Za Ka Iya “Ƙetaro Zuwa Makidoniya”?
1. Me ya sa Bulus da abokan hidimarsa suka je Makidoniya?
1 Kusan shekara ta 49 A.Z., manzo Bulus ya bar ƙasar Suriya ta Antakiya don wa’azinsa na ƙasashen waje na biyu. Maƙasudinsa shi ne ya ziyarci Afisa da kuma wasu birane a Asiya Ƙarami. Ta wurin ruhu mai tsarki an nuna masa wahayi kuma aka gaya masa ya “ƙetaro zuwa Makidoniya,” maimakon zuwa waɗannan wuraren. Shi da abokan hidimarsa sun amince da hakan da farin ciki, kuma sun samu gatar kafa ikilisiya ta farko a yankin. (A. M. 16:9, 10; 17:1, 2, 4) A yau, ana bukatar masu aikin girbi sosai a yankuna da yawa a dukan duniya. (Mat. 9:37, 38) Za ka iya taimakawa kuwa?
2. Me ya sa wasu ba sa son su ƙaura zuwa wata ƙasa?
2 Wataƙila kana da ƙwazon yin wa’azi a ƙasashen waje irin na Bulus, amma ba ka taɓa yin tunani sosai a kan ƙaura zuwa wata ƙasa ba. Wataƙila ba zai yiwu ka halarci Makarantar Koyar da Masu Wa’azi a Ƙasashen Waje ba domin shekarunka ko wataƙila domin ba ki yi aure ba ko kuna da ƙananan yara. Wataƙila kuma ba ka son ka ƙaura zuwa wata ƙasa domin kana shakka ko za ka iya koyon wani harshe. Ko kuma matsalar kuɗi ta sa ka koma wata ƙasa kuma saboda haka ba ka son ka sake ƙaura. Amma, bayan ka yi addu’a sosai a kan batun, za ka iya ganin cewa waɗannan dalilan ba za su iya hana ka ƙaura zuwa ƙasar da ake bukatar masu shela ba.
3. Me ya sa ba lallai sai ka halarci makarantar koyar da masu wa’azi a ƙasar waje kafin ka yi wa’azi a wata ƙasa ba?
3 Dole ne Sai An Horar da Mutum a Matsayin Mai Wa’azi a Ƙasar Waje? Me ya taimaki Bulus da abokan wa’azinsa su yi nasara? Sun dogara ga Jehobah da kuma ruhunsa mai tsarki. (2 Kor. 3:1-5) Saboda haka, ko da yanayinka bai ƙyale ka samu wannan koyarwa ta musamman ba, za ka iya yin nasara wajen yin wa’azi a wata ƙasa. Ka kuma tuna cewa ana koyar da kai kullum a Makarantar Hidima ta Allah da Taron Hidima. Kuma idan kana da maƙasudin halartar Makarantar Gileyad ko kuma irin wannan makarantar, ƙaura da za ka yi zuwa wata ƙasa a matsayin mai wa’azi a ƙasar wajen zai sa ka samu ƙwarewar da za ta amfane ka sosai a nan gaba sa’ad da aka gayyace ka don ka halarci ɗaya daga waɗannan makarantun.
4. Me ya sa bai kamata tsofaffi su yi watsi da batun ƙaura zuwa wata ƙasa don yin wa’azi ba?
4 Tsofaffi: Tsofaffi masu ruhaniya sosai da suka manyanta da ba su da ciwo mai tsanani za su iya yin taimako a ƙasashen da akwai bukata. Shin ka yi ritaya daga aikinka? Wasu da suke karɓan fensho da suka ƙaura zuwa ƙasashen da suke tasowa, inda kayayyaki da kuma kuɗin jinya ba su da tsada sosai, suna iya ciyar da kansu da waɗannan kuɗaɗen fiye da a ƙasar su.
