Sun Ba da Kansu da Yardar Rai—A Ƙasar Meziko
ADADIN matasa Kiristoci da ke sauƙaƙa salon rayuwarsu don su ƙara ƙwazo a hidimarsu yana ƙaruwa, kuma hakan yana da ban ƙarfafa sosai. (Mat. 6:22) Waɗanne canje-canje ne suke yi? Waɗanne ƙalubale ne suke fuskanta? Bari mu ɗan ji daga bakin waɗanda suke hidima a ƙasar Meziko.
“MUNA BUKATAR YIN CANJE-CANJE”
Dustin da matarsa Jassa ’yan Amirka ne da suka yi aure a watan Janairu na 2007. Ba da daɗewa ba bayan auren, sai suka sayi kwalekwale da suke kasuwanci da shi. Sun ajiye kwalekwalensu a wani kogi da ke birnin Astoria a jihar Oregon da ke Amirka, kusa da Tekun Fasifik. Birni ne mai ban sha’awa da ke da tuddai wanda ƙanƙara ta yi musu hula. Dustin ya ce, “mahallin garin yana da kyau sosai.” Ma’auratan suna ganin cewa sun riga sun sauƙaƙa salon rayuwarsu kuma suna dogara ga Jehobah. Sun ce: “Mukan yi aiki na ɗan lokaci da kwalekwalenmu mai tsawon kafa 26, muna halartar taro a ikilisiyar da ake wani yare dabam kuma mukan yi hidimar majagaba na ɗan lokaci sa’i-sa’i.” Amma daga baya, sun kammala cewa suna ruɗin kansu ne kawai. Dustin ya ce: “Gyaran kwalekwalenmu yana cin lokacinmu fiye da saka hannu a ayyukan ikilisiya. Mun san cewa wajibi ne mu canja salon rayuwarmu idan muna son bauta wa Jehobah ya zama kan gaba a rayuwarmu.”
Jassa ta daɗa cewa: “Kafin mu yi aure, ina zama a ƙasar Meziko kuma ina halartar taro a ikilisiyar da ake Turanci. Na so in sake komawa domin na ji daɗin hidima a wurin sosai.” Da yake suna son su yi hidima a wata ƙasa, sai Dustin da matarsa Jassa suka soma karanta labaran ’yan’uwa a bautarsu ta iyali da suka ƙaura zuwa wasu ƙasashe inda mutane suke son saƙon. (Yoh. 4:35) Dustin ya ce: “Muna son mu yi farin ciki kamar waɗannan ’yan’uwan.” Sa’ad da Dustin da matarsa Jassa suka ji cewa ana bukatar taimako a wani sabon rukuni da ke Meziko, sai suka tsai da shawarar ƙaura zuwa wajen. Sun daina aikinsu, sun sayar da kwalekwalensu, sai suka ƙaura.
“ZAƁI MAFI KYAU DA MUKA TAƁA YI”
Dustin da matarsa Jassa sun sauka a garin Tecomán da ke kusa da Tekun Fasifik, amma yana da nisan mil 2,700 daga kudancin birnin Astoria. Dustin ya ce: “Yanzu inda muke akwai zafi sosai, kuma abin da muke gani kawai shi ne itatuwan lemun tsami.” Da farko, ba su samu aiki a garin ba. Hakan ya sa su riƙa cin shinkafa da wake dare da rana har tsawon makonni, da yake abincin da ya fi araha ke nan a ƙasar. Jassa ta ce: “Sa’ad da muka soma gajiya da cin abinci iri ɗaya, sai ɗalibanmu suka soma ba mu mangwaro da ayaba da gwanda da kuma lemun tsami sur a farin leda.” Daga baya, sai ma’auratan suka soma aiki da wata makaranta da ke ƙasar Taiwan ta Intane. Kuɗin da suke samu daga wannan aikin yana biyan bukatunsu sosai.
Yaya Dustin da Jassa suke ji game da salon rayuwarsu yanzu? Sun ce: “Wannan shi ne zaɓi mafi kyau da muka taɓa yi. Dangantakarmu da Jehobah ta daɗa yin danƙo, kuma mun fi kusantar juna a matsayin ma’aurata yanzu. Kowace rana, muna yin abubuwa da yawa tare, kamar zuwa wa’azi da tattauna yadda za mu taimaka wa ɗalibanmu da kuma shirin taro. Ƙari ga haka, mun shawo kan matsaloli da muke fuskanta a dā.” Sun daɗa cewa: “Yanzu mun fi amincewa da abin da ke cikin Zabura 34:8 da ta ce, ‘Ku ɗanɗana, ku duba, Ubangiji nagari ne.’”
