Za Ka Iya Yin Hidima a Inda Ake Bukatar Masu Shelar Mulki?
“Muna jin daɗin rayuwa a Amirka amma mun damu cewa salon rayuwa na neman abin duniya zai shafe mu da yaranmu maza biyu yadda bai kamata ba. Ni da matata mun yi wa’azi a ƙasashen waje dā kuma muna so mu more irin wannan rayuwa kuma.”
DA SON rai, a shekara ta 1991, Ralph da Pam suka rubuta wa ofisoshin reshe da yawa game da muradinsu na yin hidima a inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai. Ofishin reshe da ke Mexico suka ce da akwai bukata sosai na masu shelar Mulki da za su yi wa’azi ga mutane da suke Turanci a wannan ƙasa. Hakika, wannan yankin, in ji ofishin reshen, ya “isa girbi.” (Yoh 4:35) Ba da daɗewa ba, Ralph da Pam, tare da yaransu maza biyu masu shekaru takwas da kuma goma sha biyu, suka karɓi gayyatar kuma suka soma shirin ƙaura zuwa Mexico.
Yanki Mai Girma Sosai
Ralph ya ce: “Kafin mu bar Amirka, wasu ’yan’uwa da suke da manufa mai kyau sun gaya mana: ‘Ƙaura zuwa wata ƙasa tana da lahani!’ ‘Idan kun soma ciwo fa?’ ‘Me ya sa za ku ƙaura zuwa yankin da ake Turanci? Mutanen da suke Turanci a wurin ba za su so gaskiya ba!’ Amma mun riga mun ƙuduri aniya za mu tafi. Ballantana ma, ba mu tsai da shawarar ƙaura da motsin rai ba. Mun yi shirin ƙaura shekaru da yawa. Mun guji bashi da za mu riƙa biya da daɗewa, mun ajiye kuɗi, kuma a iyali mun tattauna sau da yawa game da wahaloli da za mu iya fuskanta.”
Da farko Ralph da iyalinsa suka ziyarci ofishin reshe na Mexico. A wajen ’yan’uwa suka nuna musu taswira na dukan ƙasar kuma suka gaya musu, “Wannan ne yankinku!” Iyalin suka zauna a San Miguel de Allende, gari inda mutane da yawa da suka fito daga wasu ƙasashe suke zaune, yana misalin nisan mil 150 ne a arewancin Birnin Mexico. Bayan shekara uku, aka kafa ikilisiya na Turanci da ke da masu shela goma sha tara a wannan garin. Wannan ne ikilisiya na Turanci na farko a Mexico, amma da ƙarin aiki.
An kimanta cewa da akwai mutanen Amirka miliyan ɗaya da ke da zama a Mexico. Ƙari ga haka, da akwai mutanen Mexico gwanaye da yawa da kuma ɗalibai da Turanci ne yarensu na biyu. Ralph ya ba da bayani: “Mun yi addu’a don ƙarin masu hidima. Koyaushe muna da wurin kwana a gidanmu don ’yan’uwa da suke zuwa yankinmu don su “yi gewayar ƙasar” wato suna son su san game da ƙasar.—L. Li 13:2.
Sun Sauƙaƙa Rayuwarsu don su Faɗaɗa Hidimarsu
Ba da daɗewa ba ƙarin ’yan’uwa da suke son su faɗaɗa hidimarsu suka isa. Bill da Kathy, ma’aurata daga Amirka suna cikinsu. Sun riga sun yi hidima shekara ashirin da biyar a yankuna da ake bukatar masu shela sosai. Suna tunanin koyan Sfanisanci, amma shirinsu ya canja bayan sun ƙaura zuwa garin Ajijic a gaɓar Tafkin Chapala, mafakar waɗanda suka yi murabus daga Amirka. Bill ya ba da bayani, “a garin Ajijic mun shagala wajen neman mutanen da suke Turanci da suke son su koyi gaskiya.” Cikin shekaru biyu da isar su birnin, Bill da Kathy sun yi farin cikin ganin an kafa wata ikilisiya, wato, ikilisiyar Turanci na biyu a ƙasar Mexico.
Ken da Joanne daga Kanada suna son su sauƙaƙa rayuwarsu kuma su ƙara ba da lokaci ga wa’azin Mulki. Su ma sun ƙaura zuwa ƙasar Mexico tare da ɗiyarsu, Britanny. Ken ya ce, “Ya ɗauke mu dogon lokaci kafin mu saba zama a inda ba za mu samu ruwa mai ɗumi ba, wutan lantarki, ko kuma daman yin waya na kwanaki.” Amma, aikin wa’azi ya sa su farin ciki. Ba da daɗewa ba aka naɗa Ken bawa mai hidima kuma bayan shekara biyu ya zama dattijo. Da farko, ya yi wa ’yarsu Britanny wuya ta kasance cikin ikilisiyar Turanci da babu matasa da yawa. Amma, bayan ta soma taimaka wajen gina Majami’un Mulki, ta yi abokai da yawa a dukan ƙasar.
Patrick da Roxanne, daga jihar Texas a ƙasar Amirka, sun yi farin cikin jin cewa da akwai yankin wa’azi a ƙasar waje da ba shi da nisa sosai inda mutane suke yin Turanci. “Bayan mun ziyarci Monterrey, wani gari a arewa maso gabas a Mexico, mun ga cewa Jehobah ne ke ja-gorarmu mu yi taimako a wajen,” in ji Patrick. Sun sayar da gidansu da ke Texas cikin kwana biyar kuma suka “ƙetaro zuwa Makidoniya,” a alamance. (A. M. 16:9) Samun kuɗi don su kula da kansu a Mexico ba shi da sauƙi, amma cikin shekara biyu, sun yi farin cikin ganin cewa ƙaramin rukuni na Shaidu 17 ya girma zuwa ikilisiya da ke da masu shela arba’in.
Jeff da Deb, ma’aurata ne da suka sauƙaƙa rayuwarsu don su faɗaɗa hidimarsu. Sun sayar da babban gidansu da ke Amirka kuma suka koma cikin ƙaramin gida a Cancún, wani birni da ke kusa da teku a gabashin Mexico. A dā, sun saba halartan manyan taro a gini mai iyakwandishan kusa da gidansu. Yanzu suna yin tafiyar awa takwas don su halarci taron Turanci mafi kusa, kuma ana taron ne a filin wasa marar rufi. Amma sun sami gamsuwa sosai cewa an kafa ikilisiyar da ke da masu shela hamsin a birnin Cancún.
Wasu ’yan’uwa ’yan Mexico su ma sun soma taimako da aikin wa’azi a Turanci. Alal misali, sa’ad da Rubén da iyalinsa suka ji cewa an kafa ikilisiya na Turanci na farko a garin San Miguel de Allende kuma dukan Mexico ce yankin ikilisiyar, nan da nan suka tsai da shawara taimakawa. Da haka suna bukatar su koyi Turanci, su koyi wata al’ada dabam, kuma su yi tafiya mai nisa, wato, mil 500 a kowane mako, don su halarci taro. Rubén ya ce: “Mun yi farin cikin yi wa baƙi da suke zama a Mexico shekaru da yawa wa’azi, wannan ne lokaci na farko da waɗannan za su ji bishara a nasu yare. Wasu cikinsu sun yi kuka don farin ciki.” Bayan sun taimaka wa ikilisiyar da ke San Miguel de Allende, Rubén da iyalinsa sun yi hidima ta majagaba a garin Guanajuato, a tsakiyar ƙasar Mexico, inda suka taimaka wajen kafa ikilisiya na Turanci da ke da masu shela fiye da talatin. A yau, suna hidima a rukuni na Turanci a Irapuato, wani gari da ke kusa da Guanajuato.
Yin Wa’azi ga Waɗanda Ganin Su Bai da Sauƙi
Ban da baƙi, da akwai mutanen Mexico da yawa da suke yin Turanci. Sau da yawa yana da wuya a yi musu wa’azin saƙon Mulki domin suna zama a wuraren da masu arziki suke zama inda ’yan aikin gida ne suke buɗe ƙofa. Ko kuma idan masu gidan suka buɗe ƙofa, ba za su so su saurari saƙonmu ba domin suna tunanin cewa Shaidun Jehobah ƙaramar ɗarika ne. Amma, sa’ad da Shaidu daga wasu ƙasashe suka yi wa irin waɗannan mutanen magana, wasu suna saurarawa.
