Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 10/15 pp. 3-6
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai a Kasar Taiwan

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai a Kasar Taiwan
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SUN SHAIDA FARIN CIKIN YIN WA’AZI
  • GWAGWARMAYA DA SABON YARE
  • YIN AIKI DON BIYAN BUKATU FA?
  • “KA MORE HIDIMARKA”
  • NEMAN WURIN YIN HIDIMA
  • “HAR NA KASANCE DA AMFANI A GARE SU!”
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ba Mu Taba Kin Aikin da Jehobah Ya Ba Mu Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ta Yaya Za Mu “Dandana” Alherin Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Za Ka Iya “Ƙetaro Zuwa Makidoniya”?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 10/15 pp. 3-6

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai—A Ƙasar Taiwan

WASU ma’aurata masu suna Choong Keon da Julie, ’yan shekaru wajen 34 zuwa 36, sun yi hidimar majagaba shekaru biyar da suka shige a birnin Sydney, a ƙasar Ostareliya. Choong Keon ya ce: “Mun yi aiki jifa-jifa kuma mun ji daɗin rayuwa. Ƙari ga haka, yanayin wurin da muke da zama yana da kyau kuma muna rayuwa mai sauƙi. Mun ji daɗin kasancewa da iyalanmu da kuma abokanmu.” Duk da haka, Choong Keon da Julie ba su gamsu ba. Me ya sa? Sun san cewa yanayinsu zai iya ba su damar ƙara ƙwazo a hidimar Jehobah, amma suna jinkiri ɗaukan matakai don su yi hakan.

Da suka halarci wani babban taro a shekara ta 2009, wani jawabi da aka bayar ya sosa ransu sosai. Mai ba da jawabin ya mai da hankali ga waɗanda za su iya ƙara ƙwazo a hidimarsu. Ya ce: “Ka yi tunanin wannan misalin: Direba zai iya juya motarsa zuwa hagu ko dama ne kawai sa’ad da motar take tafiya. Hakazalika, Yesu zai yi mana ja-gora wajen faɗaɗa hidimarmu ne kawai idan muna tafiya, wato, idan muna yin iya ƙoƙarinmu don mu cim ma maƙasudinmu.”a Ma’auratan sun ga kamar mai jawabin da su yake yi. Har ila a wannan taron, an gana da wasu ma’aurata masu wa’azi a ƙasar waje da suke yin hidima a ƙasar Taiwan. Sun ce suna jin daɗin hidimarsu kuma sun ƙara da cewa ana bukatar masu shela a wurin har ila. Choong Keon da Julie sun ji kamar da su ake yi har ila.

Matarsa Julie, ta ce: “Bayan da muka halarci taron, mun yi addu’a sosai ga Jehobah ya taimaka mana mu ɗauki matakai don mu je hidima a ƙasar Taiwan.” Ta ƙara da cewa: “Amma mun yi fargaba. Don muna ganin kanmu kamar waɗanda ba su iya iyo ba da suke so su yi tsalle su faɗa cikin kogi a ɓangare mai zurfi.” Nassin da ya motsa su suka ɗauki matakin shi ne Mai Wa’azi 11:4, da ya ce: “Shi wanda ya lura da iska ba za ya shuka ba: kuma wanda ya kula da gizagizai ba za ya yi girbi ba.” Choong Keon, ya ce: “Mun ƙudura mu daina ‘kula da lura,’ wato jinkiri kuma mu soma ‘shuki da girbi.’” Sun yi addu’a sosai ga Jehobah kuma sun karanta labaran masu hidima a ƙasar waje. Ƙari ga haka, sun tuntuɓi waɗanda suke yin hidima a ƙasar Taiwan don su sami bayani game da yadda rayuwa take a can. Sai suka sayar da motocinsu kuma bayan wata uku suka ƙaura zuwa ƙasar Taiwan.

SUN SHAIDA FARIN CIKIN YIN WA’AZI

A yau, ’yan’uwa maza da mata fiye da 100 daga wasu ƙasashe sun ƙaura zuwa Taiwan don su yi hidima a wuraren da ake bukatar masu shela a ƙasar. Waɗannan ’yan’uwa ’yan shekaru 21 zuwa 73, sun ƙauro daga ƙasashen Ostareliya da Biritaniya da Kanada da Faransa da Japan da Koriya da Sifen da kuma Amirka. A cikin waɗannan ’yan’uwa akwai mata marasa aure fiye da 50. Mene ne ya taimaka wa waɗannan ’yan’uwa maza da mata masu ƙwazo su je hidima a wata ƙasa? Bari mu bincika.

Wata ’yar’uwa marar aure mai suna Laura, daga ƙasar Kanada, tana hidimar majagaba a yammacin ƙasar Taiwan. Kafin shekara goma da suka shige, ba ta jin daɗin wa’azi ko kaɗan. Laura ta ce: “Da yake ba na daɗewa a wa’azi, ban ƙware ba don hakan ba na jin daɗinsa.” Sai abokanta a Kanada suka gayyace ta zuwa Meziko don su yi wa’azi tare na wata ɗaya. Ta ƙara da cewa: “Wannan ne karo na farko da na daɗe a wa’azi kuma abin mamaki, na ji daɗin wa’azi!”

