Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .
Me Ya Sa Allah Ya Bukaci Masu Bauta Masa Su Auri ’Yan’uwansu Masu Bi Kaɗai?
▪ Dokar Allah ga Isra’ilawa ta ƙunshi wannan umurni game da al’ummai da ke kewaye da su: ‘Ba za ka yi surukuta da su ba; ɗiyarka ba za ka ba ɗansa ba, ba kuwa za ka ɗauka wa ɗanka ɗiyarsa ba.’ (Kubawar Shari’a 7:3, 4) Me ya sa aka ba su wannan umurnin?
Jehobah ya san cewa Shaiɗan yana so ya ɓata mutanensa gaba ɗayansu kuma ya sa su bauta wa allolin ƙarya. Shi ya sa Allah ya gargaɗi mutanensa cewa al’umman za su iya “juyarda ɗanka ga barin bina, domin su bauta wa waɗansu alloli.” Wannan dokar ta ƙunshi abubuwa da yawa. Idan al’ummar Isra’ila ta bauta wa allolin ƙarya, Jehobah ba zai albarkace su ba kuma ba zai taimake su ba sa’ad da suka yi yaƙi da magabtansu kuma hakan zai sa magabtansu su halaka su gaba ɗaya. Idan hakan ya faru, yaya al’ummar za ta fito da Almasihun da aka yi alkawarinsa? Hakika, Shaiɗan zai so ya rinjaye Isra’ilawa su auri mutanen da ba sa bauta wa Allah don ya cim ma burinsa.
Ka tuna cewa Allah yana kula da kowanne cikin mutanensa. Ya san cewa kowannensu zai yi farin ciki kuma zai zauna lafiya idan yana bauta masa da zuciya ɗaya. Shin, Jehobah yana da kyakkyawan dalili ne na gaya wa mutanensa cewa auren waɗanda ba sa bauta masa zai iya gurɓata su? Ka yi la’akari da misalin Sarki Sulemanu. Ya san dokar da Jehobah ya bayar cewa kada a auri mata daga al’umman da ba sa bauta wa Allah. Dokar ta ce: “Za su juyar da zuciyarku ga bin allolinsu.” Wataƙila ya yi tunani cewa wannan dokar da Allah ya bayar ba ta shafe shi ba tun da yake shi mai hikima ne sosai. Ya yi biris da dokar. Mene ne sakamakon hakan? “Matansa suka juyar da zuciyatasa zuwa bin waɗansu alloli.” Hakan abin tausayi ne! Sulemanu ya rasa tagomashin Jehobah, kuma don rashin amincinsa, al’ummar Isra’ila ta rabu.—1 Sarakuna 11:2-4, 9-13.
Wasu za su iya tunanin cewa ba a kowane yanayi ba ne irin auren nan yake da hadari. Alal misali, wani Ba’isra’ile mai suna Mahlon ya auri wata mace mai suna Ruth ’yar Moab, wadda daga baya ta zama mai bauta wa Allah. Amma auren matan Moab yana da hadari sosai. Ba a yaba wa Mahlon don ya auri ’yar Moab ba; ya mutu tun yana da ƙarfinsa, wataƙila kafin Ruth ta zama mai bauta wa Allah Jehobah. Ɗan’uwan Mahlon, mai suna Chilion, ya auri ’yar Moab mai suna Orpah, wadda ta nace wa “allahnta.” Amma, Boaz ya auri Ruth ne shekaru da yawa bayan ta zama mai bauta wa Allah. Shi ya sa daga baya Yahudawa suka ɗauki Ruth a matsayin “fitacciyar mabiya addinin Yahudawa.” Da yake Boaz da Ruth masu bauta wa Jehobah ne kafin su yi aure, Jehobah ya albarkaci aurensu.—Ruth 1:4, 5, 15-17; 4:13-17.
Shin, zai dace ne mu ba da hujja cewa auren Mahlon da Ruth ya ba mu damar auren waɗanda ba sa bauta wa Jehobah? Ba zai dace ba. Alal misali, idan wani ɗan caca ya ci kuɗi mai yawa, hakan yana nufin cewa caca sana’a ce mai kyau? A’a! Hakazalika, auren Ruth da Mahlon ba hujja ba ce na auren waɗanda ba sa bauta wa Jehobah.
Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su auri mai bin “Ubangiji” kaɗai. Kuma ya sake cewa “kada ku yi karkiya marar-dacewa tare da marasa-bangaskiya.” Wannan shawarar ta shafi Kiristoci na gaskiya da suke neman aure. Ga waɗanda suka riga suka auri marasa bauta wa Allah, Littafi Mai Tsarki na ɗauke da shawarwari da za su taimaka musu su shawo kan matsalolin da suke fuskanta. (1 Korintiyawa 7:12-16, 39; 2 Korintiyawa 6:14) Dukan shawarwarin da aka ba da sun nuna cewa Jehobah Allah, wanda ya kafa aure, yana son masu bauta masa su yi farin ciki ko da suna da aure ko a’a.