Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/1 p. 14
  • Yana Cika ‘Zukatanmu’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yana Cika ‘Zukatanmu’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • “Allah Mai Nagarta Ne da Babu Kamarsa!”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Nagarta​—Ta Yaya Za Mu Koyi Nuna Wannan Halin?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Jehovah—Mafificin Misali Na Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Ci Gaba Da Yin Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/1 p. 14

KA KUSACI ALLAH

Yana Cika ‘Zukatanmu’

Shin Jehobah ya damu da mu da gaske ko kuwa bai damu da matsalolin da muke fuskanta a duniya ba? Amsar da Littafi Mai Tsarki ya bayar tana ƙarfafa mu sosai. Hakika Allah yana kula da ’yan Adam, kuma yana so mu more rayuwa. Yana barin ’yan Adam su more alherinsa kowace rana, har da mutanen da ba sa masa godiya. Ka yi la’akari da kalmomin manzo Bulus.—Karanta Ayyukan Manzanni 14:16, 17.

Sa’ad da Bulus yake yi wa mutanen da ba sa bauta wa Allah magana a birnin Listra, ya ce: “A cikin zamanun da suka wuce [Allah] ya bar dukan al’ummai su yi tafiya cikin nasu tafarku. Amma ba ya bar kansa babu shaida ba, da shi ke yana yin alheri, yana ba ku ruwaye daga sama da kwanukan ƙoshi, yana cika zukatanku da abinci da farin ciki.” Mene ne masu sauraron Bulus suka fahimta daga abin da ya faɗa?

Ba zai yi wa mutanen Listra wuya su fahimci abin da Bulus yake nufi ba. Su manoma ne kuma ƙasarsu mai albarka ce, mai dausayi. Amma kamar yadda Bulus ya tuna musu, Allah ne ke ba da ruwan sama da kuma damina mai albarka. Saboda haka, a duk lokacin da amfanin gonarsu ya yalwata kuma duk sa’ad da suka ci abinci mai daɗi, suna morar alherin Allah ne.

Abin da Bulus ya faɗa wa mutanen Listra yana koya mana darussa masu amfani sosai game da Jehobah.

Jehobah ya ba mu ’yanci. Ka lura cewa Jehobah ya bar mutanen dukan al’ummai “su yi tafiya cikin nasu tafarku.” Wani littafin bincike da mafassaran Littafi Mai Tsarki suke amfani da shi ya ce wannan furucin yana nufin “yin abin da suka ga dama” ko kuma “yin abin da a ganinsu ya fi dacewa.” Jehobah ba ya tilasta wa kowa ya bauta masa. Ya ba mu ’yanci na zaɓan yadda muke so mu yi rayuwa.—Kubawar Shari’a 30:19.

Jehobah yana so mu san shi. Bulus ya bayyana cewa bai “bar kansa babu shaida ba.” Wannan littafin bincike da aka ambata ɗazu ya ce wannan furucin yana iya nufin cewa “Allah ya bayyana halinsa wa mutane a fili.” Abubuwa da Allah ya halitta suna ba da tabbaci mai kyau game da “al’amura nasa da ba su ganuwa,” haɗe da alherinsa da hikimarsa da ikonsa da kuma ƙaunarsa. (Romawa 1:20) Hakika, Jehobah ya bayyana kansa a cikin Littafi Mai Tsarki. (2 Timotawus 3:16, 17) Hakan ya nuna cewa yana so mu san shi, ko ba haka ba?

Yana barin ’yan Adam su more alherinsa kowace rana, har da mutanen da ba sa masa godiya

Jehobah yana so mu yi farin ciki. Bulus ya ce Allah ‘yana cika zukatanmu da abinci da farin ciki.’ Mai zunubi da bai yi imani da Jehobah ba ma yana iya cin abinci ya ƙoshi kuma ya ɗan yi farin ciki a rayuwa. Amma, Allah yana so mu more farin ciki na gaske kuma mu yi hakan har abada. Hakan zai iya faruwa ne idan muka koyi gaskiya game da shi kuma mun bi abin da muka koya don kyautata rayuwarmu.—Zabura 144:15; Matta 5:3.

A kowace rana, muna more alheri daga wurin Jehobah. Muna ƙarfafa ka ka ƙara koyan hanyoyin da za ka iya nuna wa Allah cewa kana godiya, da yake shi ne ke cika zuciyarka da “abinci da farin ciki.”

Karatun Littafi Mai Tsarki na watan Satumba

1 Korintiyawa-2 Korintiyawa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba