TATTAUNAWA TSAKANIN SHAIDUN JEHOBAH DA MUTANE
Allah Ya Damu da Wahalar da Muke Sha Kuwa?
Tattaunawar da ke gaba misali ne na yadda Shaidun Jehobah suke yi wa mutane wa’azi. A ce wata Mashaidiya mai suna Michelle ta ziyarci wata mata mai suna Sophia.
ME YA SA ALLAH YA ƘYALE WANNAN ABIN YA FARU?
Michelle: Na yi farin cikin haɗuwa da ke. Sunana Michelle ne.
Sophia: Nawa sunan kuma Sophia ne.
Michelle: Yau mun ziyarci unguwarku ne don mu rarraba wa mutane wannan warƙar, Za Ka So Ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? Barin in ba ki taki.
Sophia: Game da addini ne?
Michelle: E. Ki lura da tambayoyi guda shida da ke bangon gaba. Waɗanne ne cikin waɗannan tambayoyin—
Sophia: Dakata. Kada ki ɓata lokacinki da ni.
Michelle: Me ya sa kika faɗa haka?
Sophia: A gaskiya, ban yi imani da Allah ba.
Michelle: Na yi farin ciki da kika faɗa mini gaskiya. Ba wai ina so in tilasta miki ki amince da ra’ayina ba ne, so-in-sani ne kawai da ni. Kin daɗe da kasancewa da wannan ra’ayin ne?
Sophia: A’a. A dā ni mai bin addini ne. Amma yanzu ban yarda cewa Allah ya wanzu ba.
Michelle: Haba! Me ya sa kika daina imani da Allah?
Sophia: Mahaifiyata ta yi haɗarin mota shekaru 17 da suka shige.
Michelle: Ayya, sannu. Ta ji ciwo sosai ne?
Sophia: Hakika, kuma ta naƙasa tun lokacin.
Michelle: A gaskiya wannan abin baƙin ciki ne.
Sophia: Ƙwarai, hakan ya sa ni baƙin ciki sosai. Idan har akwai Allah, me ya sa ya ƙyale irin wannan abin ya faru? Me ya sa Allah yake ƙyale mu mu sha wahala haka?
LAIFI NE MUTUM YA TAMBAYI DALILIN DA YA SA MUKE SHAN WAHALA?
Michelle: Ba laifi ba ne mutum ya yi baƙin ciki ko kuma ya yi irin wannan tambayar. Sa’ad da muke shan wahala, mukan so mu san dalilin hakan. Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da waɗansu bayin Allah maza da mata masu aminci da suka yi irin wannan tambayar.
Sophia: Da gaske?
Michelle: Hakika. Bari in nuna miki wani misali daga cikin Littafi Mai Tsarki.
Sophia: To.
Michelle: Ki lura da abubuwan da annabi Habakkuk ya tambayi Allah kamar yadda aka rubuta a Habakkuk, sura 1, ayoyi 2 da 3: “Ya Ubangiji, har yaushe zan yi kira, kai kuwa ba ka yarda ka ji ba? Ina ta da murya gareka saboda zafin mugunta, kai kuwa ka ƙi yin ceto. Don me kake nuna mini saɓo?” Shin kin taɓa yin irin waɗannan tambayoyin ne?
Sophia: E.
Michelle: Allah bai tsawata wa Habakkuk don waɗannan tambayoyin da ya yi ba, kuma bai gaya masa cewa yana bukata ya ƙarfafa bangaskiyarsa ba.
Sophia: Da kyau.
JEHOBAH YA TSANI YA GA MUTANE SUNA SHAN WAHALA
Michelle: Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa Allah ya san irin wahalar da muke sha kuma ya damu da hakan.
Sophia: Me kike nufi?
Michelle: Bari in nuna miki wani misali daga cikin littafin Fitowa 3:7. Don Allah ki karanta mana ayar.
Sophia: To. Ayar ta ce: “Ubangiji kuma ya ce masa, Hakika na ga ƙuncin mutanena waɗanda ke cikin Masar, na kuwa ji kukarsu saboda shugabanninsu na haraji; gama na san baƙin zuciyarsu.”
