Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .
Shaidun Jehobah Suna Barin Mata Su Koyar da Mutane Ne?
▪ Hakika, a faɗin duniya, Shaidun Jehobah suna da miliyoyin mata masu koyar da mutane. Waɗannan matan da suke wa’azi game da Mulkin Allah suna da ɗimbin yawa. An yi annabci a cikin Zabura 68:11 game da su cewa: “Ubangiji ya bada sako: Mata masu-shelar bisharan kuwa babbar runduna ne.”
Amma, wa’azin da mata Shaidun Jehobah suke yi hidima ce da ta bambanta da shugabanci da mata suke yi a wasu addinai. Ta yaya suka bambanta?
Mata da suke shugabanci a coci suna koyar da ’yan cocinsu ne. Amma mata Shaidun Jehobah suna koya wa mutane Littafi Mai Tsarki ne sa’ad da suka fita wa’azi gida-gida da kuma a wasu lokatai, ba a cikin ikilisiya ba.
Wata hanya kuma da mata masu hidima a cikin Shaidun Jehobah suka bambanta da mata masu hidima a wasu addinai ita ce a ayyukan da suke yi a cikin ikilisiya. Mata da suke shugabanci a coci suna koyar da ’yan cocinsu daga kan bagadi. Amma mata Shaidun Jehobah ba sa koyarwa a cikin ikilisiya idan akwai maza da suka yi baftisma. Wannan aikin maza da suka cancanta ne kawai.—1 Timotawus 3:2; Yaƙub 3:1.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa maza ne aka ba su aikin koyarwa a cikin ikilisiya. Sa’ad da manzo Bulus yake ba wa Titus umurni, ya ce: “Saboda wannan na bar ka cikin Karita, domin ka . . . kafa dattiɓai kuma cikin kowanne birni. Bulus ya ƙara da cewa kowane ɗan’uwa da aka naɗa ya kasance “marar abin zargi, mai mace ɗaya.” (Titus 1:5, 6) Sa’ad da Bulus yake rubuta wasiƙa ga Timotawus game da ayyuka a cikin ikilisiya, ya ce: “Duk mai burin aikin kula da ikilisiya, yana burin aiki mai kyau ke nan. To, lalle ne mai kula da ikilisiya yā zama marar abin zargi, ya zama mai mace ɗaya, . . . da gwanin koyarwa kuma.”—1 Timotawus 3:1, 2, Littafi Mai Tsarki.
Shin me ya sa aka ba wa maza kawai aikin koyarwa a cikin ikilisiya? Bulus ya amsa cewa: “Amma ban yarda mace ta koyar, ko kuwa ta sami mulki bisa namiji ba, amma ta kasance a kawaice. Gama Adamu aka fara kamantawa, kāna Hawa’u.” (1 Timotawus 2:12, 13) Waɗannan ayoyin sun nuna dalilin da ya sa Allah ya ba wa maza aikin kula da koyarwa.
Shaidun Jehobah suna bin misalin Shugabansu Yesu Kristi. Sa’ad da wani almajirin Yesu mai suna Luka yake bayani game da hidimar Yesu, ya ce Yesu “ya yi ta yawo a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin Allah.” Daga baya, Yesu ya aika almajiransa su je su yi aikin wa’azin nan da ya yi, sai almajiran “suka bibbiya ƙauyuka, suna bishara.”—Luka 8:1; 9:2-6.
Hakazalika a yau, Shaidun Jehobah maza da mata suna cika aikin nan da Yesu ya yi annabcinsa, Yesu ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Matta 24:14.