Sun Ba Da Kansu Da Yardar Rai—A Ƙasar Filifin
WAJEN shekaru goma da suka shige, wasu ma’aurata da suka ba shekara talatin baya masu suna Gregorio da Marilou, suna hidimar majagaba a birnin Manila kuma suna aiki na cikakken lokaci. Ko da yake hakan bai kasance musu da sauƙi ba, amma sun yi nasara. Ana nan, sai aka ƙara wa Marilou matsayi a bankin da take aiki. Ta ce: “Ayyukan da muke yi sun sa muna jin daɗin rayuwa.” Suna samun kuɗi a kai a kai har suka yanke shawarar gina gida mai kyau a wani yanki a gabashin birnin Manila mai nisan mil 12 daga birnin. Sun ba wani kamfani kwangilar gina gidan kuma suka shirya su riƙa biyan kuɗin kaɗan-kaɗan har shekara goma.
“NA JI KAMAR INA YI WA JEHOBAH ZAMBA”
Marilou ta ce: “Ba na samun lokaci da kuma ƙarfin yin wasu abubuwa saboda ƙarin matsayi da aka ba ni a wurin aiki, kuma hakan ya sa na daina sha’awar ayyukan da suka shafi ibadata. Sai na ji kamar ina yi wa Jehobah zamba.” Ta daɗa cewa: “Ba na iya cika alkawarina ga Jehobah game da hidimarsa.” Gregorio da Marilou ba su ji daɗin yanayinsu ba, sai wata rana suka zauna don su tattauna yadda suke gudanar da rayuwarsu. Gregorio ya ce: Muna so mu yi canji amma ba mu san ainihin abin da ya kamata mu yi ba. Da yake ba mu da yara, mun tattauna yadda za mu ƙara ba da lokacinmu don yin hidimar Jehobah. Muka yi addu’a ga Jehobah don ya yi mana ja-gora.”
A wannan lokacin, sun saurari jawabai da yawa game da zuwa yin wa’azi a inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai. Gregorio ya ce: “Kamar dai Jehobah yana amsa addu’o’inmu ta waɗannan jawaban ne.” Ma’auratan suka roƙi Jehobah ya ba su gaba gaɗin yin shawarar da ta dace. Wani babban tangarɗa da suka samu ita ce yadda za su bi da kwangilar gini da suka ba da. Sun riga sun yi shekara uku suna biya. Shin mene ne za su yi? Marilou ta ce: “Idan muka saɓa yarjejeniyar, kuɗaɗe masu yawa da muka biya za su bi ruwa. Amma mun ga cewa muna da zaɓi biyu, ko mu saka nufin Jehobah farko a rayuwa ko kuma namu.” Sanin abin da manzo Bulus ya ce game da “hasara,” ya sa suka daina ginin kuma suka yi murabus da aikinsu, suka sayar da wasu kayayyakinsu, sai suka ƙaura zuwa karkarar da ke tsibirin Palawan mai nisan mil 300 daga birnin Manila.—Filib. 3:8.
SUN FAHIMCI SIRRIN
Gregorio da Marilou sun yi ƙoƙarin sauƙaƙa salon rayuwarsu kafin su ƙaura, amma ba su gama fahimtar ainihin yadda rayuwarsu za ta kasance ba sai lokacin da suka ƙaura zuwa karkarar. Marilou ta ce: “Abin ya firgitar da ni domin babu wutar lantarki da kuma abubuwan jin daɗin rayuwa a wurin. A maimakon mu kunna rashon lantarki, sai mu faskare itace kuma mu yi girki a murhu. Babu zuwa manyan shaguna ko manyan gidajen cin abinci ko kuma yin wasu abubuwan shaƙatawa da ake yi a birni.” Duk da haka, waɗannan ma’auratan ba su manta da dalilin da ya sa suka ƙaura zuwa karkarar ba, kuma ba da daɗewa ba suka saba da wurin. Marilou ta ce: “Yanzu ina jin daɗin kallon abubuwan da Allah ya halitta, har da taurari masu haske daddare. Kuma abin sha’awa ne ganin yadda mutane suke farin ciki sa’ad da muke yi musu wa’azi. Mun koyi sirrin kasancewa da wadar zuci.”—Filib. 4:12.