5. Ka faɗi labarin wani ɗan’uwan da ya yi ritaya da ya ƙaura zuwa wata ƙasa.
5 Wani ɗan’uwa daga ƙasar da ake Turanci, wanda dattijo ne da kuma majagaba, ya ƙaura zuwa wani yanki a Kudancin Asiya inda masu yawon shaƙatawa suke yawan zuwa don ya taimaki wani rukunin da ake Turanci da akwai masu shela guda tara. Rukunin suka yi wa baƙi 30,000 da suke zama a yankin wa’azi. A cikin shekara biyu, mutane 50 sun soma halartar taro. Ɗan’uwan ya rubuta: “Ƙaura zuwa wurin nan ya sa na more albarka mafi kyau. Na samu albarka da yawa sosai!”
6. Ka ba da labarin wata ’yar’uwa mara aure da ta ƙaura zuwa wata ƙasa da akwai bukata sosai.
6 ’Yan’uwa Mata Marasa Aure: Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa mata a hanyoyi masu yawa don yaɗa bishara a ƙasashen da akwai bukata sosai. (Zab. 68:11) Wata ’yar’uwa marar aure tana da muradin faɗaɗa hidimarta a wata ƙasa, amma iyayenta sun damu da zaman lafiyarta. Sai ta zaɓi ƙasar da akwai zaman lafiya kuma ba tsadar kaya, ta rubuta wa ofishin reshe, kuma aka aika mata da takamammun bayanan da za su taimake ta. Ta more albarka da yawa a cikin shekaru shida da ta yi hidima a ƙasar. Ta ce: “Da zan samu zarafin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki kalila da a ce ina gida. Amma yin hidima a inda akwai bukata sosai ya sa na samu gudanar da nazarin da yawa kuma na kyautata koyarwarta sosai.”
7. Ka ba da labarin wata iyali da ta ƙaura zuwa wata ƙasa.
7 Iyalai: Idan kana da yara, shin za su iya hana ka ƙaura zuwa wata ƙasa don yaɗa bishara sosai? Wata iyali da suke da yara biyu, ɗaya mai shekara goma ɗaya kuma takwas, sun gwada hakan. Mahaifiyar ta rubuta labarinsu: “Muna farin ciki don mun yi renon yaranmu a nan, domin suna cuɗanya da majagaba na musamman da masu wa’azi a ƙasashen waje. Yin hidima a inda akwai bukata sosai ya sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana sosai.”
8. Zai yiwu a yi hidima a wata ƙasa ba tare da koyon sabon yare ba? Ka bayyana.
8 Damuwa Game da Yare: Shin koyon sabon yare yana hana ka ƙaura zuwa wata ƙasa? Wataƙila ana yarenku a wasu ƙasashen da akwai bukatar masu wa’azin Mulki sosai. Wasu ma’aurata da suke Turanci sun ƙaura zuwa wata ƙasa da ake Sifanisanci da akwai baƙi da yawa daga wata ƙasa da suke Turanci. Bayan da ofishin reshe ya aika musu jerin sunayen ikilisiyoyi na Turanci da suke da bukata, sai suka zaɓi ɗaya kuma suka ziyarci ikilisiyar sau biyu. Suka koma gida, rage kashe kuɗin da suke yi a kowane wata kuma suka yi shekara guda suna tara kuɗi. Sa’ad da suka yi shirin ƙaura, ’yan’uwan da ke yankin suka samo musu gida mai araha.
9, 10. Mene ne ya kamata waɗanda suka ƙaura zuwa wata ƙasa su yi tunani a kai, kuma me ya sa?
9 Baƙi daga Wata Ƙasa: Shin ka koyi gaskiya ne bayan ka ƙaura zuwa wata ƙasa? Wataƙila akwai bukata na masu girbi sosai a ƙasarku. Za ka iya yanke shawarar koma gida don ka taimaka? Mai yiwuwa, zai fi kasance maka da sauƙi ka samu masauƙi da kuma aiki a wurin fiye da baƙo tun da ƙasarku ne. Kuma wataƙila kana jin yaren ƙasar. Ƙari ga hakan, ƙila mutane za su fi son su saurare ka fiye da wanda ba ɗan ƙasa ba.
