar biyayyarmu ga Allah na kawo wane sakamako?

18 A yau, yin biyayya ga Jehobah ya ƙunshi jimre wa tsanantawa don mu kasance da aminci. (Ayukan Manzanni 5:29) Kuma biyayyarmu ga dokar Jehobah na yin wa’azi da koyarwa ya ƙunshi jimrewa har zuwa ƙarshen wannan zamanin. (Matta 24:13, 14; 28:19, 20) Muna bukatar mu ci gaba da jimrewa don mu ci gaba da taruwa da ’yan’uwanmu, duk da cewa muna iya fuskantar matsi daga duniya. Allahnmu mai ƙauna yana sane da ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na yin biyayya a waɗannan fasalolin. Idan muna son mu yi cikakkiyar biyayya, muna bukatar mu yaƙi jikinmu na zunubi kuma mu guje wa mugunta, mu so abin da ke da kyau.—Romawa 12:9.

19 Sa’ad da muka bauta wa Jehobah cikin ƙauna da kuma zuciya da ke cike da godiya, a gare mu zai zama “mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Hadayun da suka dace suna da kyau, amma cikakkiyar biyayya cikin ƙauna ce Jehobah ya fi so.—Misalai 3:1, 2.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa za mu iya cewa muna da wani abu da za mu iya ba Jehobah?

• Waɗanne kurakurai ne Saul ya yi?

• Ta yaya za ka iya nuna cewa ka yarda biyayya ta fi hadaya?

• Menene ke motsa ka ka yi biyayya ga Jehobah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba