Ka Koya Daga Kalmar Allah
Mene Ne Zai Faru a Ranar Shari’a?
Wannan talifin ya tattauna tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin tunani a kansu kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Mene ne Ranar Shari’a?
Kamar yadda aka nuna a hoton da yake damar shafin nan, mutane da yawa sun ɗauka cewa Ranar Shari’a, biliyoyin mutane za su tsaya a gaban kursiyin Allah. Kuma za a yi musu shari’a bisa ga abubuwan da suka yi a dā. Bayan haka, wasu za su je sama, wasu kuma za a azabtar da su a jahannama. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an kafa Ranar Shari’a ne domin a ceci mutane daga rashin adalci. (Zabura 96:13) Allah ya naɗa Yesu a matsayin Alƙali wanda zai yi wa mutane adalci.—Ka karanta Ishaya 11:1-5; Ayyukan Manzanni 17:31.
2. Ta yaya za a tabbatar da adalci a Ranar Shari’a?
Mutumi na farko, Adamu, ya yi wa Allah tawaye. Ta hakan, ya yi rashin adalci kuma domin wannan tawayen ne ’yan Adam suke wahala da kuma mutuwa. (Romawa 5:12) Yesu zai daidaita wannan rashin adalci ta wajen ta da biliyoyin mutane daga matattu. Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa hakan zai faru a sarautar Yesu na shekara dubu.—Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 20:4, 11, 12.
Za a yi wa waɗanda aka ta da daga matattu shari’a bisa ga ayyukansu bayan an bayyana abin da ke cikin “littattafai” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna sura 20 ne, ba bisa ga abubuwan da suka yi kafin su mutu ba. (Romawa 6:7) Manzo Bulus ya rubuta cewa za a ta da “masu-adalci da . . . marasa-adalci” daga matattu kuma za a koya musu gaskiya game da Allah.—Ka karanta Ayyukan Manzanni 24:15.
3. Mene ne za a cim ma a Ranar Shari’a?
Waɗanda suka mutu a duhun kai za su koyi abubuwa game da Jehobah Allah don su bauta masa. Hakan zai ba su damar yin canji zuwa mutane masu aikata nagarta. Idan suka yi hakan, tashinsu daga matattu zai zama “tashi na rai.” Amma waɗansu da aka ta da ba za su so su yi nagarta ba. Saboda haka, tashinsu daga matattu zai zama “tashi na [hukunci].”—Ka karanta Yohanna 5:28, 29; Ishaya 26:10; 65:20.
A cikin shekara dubu, Jehobah zai mai da mutanen da suka yi biyayya kamiltattu, kamar yadda iyayenmu na fari suke kafin su yi zunubi. Wannan shi ne Ranar Shari’a. (1 Korintiyawa 15:24-28) Babu shakka, wannan albishiri mai daɗi ne ga dukan masu biyayya. Yayin da hakan yake faruwa, Allah zai ɗaure Shaiɗan Iblis, amma bayan shekaru dubun, zai sāke shi kuma Shaiɗan zai gwada mutane. Wannan shi ne gwaji na ƙarshe. Shaiɗan zai so ya yaudari mutane su daina bauta wa Jehobah. Waɗanda suka ƙi bin Shaiɗan za su tsira kuma za su yi rayuwa har abada a duniya.—Ka karanta Ishaya 25:8; Ru’ya ta Yohanna 20:7-9.
4. Wace ranar shari’a ce kuma za ta amfane ’yan Adam?
Littafi Mai Tsarki ya sake kwatanta wata aukuwa da “ranar shari’a.” Wannan aukuwar ce za ta kawo ƙarshen wannan mugun yanayin da duniya take ciki a yau. Za a halaka dukan mugaye a wannan ranar kamar yadda aka halaka mugaye da Rigyawa a zamanin Nuhu. Abin farin ciki shi ne, za a halaka “marasa bin Allah” bayan haka, adilai za su zauna a duniya, kuma “adalci” zai tabbata a lokacin.—Ka karanta 2 Bitrus 3:6, 7, 13, Littafi Mai Tsarki.
Ka duba shafi na 213 zuwa shafi na 215 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah suka wallafa don ƙarin bayani.
[Hoto a shafi na 24]
“The Last Judgement,” by Gustave Doré, 1832-1883
[Inda Aka Ɗauko Hoto]
Engravings by Doré