“Babu abin da ke kawo farin ciki kamar ganin yadda sababbi suke samun ci gaba a cikin ikilisiyar. Yanzu rayuwarmu tana da ma’ana fiye da dā.”—Gregorio da Marilou
Gregorio ya ce: “Sa’ad da muka zo nan, Shaidun Jehobah guda huɗu ne kawai a garin. Sun yi farin ciki sa’ad da na soma ba da jawabi kowane mako kuma nake kaɗa jita sa’ad da muke waƙoƙin Mulki a taro.” A shekara ɗaya kawai, ma’auratan sun shaida yadda ƙaramin rukunin nan ya zama ikilisiya mai masu shela ashirin da huɗu. Gregorio ya ci gaba da cewa: “Irin ƙaunar da ’yan’uwa da ke ikilisiyar suka nuna mana ta ratsa zuciyarmu sosai.” Sun yi shekara shida suna hidima a wannan yankin, sun kammala da cewa: “Babu abin da ke kawo farin ciki kamar ganin yadda sababbi suke samun ci gaba a cikin ikilisiyar. Yanzu rayuwarmu tana da ma’ana fiye da dā.”
NA ‘ƊANƊANA, NA DUBA, CEWA JEHOBAH NAGARI NE’!
’Yan’uwa kusan 3,000 a ƙasar Filifin sun ƙaura zuwa inda ake da bukatar masu shelar Mulki sosai. Akwai mata guda ɗari biyar a cikinsu da ba su yi aure ba. Ɗaya cikinsu ita ce Karen.
Karen ’yar shekara 25 ce, kuma ta girma a birnin Baggao, Cagayan. Sa’ad da take matashiya, ta yi tunanin yadda za ta iya faɗaɗa hidimarta. Ta ce: “Sanin cewa babu sauran lokaci sosai kuma dukan mutane suna bukatar su ji saƙon Mulki, ya sa ni marmarin yin hidima a inda ake bukatar ƙarin masu wa’azi.” Ko da yake wasu danginta sun shawarce ta ta je makarantar sama da sakandare maimakon zuwa karkara wa’azi, Karen ta yi addu’a ga Jehobah don ya ja-gorance ta. Ta kuma nemi shawara daga wajen waɗanda suke hidima a inda ake da bukata. Sa’ad da take ’yar shekara 18, ta ƙaura zuwa wata karkara da ke da nisan mil 40 daga gidansu.
Karen tana hidima a wata ƙaramar ikilisiya a wani yanki da ke da tuddai kusa da gaɓar tekun Fasifik. Karen ta ce: “Kafin mu isa sabuwar ikilisiyar daga Baggao, muna tafiya da ƙafa na tsawon kwana uku, muna hawa da saukowa daga kan duwatsu kuma muna haye koguna fiye da talatin.” Ta daɗa cewa: “Ina tafiyar awa shida da ƙafa zuwa gidan wasu ɗalibaina kuma in kwana a wurin, washegari kuma sai na sake tafiyar awa shida da ƙafa zuwa gida.” Shin ta amfana kuwa? Cike da murmushi ta ce: “A wasu lokatai ƙafafuna suna mini zafi, amma, na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibai goma sha takwas. Hakika, na ‘ɗanɗana, na duba, cewa Jehobah nagari ne’!”—Zab. 34:8.
“NA KOYI YADDA AKE DOGARA GA JEHOBAH”
Mene ne ya motsa wata ’yar’uwa mai suna Sukhi da ta ba shekara 40 baya da ke zama a ƙasar Amirka ta ƙaura zuwa ƙasar Filifin? Ta halarci wani taron da’ira ne a shekara ta 2011, kuma a taron an gana da wasu ma’aurata. Sun ba da labarin yadda suka sayar da kayayyakinsu kuma suka ƙaura zuwa ƙasar Meziko don su taimaka da yin wa’azi a wurin. Ta ce: “Wannan ganawar ta sa na soma tunani a kan wasu maƙasudan da ban taɓa tunaninsu ba a dā.” Sukhi ’yar ƙasar Indiya ce, kuma sa’ad da ta ji cewa ana bukatar ƙarin masu shela da za su yi wa masu yaren Punjabi da ke zama a ƙasar Filifin wa’azi, sai ta yanke shawarar zuwa yin hidima a wurin. Shin ta fuskanci ƙalubale kuwa?
Sukhi ta ce: “Yanke shawarar kayayyakin da zan ajiye da kuma waɗanda zan sayar bai kasance mini da sauƙi ba. Kuma bayan na zauna a gidana na tsawon shekara 13, yanzu ina zama na ɗan lokaci da wani dangina kuma ba na rayuwar jin daɗi kamar dā. Ko da yake hakan ba sauƙi, amma hanya ce mai kyau da ke taimaka mini in sauƙaƙa salon rayuwata.” Waɗanne ƙalubale ne ta fuskanta sa’ad da ta ƙaura zuwa ƙasar Filifin? Ta ce: “Tsoron ƙwari da kuma kewar ’yan’uwana da na baro a gida ne babban ƙalubale da na fuskanta. Na koyi yadda ake dogara ga Jehobah fiye da dā.” Shin ta amfana kuwa? Ta yi murmushi ta ce: “Jehobah yana cewa, ‘Ku gwada ni haka nan yanzu, ko ba zan zuba muku albarka ba.’ Na ga gaskiyar waɗannan kalmomin sa’ad da wata da na yi wa wa’azi ta tambaye ni, ‘Yaushe za ki dawo? Ina da tambayoyi da yawa.’ Ina farin ciki da kuma gamsuwa sosai ganin cewa ina iya taimaka wa mutanen da suke so su koya game da Jehobah!” (Mal. 3:10) Sukhi ta daɗa cewa: “Hakika, yanke shawarar ƙaura ne ya fi wuya. Amma bayan na yi hakan, na yi mamakin ganin yadda Jehobah ya taimake ni sosai.”
“NA DAINA FARGABA”
Wani ɗan’uwa da ya yi aure mai suna Sime da ya kusan shekara arba’in, ya bar ƙasar Filifin don ya soma aiki mai armashi a wata ƙasa a Gabas ta Tsakiya. Sa’ad da yake wurin, wani mai kula da da’ira ya ƙarfafa shi, kuma ya saurari jawabin da wani ɗan’uwa da ke cikin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya ba da, kuma hakan sun sa ya saka bautar Jehobah kan gaba a rayuwarsa. Sime ya ce: “Yin tunani a kan barin aikin na ya dame ni sosai.” Duk da hakan, ya yi murabus da aikinsa kuma ya koma ƙasar Filifin. Yanzu, Sime da matarsa Haidee suna hidima a tsibirin Davao del Sur da ke kudancin ƙasar inda ake bukatar masu shelar Mulki don a faɗaɗa yankin. Sime ya ce: “Ina hamdala sosai cewa na daina fargabar barin aikina kuma na saka bautar Jehobah a kan gaba fiye da dā. Abin da ya fi armashi a rayuwa shi ne bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu!”
“HAKAN YA GAMSAR DA MU SOSAI”
Wasu ma’aurata majagaba da suka ba shekara talatin baya masu suna Ramilo da Juliet, sun sami labari cewa akwai wata ikilisiya da ke da nisan mil 20 daga gidansu da ke bukatar taimako, sai suka yarda cewa za su taimaka. A kowane mako kuma a kowane yanayi, Ramilo da Juliet suna tafiya da babur ɗinsu don su halarci taro kuma su fita yin wa’azi. Ko da yake sun fuskanci ƙalubalen tafiya a hanyoyin da ba su da kyau da kuma gadan katako, suna farin ciki cewa sun faɗaɗa hidimarsu. Ramilo ya ce: “Ni da matata muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 11! Ana bukatar sadaukarwa don yin hidima a inda ake da bukata kuma muna farin ciki sosai don mun yi hakan!”—1 Kor. 15:58.
Shin kana so ka sami ƙarin bayani game da yin hidima a inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai a ƙasarku ko kuma a ƙasar waje? Idan amsarka e ce, ka gaya wa mai kula da da’irarku, kuma ka karanta wannan talifin “Za Ka Iya ‘Ƙetaro Zuwa Makidoniya’?” da ke Hidimarmu ta Mulki ta Nuwamba 2011.