ME YA MOTSA MUTANE DA YAWA SU BA DA KANSU?
’Yan’uwa maza da mata fiye da 2,900 sun ƙaura zuwa ƙasar Meziko don su yi hidima a yankunan da ake bukatar masu wa’azi. Wasunsu ma’aurata ne, wasu kuma ba su yi aure ba. Da yawa a cikinsu ’yan shekara 20 zuwa 39 ne. Me ya sa waɗannan ’yan’uwan suka soma irin wannan aikin? Sa’ad da aka yi wa wasu wannan tambayar, sai suka ba da dalilai uku. Ka san dalilan?
Don suna ƙaunar Jehobah da kuma mutane. Leticia da ta yi baftisma tun tana ’yar shekara 18 ta ce: “Sa’ad da na keɓe kaina ga Jehobah, na fahimci cewa hakan yana nufin zan bauta masa da dukan zuciyata da kuma raina. Na so in daɗa ba da lokaci da kuma nuna ƙwazo a hidimarsa domin in nuna masa cewa ina ƙaunarsa da dukan raina.” (Mar. 12:30) Hermilo mijin Leticia, ya ƙaura zuwa inda ake bukatar masu wa’azi sosai sa’ad da yake matashi. Ya ce: “Na gane cewa hanya mafi kyau da zan ƙaunaci maƙwabtana ita ce ta wajen taimaka musu su zama abokan Allah.” (Mar. 12:31) Sai ya ƙaura daga birnin Monterrey, inda yake aiki a banki da kuma rayuwar jin daɗi, zuwa wani ƙaramin gari.
Don suna son su yi farin ciki dindindin. Jim kaɗan bayan Leticia ta yi baftisma, sai ta bi wata majagaba zuwa wani gari kuma suka yi wa’azi har wata ɗaya a wurin. Leticia ta ce: “Na yi mamaki ƙwarai, kuma yadda mutanen suka saurari saƙonmu ya sa ni farin ciki sosai. A ƙarshen wannan watan, sai na ce wa kaina, ‘Abin da nake son in yi da rayuwata ke nan!’” Wata ’yar’uwa matashiya mai suna Essly, ta soma wannan hidimar domin ta ga cewa waɗanda suke hidimar suna farin ciki. Sa’ad da take makarantar sakandare, ta haɗu da Shaidu da suke hidima a inda ake bukatar masu wa’azi sosai. Ta ce: “Yadda suke farin ciki ya sa na so in yi irin rayuwarsu.”’Yan’uwa mata da yawa sun bi gurbin Essly. A ƙasar Meziko, ’yan’uwa mata da ba su yi aure ba da suke hidima a inda ake bukatar masu wa’azi sosai sun fi 680. Hakika, sun kafa misali mai kyau ga manya da kuma ƙanana.
Don suna son rayuwarsu ta kasance da ma’ana. Da Essly ta kammala makarantar sakandare, sai ta samu sukolashif na zuwa jami’a. Tsararta sun ƙarfafa ta cewa ta je makarantar don ta samu digiri, ta soma aiki, ta sayi mota kuma ta yi tafiye-tafiye tana shaƙatawa. Duk da haka ba ta bi shawararsu ba. Essly ta ce: “Na san wasu abokaina Kiristoci da suka biɗi waɗannan abubuwa, kuma na lura cewa sun daina mai da hankali ga ayyukan da suka shafi bautarmu. Na kuma ga cewa suna daɗa fuskantar matsaloli sa’ad da suke cusa kansu cikin ayyukan wannan duniyar. Na so in bauta wa Jehobah tun ina ƙuruciya.”
Essly ta daɗa koyan wasu abubuwa don ta samu aikin da ba zai hana ta yin hidimar majagaba ba. Bayan haka, ta ƙaura zuwa wani yanki da ake bukatar masu shela ruwa a jallo. Kuma ta soma koyon yaren mutanen Otomi da kuma Tlapaneco, ko da yake yin hakan ba cin tuwo ba ne. Yanzu da ta yi wannan hidimar na shekara uku, ta ce: “Yin hidima a inda ake bukatar masu shela sosai ya sa rayuwata ta kasance da ma’ana sosai. Mafi muhimmanci ma, ya ƙarfafa dangantaka ta da Jehobah.” Phillip da Racquel, ma’aurata ne daga ƙasar Amirka da suka ɗan ba shekara 30 baya, kuma sun yarda da furucin Essly. Sun ce: “Mutane suna jin cewa rayukansu na cikin haɗari don yanayin duniya yana canjawa. Amma, yin hidima a inda mutane suke saurarar saƙon Littafi Mai Tsarki yana tabbatar mana cewa rayuwarmu tana da ma’ana. Muna samun gamsuwa sosai!”