10 Wani mutum ya yi gudun hijira daga Albaniya zuwa Italiya, ya samu aiki mai kyau, kuma yana aika wa iyalinsa kuɗi a Albaniya. Bayan ya karɓi gaskiya, sai ya soma koya wa wasu majagaba na musamman ’yan Italiya da suke son zuwa hidima a Albaniya yaren Albaniya. Ɗan’uwan ya rubuta: “Suna son su ƙaura zuwa yankin da na bari. Ba su san yaren ba amma sun yi ɗokin zuwa wurin. Ni cikakken ɗan Albaniya ne. Na tambayi kaina, Mene ne nake yi a Italiya?” Ɗan’uwan ya yanke shawarar koma Albaniya don ya taimaka wajen yaɗa bishara. Ya ce: “Shin ina nadama don na bar aiki da kuɗi a Italiya? Ko kaɗan! Na samu aiki na ƙwarai a Albaniya. A gani na, aikin da ya fi muhimmanci kuma yake sa farin ciki sosai shi ne bauta wa Jehobah da dukan dukiyarmu!”
11, 12. Mene ne ya kamata waɗanda suke son su ƙaura zuwa wata ƙasa su yi?
11 Yadda Za a Yi Hakan: Kafin Bulus da abokan aikinsa su je Makidoniya, sun so su nufi yamma, amma “Ruhu Mai-tsarki ya hana su,” sai suka nufi arewanci. (A. M. 16:6) Sa’ad da suka kusan kai Bitiniya, sai Yesu ya hana su. (A. M. 16:7) Ta wajen Yesu Jehobah ya ci gaba da kula da aikin wa’azi. (Mat. 28:20) Saboda haka, idan kana shawarar zuwa wata ƙasa, ka yi addu’a don Jehobah ya taimake ka.—Luk 14:28-30; Yaƙ. 1:5; ka duba akwatin nan “Yadda Za Ka San Ko Ƙasar da Za Ka Ƙaura Tana da Bukata” a shafi na 6.
12 Ka nemi shawara daga wajen dattawa da wasu ’yan’uwa Kirista da suka manyanta. (Mis. 11:14; 15:22) Ka karanta littattafan da aka buga game da yin hidima a wata ƙasa kuma ka yi bincike a kan ƙasar da kake son ka je. Za ka iya ziyarar ƙasar da kake son ka je, wataƙila na tsawon wasu kwanaki? Idan kana son ka ƙaura zuwa wata ƙasa, za ka iya rubuta wasiƙa ga ofishin reshen da ke kula da aiki a ƙasar, ta wajen yin amfani da adireshin da ke littafi nan Yearbook of Jehovah’s Witnesses na kwanan nan. Amma dai, maimakon ka aika wasiƙarka kai tsaye zuwa ofishin reshe, ka miƙa wa dattawan ikilisiyarku saboda su rubuta kalamansu kafin su aika wasiƙar.—Ka duba littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, shafuffuka na 111-112.
13. Ta yaya ofishin reshe zai taimaka maka, amma waɗanne abubuwa ne za ka ɗauki nauyinsu?
13 Ofishin reshe zai aika maka da bayanai masu amfani game da ƙasar don ka tsai da shawara, amma ba su ne za su ɗauki nauyin kula da kai ko nema maka izinin zama a ƙasar ko biza ko kuma masauƙi ba. Waɗannan batutuwa ne da kai da kanka za ka yi la’akari da su sosai kafin ka ƙaura. Ƙari ga hakan, kai ne za ka je ofishin jakadanci don neman bayani game da yadda ake samun biza da kuma izinin aiki. Ya kamata waɗanda suka ƙaura su iya kula da kansu da kuma wasu abubuwan da suke bukata.—Gal. 6:5.