Yi la’akari da misalin Gloria da take birnin Querétaro, a tsakiyar Mexico. Ta ba da bayani: “Shaidu masu yaren Sfanisanci sun yi mini magana dā amma ban saurare su ba. Amma, sa’ad da iyalina da abokai na suka soma samun matsala, na soma baƙin ciki kuma na yi wa Allah addu’a, ina roƙonsa ya taimake ni na samu hanyar magance matsalar. Ba da daɗewa ba, wata mata mai yin Turanci ta zo gidanmu. Ta yi tambaya ko akwai wani a gidan da yake Turanci. Domin ita baƙuwa ce, ina son na san ta, kuma na gaya mata cewa ina jin Turanci. Sa’ad da take magana, ‘Ina ta mamakin abin da ya kawo ’yar Amirka unguwarmu.’ Amma na yi addu’a ga Allah ina neman taimako. Wataƙila wannan baƙuwar ce amsar addu’ata ga Allah.” Gloria ta yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita kuma ta samu ci gaba da sauri kuma ta yi baftisma, duk da hamayya daga iyalinta. A yau, Gloria tana hidimar majagaba na kullum, kuma mijinta da ɗanta suna bauta wa Jehobah.
Lada ga Waɗanda Suka Faɗaɗa Hidimarsu
Gaskiya ne cewa akwai ƙalubale tattare da yin hidima inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai, amma albarkar tana da yawa. Ralph da aka ambata a somawar wannan talifin ya ce: “Mun gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane daga Britaniya, Sin, Jamaica, Sweden, da kuma manyan mutane daga ƙasar Gana. Wasu cikin waɗannan ɗaliban na Littafi Mai Tsarki sun shiga hidima na cikakken lokaci da kansu. Cikin shekaru da suka shige, iyalinmu ta ga ikilisiyoyin Turanci guda bakwai da aka kafa. ’Ya’yanmu maza sun soma majagaba tare da mu, kuma a yanzu suna hidima a Bethel a Amirka.”
A yanzu, da akwai ikilisiyoyin Turanci tamanin da takwas da kuma rukunoni masu yawa a Mexico. Menene ya sa aka samu irin wannan ƙaruwan? Mutane da yawa masu Turanci a Mexico ba su taɓa magana da Shaidu ba. Wasu sun saurara domin ba mai tsananta musu kamar yadda ake yi a ƙasarsu. Har ila wasu sun yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su domin sun yi murabus kuma suna da lokacin biɗar abubuwa na ruhaniya. Ƙari ga haka, fiye da kashi uku na masu shela a ikilisiyoyin Turanci suna hidima na majagaba, hakan ya sa aka ƙara himma da kuma ƙaruwa a waɗannan ikilisiyoyin.
Albarka na Jiranka
Babu shakka, ƙarin mutane daga dukan duniya za su saurari saƙon Mulki da aka gaya musu a nasu yaren. Saboda haka, yana da ban ƙarfafa a ga cewa ’yan’uwa da yawa masu ruhaniya, ƙanana da manya, marasa aure da waɗanda suka yi aure suna shirye su ƙaura zuwa wuraren da ake bukatar masu shelar Mulki sosai. Hakika, suna iya jimre da wahala, amma wannan ba komi ba ne idan aka gwada da farin ciki da suke yi sa’ad da suka samu mutane masu zuciyar kirki da suka karɓi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Kana iya yin canje-canje da za su taimake ka ka ƙaura zuwa wani yanki a ƙasarku ko kuma wata ƙasa inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai?a (Luk 14:28-30; 1 Kor. 16:9) Idan kana shirye ka yi haka, ka tabbata cewa za ka sami albarka da yawa.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da hidima a inda ake da bukata sosai, ka duba littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, shafuffuka na 111-112.