YADDA ZA KA BI DA ƘALUBALE
Babu shakka, yin hidima a inda ake bukatar masu shela sosai yana da nasa matsaloli. Wata matsalar ita ce yadda za ka samu kuɗin biyan bukatunka. Don ka shawo kan wannan matsalar, kana bukatar ka kasance da shirin sauya salon rayuwarka bisa ga yanayin yankin. Verónica, wata majagaba da ta ƙware sosai ta ce: “A wani yankin da na taɓa yin hidima, ina dafa abinci kuma in sayar. A wani yankin kuma, na sayar da riguna kuma ina wa mutane aski. A yanzu, ina shara a wani gida kuma ina koya wa wasu sababbin iyaye yadda za su yi renon yaransu.”
Ba shi da sauƙi mutum ya saba da al’adu da kuma salon rayuwar mutanen wani yankin dabam. Abin da ya faru da Phillip da Racquel ke nan sa’ad da suke hidima a yankin da ake yaren Nahuatl. Phillip ya ce: “Al’adarmu ta bambanta sosai da tasu. Amma, abin da ya taimaka mana shi ne mun fi mai da hankali ga al’adunsu masu kyau, kamar yadda iyalai suke kusantar juna sosai da kuma yadda suke faɗin gaskiya da kuma halinsu na karimci.” Racquel ta daɗa cewa: “Mun koyi abubuwa da yawa daga yankin da kuma ’yan’uwa da muke hidima tare.”
TA YAYA ZA KA SHIRYA KANKA?
Idan kana son ka yi hidima a yankunan da ake bukatar masu wa’azi, wane shiri ne za ka yi? ’Yan’uwa da suka taɓa yin wannan hidimar sun ce, kafin ka ƙaura, ka soma sauƙaƙa salon rayuwarka kuma ka kasance da wadar zuci. (Filib. 4:11, 12) Mene ne kuma ya kamata ka yi? Leticia ta ce: “Na ƙi yin duk aikin da zai bukaci mutum ya kasance a wuri ɗaya na dogon lokaci. Ina son in kasance a shirye don ƙaura a kowane lokaci zuwa duk inda ake da bukata.” Hermilo ya ce: “Na koyi yadda ake dahuwa da wanki da kuma guga.” Verónica kuma ta ce: “Sa’ad da nake gida tare da iyayena da kuma ’yan’uwana, ina yin shara. Na koyi dafa abinci mai gina jiki da ɗan kuɗi, kuma na koyi yin ajiyar kuɗi.”
Levi da Amelia ma’aurata ne shekara takwas yanzu, su ’yan Amirka ne kuma sun faɗi yadda yin addu’a ta taimaka musu su yi shirin yin hidima a Meziko. Levi ya ce: “Mun lissafa yawan kuɗin da muke bukata don mu yi hidima na shekara guda a wata ƙasa, sai muka roƙi Jehobah ya sa mu samu kuɗin.” Jehobah ya amsa addu’arsu a cikin ’yan watanni, kuma suka ƙaura nan da nan. Levi ya kuma ce: “Jehobah ya amsa addu’armu, yanzu ya rage mu cika alkawarinmu.” Amelia ta daɗa, cewa: “Mun ɗauka shekara ɗaya tak za mu yi a nan, amma yanzu mun kai shekara bakwai, kuma ba ma tsammanin za mu koma! Kasancewa a nan yana ba mu tabbaci cewa Jehobah yana taimaka mana. Muna ganin tabbacin alherinsa a kowace rana.”
Adam da Jennifer ma’aurata ne daga Amirka, kuma addu’a ce ta taimaka musu su soma hidima a Meziko. Ga shawarar da suka bayar: “Kada ka jira har sai kome ya yi daidai. Ka riƙa yin addu’a game da maƙasudinka na yin hidima a wata ƙasa, kuma ka aikata bisa ga addu’arka. Ka sauƙaƙa salon rayuwarka, kuma ka rubuta wasiƙa ga ofishin reshe da ke ƙasar da za ka so ka yi hidima. Bayan ka kammala shiri, sai ka ɗauki mataki.”a Idan ka yi hakan, za ka more dangantaka mai kyau da Jehobah, kuma za ka yi farin ciki sosai.
a Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan, “Za Ka Iya ‘Ƙetaro Zuwa Makidoniya’?” da ke cikin Hidimarmu Ta Mulki ta Nuwamba 2011.