Daɗin hidima da Laura ta ji a Meziko ya sa ta tunanin zuwa wata ikilisiya da ake wani yare a ƙasar Kanada. Ta soma koyan yaren China da kuma hidima a wani rukunin da suke yin yaren, sai ta tsai da shawarar zuwa Taiwan. Abin da ta yi ke nan a watan Satumba na shekara ta 2008. Laura ta ce: “Na yi shekara ɗaya kafin in saba da wurin, amma yanzu ba na son in koma Kanada.” Yaya take ji game da wa’azi? Ta ce: “Ina jin daɗinsa yanzu. Ganin waɗanda kake yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su suna canja salon rayuwarsu yayin da suke koyo game da Jehobah, abin farin ciki ne. Hidima a ƙasar Taiwan tana sa ni farin ciki saboda wannan canji da mutane suke yi.”

GWAGWARMAYA DA SABON YARE

Wasu ma’aurata da ke tsakanin shekara 34 zuwa 36 masu suna Brian da Michelle, sun je ƙasar Taiwan shekaru takwas da suka shige. Ba su ji daɗin wa’azi ba da farko. Amma wani ƙwararren mai wa’azi a ƙasar waje ya gaya musu cewa: “Ko da ’yar warƙa ce kaɗai kuka ba wani, ya kamata ku tuna cewa wataƙila shi ne ƙaro na farko da ya soma jin wani abu game da Jehobah. Don haka, aikin da kuke yi a wa’azi yana da muhimmanci!” Wannan furucin ya ƙarfafa Brian da Michelle su ci gaba da hidima. Wani ɗan’uwa kuma ya gaya musu: “Idan kuna gwada ci gabanku a kowane babban taro a maimakon kowace rana, ba za ku yi sanyin gwiwa ba.” Hakika, sun sami ci gaba kuma suna ƙwarewa a hidimar majagaba.

Mene ne zai motsa ka ka soma koyan wani yare? Ka yi ƙoƙari ka ziyarci ƙasar da za ka so ka je hidima. Ka halarci taronsu, ka yi abota da ’yan’uwan kuma ka fita wa’azi tare da su. Brian ya ce: “Bayan ka lura cewa mutane da yawa suna jin saƙon Mulkin kuma ka ga yadda ’yan’uwan suke ƙaunarka, hakan zai sa ka je wata ƙasa don ka yi hidima.”

YIN AIKI DON BIYAN BUKATU FA?

’Yan’uwa da yawa da suka je hidima a wuraren da ake bukatar masu shela sun biya bukatunsu ta wurin koyar da Turanci. Kristin da Michelle suna sana’ar kifi don su sami abin biyan bukata. Kristin ya ce: “Ban taɓa yin wannan sana’ar ba, amma ta taimaka mini in ci gaba da hidima a ƙasar.” Bayan wani lokaci, Kristin ya sami wasu masu ciniki. Wannan sana’ar tana taimaka masa ya biya bukatunsa da na matarsa. Ƙari ga haka, tana ba su damar yin aikin da ya fi muhimmanci, wato hidimar majagaba.

“KA MORE HIDIMARKA”

William da Jennifer, wasu ma’aurata daga Amirka, sun ƙaura zuwa ƙasar Taiwan shekaru bakwai da suka shige. William ya ce: “Koyan yaren da yin hidimar majagaba da hidima a cikin ikilisiya da kuma yin aiki don biyan bukata sukan gajiyar da mu a wani lokaci.” Mene ne ya taimaka musu su yi nasara da kuma farin ciki? Sun kafa maƙasudai da za su iya cim ma. Alal misali, da yake ba su da dogon buri sa’ad da suke koyan yaren China, ba su karaya ba a lokacin da koyan yaren ya yi wuya.

William ya tuna cewa wani mai kula mai ziyara ya taɓa gaya masa cewa bayan mun kafa maƙasudi a ibadarmu, ya kamata mu yi farin ciki sa’ad da muke ɗaukan matakai don mu cim ma maƙasudin. Bin wannan shawarar ya taimaka wa William da matarsa su saba da yanayin wurin, su karɓi shawara daga ’yan’uwa da suka manyanta a yanki kuma su daidaita ra’ayinsu don su ji daɗin hidimarsu a ƙasar. Ya ƙara da cewa: “Ƙari ga haka, ya taimaka mana mu keɓe lokaci don mu fita yawo kuma mu ji daɗin kallon halittu a wannan tsibirin da muke yin hidima.”