[Akwati da ke shafi na 21]
Masu Farin Ciki da Suka Yi Murabus Sun Jawo hankalin Mutane
Beryl ta ƙaura daga Britaniya zuwa Kanada. A wajen, ta yi aiki a matsayin manaja a kamfanonin ƙasashen waje dabam-dabam. Ta zama gwani a hawan doki kuma aka zaɓe ta ta wakilci Kanada a wasan Olimfik a shekara ta 1980. Bayan da ta yi murabus, kuma ta koma Chapala, a Mexico da zama, Beryl da mijinta sau da yawa suna cin abinci a gidan abinci. Sa’ad da ta ga waɗanda suka yi murabus da suka iya Turanci kuma suna farin ciki, ta gabatar da kanta kuma ta tambaye su abin da suke yi a Mexico. Waɗannan masu farin ciki kusan koyaushe Shaidun Jehobah ne. Beryl da mijinta suka yi tunani cewa idan ana samun farin ciki da ma’ana a rayuwa ta wajen sanin Allah, su ma suna son su san shi. Bayan sun halarci taro watanni da yawa, Beryl ta yarda ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta zama Mashaidiya. Beryl ta yi shekaru da yawa tana hidima na majagaba na kullum.
[Akwati da ke shafi na 22]
“Albarka Ce Su Kasance Tare da Mu”
’Yan’uwa da suke yankin da ake bukatar masu shelar Mulki suna godiya sosai ga waɗanda suka ƙaura zuwa ƙasashen don su taimaka. Wani ofishin reshe a Caribbean ya rubuta: “Idan masu wa’azi a ƙasashen waje da ke nan suka tafi, ikilisiyoyin ba za su kasance da ƙarfi ba kuma. Albarka ce su kasance tare da mu.”
Kalmar Allah ta ce “mata masu-shelar bishara babbar runduna ne.” (Zab. 68:11) Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa da akwai ’yan’uwa mata da yawa da ba su yi aure ba da suke hidima a ƙasar waje. Irin waɗannan ’yan’uwa mata masu sadaukar da kansu suna taimakawa sosai. Wani ofishin reshe a Gabashin Turai ya ce: “A ikilisiyoyinmu masu yawa, ’yan’uwa mata sun fi yawa, wani lokaci wajen kashi saba’in na masu shela a ikilisiyar mata ne. Yawancinsu sababbi ne cikin gaskiya, amma ’yan’uwa mata majagaba da ba su yi aure ba da suka zo daga wasu ƙasashe suna ba da taimako sosai ta wajen koyar da sababbin. Muna ɗaukan waɗannan mata daga wasu ƙasashe da tamani sosai!”
Yaya irin waɗannan ’yan’uwa mata suke ji game da yin hidima a wasu ƙasashe? “Ƙalubalen suna da yawa,” in ji Angelica, wata ’yar’uwa mai shekaru wajen talatin da biyar, wadda ta yi hidimar majagaba na shekaru da yawa a ƙasar waje a matsayin wadda ba ta yi aure ba. “A wani waje da nake hidima, kullum ina fama da tafiya cikin hanyoyi masu taɓo kuma na ga mutane da yawa da suke shan wahala, kuma hakan na sa ni baƙin ciki. Amma na samu gamsuwa wajen taimaka wa mutane a hidima. Ina farin ciki da kalamai na godiya daga ’yan’uwa mata da ke yankin da sau da yawa suna gode mini don zuwa na taimake su. Wata ’yar’uwa ta gaya mini cewa misalina na zuwa ƙasarsu daga wuri mai nisa don na yi hidimar majagaba ya motsa ta ta soma hidimar majagaba.”
Sue, wadda majagaba ce mai shekaru hamsin da wani abu, ta ce: “Babu shakka za ka fuskanci matsaloli, amma ba za a gwada wannan da albarkar da za ka samu ba. Hidima na kawo farin ciki! Tun da yake ina daɗewa a hidima da ’yan’uwa mata matasa, ina gaya musu abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu a kan yadda za a bi da matsaloli. Sau da yawa suna gaya mini cewa misalina wajen bi da matsaloli sa’ad da nake hidima shekaru da yawa a matsayin majagaba da ba ta yi aure ba na taimakonsu su ga cewa su ma suna iya sha kan ƙalubale a rayuwarsu. Taimaka wa waɗannan ’yan’uwa mata na sa na samu gamsuwa ta ƙwarai.”
[Taswira da ke shafi na 23]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
MEXICO
Guanajuato
Irapuato
Chapala
Ajijic
Tafkin Chapala
Monterrey
San Miguel de Allende
Querétaro
BIRNIN MEXICO
Cancún
[Hotunan da ke shafi na 23]
Wasu suna farin cikin yin wa’azi ga baƙi da suka ji bishara a lokaci na farko