Michelle: Mun gode da karatu. Bisa ga wannan ayar, shin a ganinki Allah yana ganin duk lokacin da mutanensa suke shan wahala ne?
Sophia: E, yana gani.
Michelle: Ba wai yana ganin abin da ke faruwa ne kawai ba. Ki sake duba kalmomin da ke ƙarshen ayar. Allah ya ce: “Na san baƙin zuciyarsu.” Shin waɗannan kalmomin ba su nuna mana cewa Allah ya damu da mu ba?
Sophia: Hakika, sun nuna cewa Allah ya damu da mu da gaske.
Michelle: Ba wai Allah yana kallon mu kawai sa’ad da muke shan wahala ba, amma yana damuwa da mu har ya yi baƙin ciki sa’ad da muke fuskantar matsaloli.
Sophia: Na yarda da ke.
Michelle: Bari mu karanta wani misali dabam da ya nuna yadda Allah ya ji sa’ad da mutanensa suke shan wahala a Ishaya 63:9. Sashe na farko ya ce: “Cikin dukan ƙuncinsu ya ƙuntata.” Shin, kina ganin Allah ya damu ne a lokacin da mutanensa suka sha wahala?
Sophia: Hakika.
Michelle: Sophia, gaskiyar ita ce, Allah yana ƙaunar mu sosai kuma ba ya jin daɗi sa’ad da muke shan wahala. Idan muna baƙin ciki, yana baƙin ciki tare da mu.
ME YA SA YA ƘI ƊAUKAN MATAKI HAR YANZU?
Michelle: Kafin in tafi, bari in nuna miki wani abu.
Sophia: Me ke nan?
Michelle: Ki lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da iko da Allah yake da shi. Don Allah ki karanta mana Irmiya 10:12.
Sophia: To. Wurin ya ce: “Ta wurin ikonsa ya yi duniya, ta wurin hikimarsa ya kafa duniya, ta wurin fahiminsa kuma ya shimfiɗa sammai.”
Michelle: Na gode. Bari mu ɗan tattauna ayar. Babu shakka, ba ƙaramin iko ba ne Allah ya yi amfani da shi wajen halittar sararin samaniya da duniya da kuma dukan abubuwan da ke ciki, ko ba haka ba?
Sophia: Haka ne.
Michelle: Idan Allah ne ya halicci dukan abubuwan da muke gani da ikonsa, shin hakan bai nuna cewa yana da ikon sarrafa abubuwan da ya halitta ba?
Sophia: Hakika.
Michelle: Ki sake yin tunanin mahaifiyarki. Me ya sa wahalar da take sha yake sa ki baƙin ciki?
Sophia: Domin ita mahaifiyata ce, kuma ina ƙaunar ta.
Michelle: A ce kina da ikon warkar da ita, da ba ki yi hakan ba?
Sophia: Me zai hana?
Michelle: Ki yi tunanin abin da hakan yake nufi. Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa Allah yana ganin wahalar da muke sha, ya damu da mu, kuma yana da iko marar iyaka. Kin yi tunanin yawan haƙurin da Allah yake da shi da ya sa bai kawar da shan wahala nan da nan ba?
Sophia: Ban taɓa yin tunanin wannan ba.
Michelle: Kina ganin akwai kyakkyawan dalilin da ya sa Allah ya ƙyale mu muna shan wahala har yanzu?a
Sophia: Hmm, wataƙila fa.
Michelle: Na ji kamar ana miki waya, zan dawo wata rana don mu ci gaba da tattaunawar.
Sophia: Na gode. Sai wata rana.b
Ka taɓa tunanin wani abu da za ka so ka sami ƙarin bayani a kai daga cikin Littafi Mai Tsarki? Kana son ka ƙara sanin wasu koyarwar Shaidun Jehobah ko kuma dalilin da ya sa suka yi imani da wasu abubuwa? Idan haka ne, ka nemi ƙarin bayani daga Shaidun Jehobah. Za su yi farin ciki su tattauna waɗannan batutuwan da kai.
a Don ƙarin bayani, ka duba babi na 11 a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.
b Wani talifi a gaba a cikin wannan jerin talifofi zai tattauna dalilin da ya sa Allah ya ƙyale shan wahala.