TARIHI
“Na Zama Dukan Abu ga Dukan Mutane”
A shekara ta 1941, mahaifina ya gaya wa mahaifiyata cewa: “Idan kika yi baftisma, zan sake ki!” Mahaifiyata ta yanke shawarar yin baftisma duk da barazanar da mahaifina ya yi. Don haka, sai mahaifina ya sake ta kuma a lokacin ina ɗan shekara takwas.
KAFIN mahaifina ya bar mu, ina son in san gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Mahaifiyata ta karɓi wasu littattafan Shaidun Jehobah, kuma ina son abin da ke cikinsu musamman hotunan. Mahaifina ba ya son mahaifiyata ta koya min abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Amma ina son na koyi wasu abubuwa kuma nakan yi tambayoyi, don haka, takan yi nazari da ni idan mahaifina ba ya gida. Saboda haka, ni ma na yanke shawarar bauta wa Jehobah. Na yi baftisma lokacin da nake shekara goma a shekara ta 1943 a garin Blackpool, da ke ƙasar Ingila.
YADDA NA SOMA BAUTA WA JEHOBAH
Tun daga wannan lokacin, ni da mahaifiyata muna wa’azi a kai a kai. Muna amfani da garmaho don mu gabatar da saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Garmahon yana da girma da kuma nauyi sosai. Da yake ni ƙaramin yaro ne, ɗaukansa ya yin mini wuya!
Ina son in soma hidimar majagaba sa’ad da na kai shekara 14, amma mahaifiyata ta ce na je na gaya wa mai kula da da’irarmu. Da na gaya masa, sai ya ce in je in koyi wata sana’ar da za ta taimaka min in kula da kaina sa’ad da nake hidimar majagaba. Na yi abin da ya faɗa kuma bayan na yi aiki na shekara biyu, sai na je na gaya ma wani mai kula da da’ira cewa ina so in soma hidimar majagaba, sai ya ce min, “Ka soma kawai!”
Saboda haka, a watan Afrilu na shekara ta 1949 ni da mahaifiyata muka sayar da kayan gidanmu kuma muka ƙaura zuwa garin Middleton da ke kusa da Manchester. A nan ne muka soma hidima kuma bayan watanni huɗu, sai na zaɓi wani ɗan’uwa wanda zan riƙa hidimar tare da shi. Ƙari ga haka, ofishin da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah da ke ƙasarmu ya tura mu zuwa wata ikilisiya da aka kafa ba da daɗewa ba a garin Irlam. Mahaifiyata kuma ta zaɓi wata ‘yar’uwa don su yi hidima tare a wata ikilisiya.
Ko da yake ni ɗan shekara 17 ne kawai a lokacin, an gaya mini da ɗan’uwan da muke wa’azi tare cewa mu riƙa gudanar da taro da yake babu ‘yan’uwa maza da suka manyanta a ikilisiyar da muka koma. Bayan hakan, aka tura ni ikilisiyar da ke garin Buxton, don ba su da masu shela sosai, saboda suna bukatar taimako. Abubuwan da na shaida a waɗannan shekarun sun horar da ni don in ƙware a hidimomin da zan yi a nan gaba.
Ni da wasu muna sanar da jigon jawabin da za a yi a birnin Rochester, New York, 1953
A shekara ta 1951, na cika fom na zuwa Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead. Amma an tilasta mini in soma aikin soja a watan Disamba na shekara ta 1952. Na nemi a cire sunana domin ina hidima ta cikakken lokaci, amma kotu ba ta amince da hakan ba kuma ta yanke min hukuncin yin wata shida a fursuna. Da nake fursuna ne aka gayyace ni zuwa aji na 22 na Makarantar Gilead. Don haka, a watan Yuli na shekara ta 1953, na kama hanya zuwa jihar New York da jirgin ruwa da ake kira Georgic.
Da na isa, sai na halarci taron New World Society Assembly da aka yi a shekara ta 1953. Sai na yi tafiya da jirgin ƙasa zuwa birnin South Lansing da ke jihar New York wurin da makarantar take. Ba ni da kuɗi da yake bai daɗe ba da na fito daga fursuna. Don haka, da na sauka daga jirgin, sai na shiga mota zuwa birnin South Lansing, kuma na ari kuɗi daga wurin wani fasinja don na biya kuɗin mota.
YIN HIDIMA A WATA ƘASA
An horar da mu sosai a Makarantar Gilead don mu “zama dukan abu ga dukan mutane,” sa’ad da muke hidima a wata ƙasa. (1 Kor. 9:22) An tura ni da Paul Bruun da kuma Raymond Leach zuwa ƙasar Filifin. Mun yi watanni da yawa kafin mu samu biza, bayan da muka samu, sai muka kama hanya da jirgin ƙasa kuma muka bi ta birnin Rotterdam da Bahar Rum da kogin Suez da Tekun Indiya da Malaysia da kuma Hong Kong. Mun yi kwanaki 47 muna tafiya a cikin teku sai muka isa birnin Manila a ranar 19 ga Nuwamba a shekara ta 1954.
Ni da ɗan’uwa Raymond Leach da muka yi tafiya kwanaki 47 ta jirgin ruwa zuwa Filifin
A wajen wajibi ne mu yi rayuwa da ta jitu da al’adar mutanen, da ƙasarsu da kuma yarensu. Amma, da farko an tura mu ukun zuwa ikilisiyar da ke Quezon City don mutane da yawa da ke wurin suna Turanci. Bayan mun yi wata shida a wurin, mun koyi wasu kalmomi a yaren Tagalog. Amma, wurin da za a tura mu hidima a nan gaba zai ba mu zarafin koyan yaren sosai.
Wata rana a watan Mayu a shekara ta 1955 da muka dawo gida bayan mun tashi daga wa’azi, sai ni da Ɗan’uwa Leach muka samu wasiƙu a ɗakinmu. Da muka karanta sai muka ga cewa an tura mu hidimar masu kula da da’ira. Ni ɗan shekara 22 ne kawai a lokacin, amma wannan hidimar ta ba ni zarafin “zama dukan abu ga dukan mutane” a wasu hanyoyi.
Ina ba da jawabi a taron da’ira da aka yi a yaren Bicol
Alal misali, na ba da jawabi na farko a matsayin mai kula da da’ira a gaban wani shago a wani ƙauye. Ba da daɗewa ba, na koyi cewa mutanen Filifin sun ɗauka cewa yin jawabi ga jama’a yana nufin a yi jawabin fili ko waje! Yayin da nake ziyarar ikilisiyoyi dabam-dabam, nakan ba da jawabi a wasu rumfuna da ake kira gazebo, a kasuwa, a gaban majami’u ko kuma wuraren da ake buga kwallon raga, da wuraren hutu da kuma kan tituna. Akwai lokacin da ruwan sama ya hana ni ba da jawabi a kasuwa a birnin San Pablo, sai na gaya wa ‘yan’uwa da suka manyanta a ba da jawabin a cikin Majami’ar Mulki. Bayan haka, sai suka tambaye ni ko za a ba da rahoto cewa jawabi ne ga jama’a tun da yake ba a ba da jawabin a waje ba!
A lokacin mukan zauna a gidajen ‘yan’uwa. Ko da yake ba su da arziki, su masu tsabta ne sosai. Ina kwana a kan tabarma a ƙasa. Kuma ina wanka a waje, ko da yake ban saba da hakan ba. Nakan yi tafiya da wata irin mota da ake kiran jeepney da bas kuma a wasu lokatai da kwalekwale sa’ad da nake zuwa wasu yankuna da ke kusa da teku. Ban taɓa sayan mota ba a duk shekarun da nake hidima.
Yin wa’azi da ziyarar ikilisiyoyi sun taimaka min in koyi yaren Tagalog. Ban je makaranta ba don koyon wani yare, amma na koya ta wajen sauraron ‘yan’uwa sa’ad da suke wa’azi da kuma a taron ikilisiya. ‘Yan’uwan suna son su taimaka min kuma ina musu godiya don yadda suka yi haƙuri da ni da kuma yi min gyara a lokacin da ya dace.
Da shigewar lokaci, ƙarin ayyuka da na samu sun sa na daidaita ra’ayina game da wasu abubuwa. A shekara ta 1956, sa’ad da Ɗan’uwa Nathan Knorr ya kawo ziyara a ƙasar, mun yi babban taro kuma aka ce in yi ma’amala da kafofin yaɗa labarai. Ban iya aikin ba, amma ‘yan’uwa sun taimaka min sosai. Bayan haka, kafin shekara guda Ɗan’uwa Frederick Franz daga hedkwatarmu ya kawo ziyara. Kuma aka shirya wani babban taro a ƙasar, ni ne na yi hidima a matsayin mai kula da taron. Ƙari ga haka, na koyi darasi daga yadda Ɗan’uwa Franz ya amince da al’adar mutanen. ‘Yan’uwan sun yi farin ciki sosai sa’ad da suka ga Ɗan’uwa Franz ya saka kayan mutanen Filifin sa’ad da yake ba da jawabi.
Ina bukatar in sake daidaita ra’ayina sa’ad da aka tura ni hidimar mai kula mai ziyara. A lokacin, mukan nuna fim ɗin nan The Happiness of the New World Society, a wurin da jama’a suke. A wasu lokatai, ƙwari sukan dame mu. Wutan na’urar da muke amfani da shi ne yake jawo su kuma su maƙale a na’urar. Aiki ne sosai in riƙa goge na’urar bayan hakan! Ƙari ga haka, shirya yadda za a nuna wannan fim ba shi da sauƙi, amma muna farin ciki sosai yayin da mutane suke sanin yadda ƙungiyar Jehobah take gudanar da ayyukanta a dukan duniya.
Firistocin Katolika a wasu wurare suna gaya wa hukumomi su hana mu yin manyan taro. Ƙari ga haka, sukan buga ƙararrawar coci sosai sa’ad da ake ba da jawabai kusa da cocinsu don kada mutane su ji jawabin. Duk da haka, an samu ci gaba sosai kuma mutane da yawa a waɗannan wuraren suna bauta wa Jehobah yanzu.
HIDIMOMIN DA SUKA SA NA DAIDAITA RA’AYINA
A shekara ta 1959, na samu wasiƙa cewa in koma ofishinmu da ke ƙasar. Hakan ya sa na ƙara koyon abubuwa da yawa. Da shigewar lokaci, aka ce na ziyarci wasu ƙasashe. Da nake yin waɗannan tafiye-tafiyen ne na haɗu da Janet Dumond wata mai wa’azi a ƙasar Thailand. Mun yi ta rubuta wa juna wasiƙu kuma daga baya muka yi aure. Mun yi shekaru 51 muna jin daɗin hidimarmu.
Ni da matata a ɗaya daga cikin yankunan da ke bakin teku a Filifin
Na sami gatan ziyarar mutanen Jehobah a ƙasashe 33. Na gode wa Jehobah cewa hidimar da na yi da farko ta taimaka min sosai don na iya bi da ƙalubalen yin sha’ani da mutane dabam-dabam. Waɗannan tafiye-tafiyen sun sa na san mutane sosai kuma ya taimaka min in ga yadda Jehobah yake ƙaunar dukan mutane.—A. M. 10:34, 35.
Muna yin wa’azi a kai a kai
TSUGUNI BA TA ƘARE BA A DAIDAITA RA’AYINA
Yin hidima tare da ‘yan’uwanmu a ƙasar Filifin ya sa ni farin ciki sosai! Adadin masu shela a ƙasar ya ninka na lokacin da na soma hidima shekaru 60 da suka shige sau goma. Ni da matata Janet mun ci gaba da hidima a ofishinmu da ke Quezon City a ƙasar Filifin. Ƙari ga haka, bayan shekara 60 na yin hidima a wata ƙasa, har ila ina bukatar yin canje-canje don in sami zarafin yin duk wani abin da Jehobah yake son in yi. Ƙari ga haka, muna bukatar mu kasance a shirye mu yi kowace irin hidima da ƙungiyar Jehobah take so mu yi don irin canje-canje da ake yi kwanan nan.
Yadda adadin Shaidu ya ƙaru yana sa mu farin ciki sosai
Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu bi ja-gorar Jehobah, kuma hakan ya taimaka mana sosai a rayuwa. Mun kuma yi ƙoƙari mu yi duk wani canjin da ake bukata don mu yi wa ‘yan’uwanmu hidima. Ƙari ga haka, mun ƙuduri aniya mu “zama dukan abu ga dukan mutane,” har tsawon lokacin da Jehobah yake son mu yi hakan.
Har ila muna hidima a ofishinmu da ke Quezon City