14. Me ya kamata mu mai da hankali ga kafin mu ziyarci ko ƙaura zuwa wata ƙasa da aka hana aikinmu?
14 Ƙasashen da Aka Hana Aikin: Yana wa ’yan’uwa wuya su bauta wa Jehobah a wasu ƙasashe. (Mat. 10:16) Masu shela da suka ƙaura zuwa waɗannan yankunan za su iya sa a sa wa aikinmu ido kuma za su jefa ’yan’uwanmu da ke yankin cikin haɗari. Idan kana tunanin ƙaura zuwa waɗannan ƙasashen, don Allah ka rubuta wasiƙa ta hanyar dattawan ikilisiyarku zuwa ofishin reshe da ke yankinku.
15. Ta yaya waɗanda ba za su iya ƙaura zuwa wata ƙasa ba za su iya faɗaɗa hidimarsu?
15 Idan Ba Za Ka Iya Ƙaura Ba: Idan ba za ka iya ƙaura zuwa wata ƙasa ba, kada hakan ya sa ka sanyin gwiwa. Wataƙila akwai wata “ƙofa mai-faɗi mai-yalwar aiki” tana buɗe gare ka. (1 Kor. 16:8, 9) Mai kula da da’irarku zai iya sanin yankunan da suke kusa da gidanka. Wataƙila za ka iya taimaka wa wata ikilisiya ko rukunin wani yare dabam . Ko kuwa za ka iya faɗaɗa hidimarka a ikilisiyar da kake. Ko yaya yanayinka, abu mai muhimmanci shi ne ka yi hidimarka da dukan zuciya.—Kol. 3:23.
16. Yaya ya kamata mu bi da waɗanda suke son su ƙaura zuwa wata ƙasa?
16 Shin ka san wani ɗan’uwa mai ruhaniya da ya manyanta da yake son ya yi hidima a wata ƙasa? Zai dace ka tallafa masa kuma ka ƙarfafa shi! Bayan Roma da Iskandariya, Suriya na Antakiya ne birni na uku mafi girma a Daular Roma a lokacin da Bulus ya bar wurin. Da yake suna da yanki mai girma, babu shakka, ikilisiyar Antakiya suna bukatar hidimar Bulus kuma za su yi kewarsa sosai idan ya tafi. Amma duk da haka, Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa ’yan’uwan sun ƙarfafa Bulus kada ya bar wurin ba. Kamar dai, maimakon yin tunani game da yankinsu kaɗai, sun tuna cewa “gonar kuwa, ita ce duniya.”—Matta 13:38, Littafi Mai Tsarki.
17. Waɗanne dalilai muke da su na “ƙetaro zuwa Makidoniya”?
17 Bulus da abokan hidimarsa sun samu albarka sosai don amsar gayyatar ƙetarewa zuwa Makidoniya da suka yi. Yayin da suke birnin Filibi da ke Makidoniya, suka tarar da Lidiya, “Ubangiji kuwa ya buɗe zuciyarta, da za ta lura da abin da Bulus yana faɗi.” (A. M. 16:14) Ka yi tunanin farin cikin da Bulus da kuma abokan hidimarsa a ƙasar waje suka yi sa’ad da Lidiya da kuma iyalinta suka yi baftisma! A ƙasashe da yawa, akwai masu zukatan kirki kamar Lidiya da ba su ji saƙon Mulki ba tukun. Idan ka “ƙetaro zuwa Makidoniya” za ka iya shaida farin cikin samunsu da kuma taimaka musu.
[Akwati a shafi na 6]
Yadda Za Ka San Ko Ƙasar da Za Ka Ƙaura Tana da Bukata
• Ka duba Hidimarmu Ta Mulki ta Fabrairu. Ka mai da hankali ga shafin da aka rubuta rabuwar masu shela ga jimilla.
• Ka bincika talifofi da kuma labarai na wata ƙasa ta yin amfani da littafin nan Watch Tower Publication Index.
• Ka tattauna da masu shela da suka taɓa ziyartar ƙasar ko zama a wurin.
• Idan kana son ƙasar da za ka iya yin wa’azi a yarenku, ka duba wuraren bincike kamar Intane don sanin yawan mutane da suke yaren a ƙasar.