Kamar yadda William da Jennifer suka ji, Megan, wata majagaba marar aure ’yar Amirka, tana jin daɗin hidimar da take yi sa’ad da take ƙoƙarin cim ma burinta na iya yaren China. Kowane mako tana zuwa wa’azi tare da wani rukunin masu shela da suke yin wa’azi a wani yankin da ake son saƙonmu, wato tashar jirgin ruwa mafi girma a ƙasar Taiwan da ke birnin Kaohsiung. Megan takan shiga jiragen ruwan don ta yi wa’azi ga masu kama kifi da suka zo daga ƙasashen Bangladesh da Indiya da Indonisiya da Filifin da Thailand da kuma Vanuatu. Ta ce: “Da yake masuntan ba sa daɗewa a tashar, muna soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su nan da nan. Don in iya yin nazari da dukansu, nakan yi nazari da mutane huɗu ko biyar a lokaci ɗaya.” To, koyan yaren China da take yi kuma fa? Ta ce: “Da so samu ne, da na so in iya yaren da sauri, amma na tuna da abin da wani ɗan’uwa ya gaya mini, ‘Idan kika yi iya ƙoƙarinki, Jehobah zai albarkace ki.’”

NEMAN WURIN YIN HIDIMA

Kafin wata ’yar Biritaniya mai suna Cathy, ta je hidima a wata ƙasa, ta yi bincike sosai game da ƙasar da ta dace da mata marasa aure. Ta yi addu’a ga Jehobah kuma ta aika wasiƙu zuwa ofisoshin reshe na wasu ƙasashe don ta sami bayani a kan matsalolin da mata marasa aure za su iya fuskanta. Bayan haka, sai ta yi tunani sosai a kan amsoshin da aka ba ta, kuma daga baya, ta kammala cewa zai dace ta je ƙasar Taiwan.

A shekara ta 2004, sa’ad da Cathy take da shekara 31, ta ƙaura zuwa Taiwan kuma ta sauƙaƙa rayuwarta a can. Ta ce: “Na tambayi ’yan’uwa da ke yankin su nuna mini inda zan riƙa sayan ’ya’yan itatuwa da kuma ganye a farashi mai sauƙi. Shawarar da suka ba ni ya sa kuɗina ya yi auki.” Mene ne ya taimaka mata ta yi rayuwa mai sauƙi? Cathy ta ce: “Ina yin addu’a ga Jehobah kullum don ya taimaka mini in gamsu da abinci da kuma sutura masu sauƙi. Na ga cewa Jehobah ya amsa mini addu’o’ina ta wurin taimaka mini in kasance da wadar zuci ko da yake ba na samun dukan abubuwan da nake so.” Ta daɗa da cewa: “Ina jin daɗin irin salon rayuwa da nake yi don hakan yana taimaka mini in mai da hankali ga hidimata da kuma dangantakata da Jehobah.”

Cathy tana jin daɗin rayuwa mai sauƙi da take yi. Ta bayyana cewa: “Yanzu ina yin wa’azi a wuraren da mutane da yawa suke son saƙon bisharar. Hakan yana sa ni farin ciki sosai!” Ikilisiyoyin yaren China biyu ne kawai a birnin da Cathy ta soma hidimar majagaba sa’ad da ta ƙaura zuwa ƙasar Taiwan, amma yanzu suna da ikilisiyoyi bakwai. Cathy ta ce: “Ganin yadda ikilisiyoyin nan suka girma da kuma yadda na saka hannu a yin wannan aikin wa’azi da ke kama da girbi yana sa ni farin ciki sosai!”

“HAR NA KASANCE DA AMFANI A GARE SU!”

Wane sakamako ne Choong Keon da matarsa Julie, da aka ambata a farkon wannan talifin suka samu? Da farko, Choong Keon ya ɗauka ba shi da amfani a ikilisiyar don bai iya yaren China sosai ba. Amma ’yan’uwa da ke ikilisiyar ba sa ganin haka. Choong Keon ya ce: “A matsayin bawa mai hidima, an ba ni wasu ƙarin ayyuka a lokacin da muka rabu zuwa ikilisiyoyi biyu. A lokacin ne na ji kamar ina hidima a inda ake bukatar masu shela sosai.” Da farin ciki ya ce: “Akwai bukata sosai, har na kasance da amfani a gare su!” A yanzu yana hidima a matsayin dattijo. Matarsa Julie ta daɗa da cewa: “Muna ganin mun cim ma wani abu mai kyau, mun sami gamsuwa kuma muna farin ciki matuƙa. Mun zo nan don mu taimaka ne, amma ganin sakamako mai kyau da muka samu, muna ganin mu ne aka taimaka wa. Mun gode wa Jehobah da ya sa muka zo hidima a nan!”

A ƙasashe da yawa, ana bukatar ƙarin masu shela don wannan aikin. Shin ka kusan gama makaranta kuma kana tunanin irin aikin da za ka yi? Shin kai marar aure ne kuma kana son ƙungiyar Jehobah ta yi amfani da kai sosai? Kana son iyalinka ta yi farin ciki don abubuwan da suka cim ma a bautarsu ga Jehobah? Ka yi ritaya kuma kana da ƙwarewar da za ta amfani mutane? Za ka kasance da tabbaci cewa, idan ka daɗa ƙwazo a hidimarka ta wurin zuwa inda ake bukatar masu shela, Jehobah zai albarkace ka sosai.

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2012, shafi na 10, sakin layi na 7-8.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba