Tarihi
Jehobah Ya Koyar da Ni In Yi Nufinsa
Max Lloyd ne ya ba da labarin
A cikin wani dare a shekara ta 1955, a ƙasar Paraguay da ke nahiyar Amirka ta Kudu, ’yan tarzoma sun kewaye gidan da ni da wanda muke hidima tare muke zama. ’Yan tarzomar suna ihu suna cewa: “Allahnmu mai shan jini ne, kuma yana son ya sha jinin waɗannan baren.” Ta yaya muka kasance a cikin wannan yanayin?
JEHOBAH ya fara koya mini yin nufinsa shekaru da yawa da suka shige a ƙasar Ostareliya inda na yi girma. Mahaifina ya karɓa littafin nan Enemies daga hannun wata Mashaidiya a shekara ta 1938. Da shi da mahaifiyata sun riga sun gaji da koyarwar limamin cocinsu don limamin bai gaskata da wasu sassa na Littafi Mai Tsarki ba. Bayan shekara ɗaya, iyayena suka keɓe kansu kuma suka yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah. Daga wannan lokacin ne na fara saka yin nufin Jehobah farko a rayuwata. Yayata Lesley wadda ta girme ni da shekara biyar ta yi baftisma bayan iyayena, ni kuma na yi baftisma a shekara ta 1940, sa’ad da nake ɗan shekara tara.
Ba da daɗewa ba bayan Yaƙin Duniya na biyu, aka hana Shaidun Jehobah buga da kuma rarraba littattafai a ƙasar Ostareliya. Saboda haka, sa’ad da nake yaro, na koyi bayyana imanina ta wajen yin amfani da Littafi Mai Tsarki kaɗai. Sai na fara zuwa makaranta da Littafi Mai Tsarki don bayyana dalilin da ya sa ba zan sara wa tuta ba ko kuma goyon baya yaƙin da ƙasashe suke yi.—Fit. 20:4, 5; Mat. 4:10; Yoh. 17:16; 1 Yoh. 5:21.
Ɗaliban makarantarmu da yawa suka ƙi yin tarayya da ni domin suna gani cewa ni “ɗan leƙen asirin ƙasar Jamus” ne. A lokacin, ana nuna silima a makaranta. Ana bukatar kowa ya tashi kuma ya yi taken ƙasar kafin a fara nuna silima ɗin. Don na ƙi tashiwa, yara maza biyu ko uku suka ja gashi na don in tashi. Daga baya aka kore ni daga makaranta domin na ƙi canja imanina da ke bisa Littafi Mai Tsarki. Amma, na kammala makarantana a gida.
NA CIM MA MAƘASUDINA
Na kafa maƙasudi cewa zan soma hidima ta cikakken lokaci a matsayin majagaba sa’ad da na kai shekara 14. Amma na yi baƙin ciki sa’ad da iyayena suka ce zan yi aiki tukuna. Sun nace zan kasance tare da su kuma na biya kuɗin haya da na abinci, amma sun gaya mini cewa zan soma hidimar majagaba sa’ad da na kai shekara 18. Hakan ya sa muna zancen kuɗi kullum da iyayena. Na nace cewa ina son na riƙa ajiye kuɗin don hidimar majagaba, amma suna ta kwacewa.
A lokacin da zan soma hidimar majagaba, iyayena sun gaya mini cewa sun ajiye mini kuɗin a bankin. Sai suka ba ni dukan kuɗin don na saya tufafi da wasu abubuwa da nake bukata don hidimar majagaba. Sun koya mini na kula da kaina kuma kada na sa rai cewa wasu za su kula da ni. Duk sa’ad da na tuna da wannan, ina sanin cewa sun taimake ni sosai.
Sa’ad da ni da yayata Lesley muke girma, majagaba sukan sauka a gidanmu, kuma mun ji daɗin fita wa’azi tare da su. Muna yawan yin wa’azi na gida-gida da na kan titi, da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a ƙarshen mako. A waɗannan shekarun, ana bukatar kowane mai shela ya ba da sa’o’i 60 a wata. Mahaifiyata tana samun waɗannan sa’o’in, ta hakan ta kafa mini da yayata Lesley misali mai kyau.
HIDIMAR MAJAGABA A TSIBIRIN TASMANIA
Na fara hidimar majagaba a tsibirin Tasmania da ke ƙasar Ostareliya tare da yayata da mijinta. Amma, ba da daɗewa ba suka halarci aji na 15 na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead. Da yake ni mai jin kunya ne sosai kuma ban taɓa zama ni kaɗai ba, wasu suka yi zato cewa zan yi hidima na wata uku kawai a Tasmania. Amma, a cikin shekara guda, wato a shekara ta 1950, aka ba ni wani gata a cikin ikilisiya, wannan gatan daidai ne da na mai tsara ayyukan rukunin dattawa a yau. Daga baya, aka naɗa ni majagaba na musamman, kuma wani ɗan’uwa matashi ya zama abokin hidimata.
An tura mu hidima a wani gari da ke ware inda ake haƙa jan ƙarfe kuma babu Shaidu a wurin. Bas ne ya kai mu wurin kuma mun isa wurin da rana. A ranar da muka isa garin mun kwana a wani tsohon hotal daddare. Washegari da muke wa’azi gida-gida, muka gaya wa waɗanda muke wa wa’azi cewa muna neman ɗakin haya. Kafin dare ya yi, wani mutum ya gaya mana cewa akwai wani ɗakin haya a gidan wani limami a kusa da cocin Presbyteria kuma mu yi magana da shi. Limamin mai fara’a ne kuma ya ba mu ɗakin. Fitowa daga gidan limamin kowace rana zuwa wa’azi wani abin mamaki ne.
Mutane suna saurarar wa’azi sosai a yankin. Mun tattauna da mutane sosai kuma muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Sa’ad da hukumomin coci da ke babban birnin jihar suka ji cewa Shaidun Jehobah suna zama a gidan limaminsu, suka gaya masa ya kore mu nan da nan. Sai aka waye gari ba mu da masauki!
Washegari bayan muka yi wa’azi har tsakar rana, muka nemi inda za mu kwana. Mun samu wurin kwanciya a ƙarƙashin rumfan wani filin wasa. Mun ɓoye jakunkunarmu a wajen kuma muka ci gaba da wa’azi. Da dare ya soma yi, muka tsai da shawara mu yi wa’azi a gidajen da suka rage a titin. A wani gida da muka je, sai mai gidan ya ba mu hayar ciki da falo a gidansa!
HIDIMAR KULA DA DA’IRA DA KUMA MAKARANTAR LITTAFI MAI TSARKI TA GILEAD
Bayan watanni takwas a wannan yankin, ofishin reshe na Ostareliya ya gayyace ni na zama mai kula da da’ira. Hakan ya sa ni mamaki don ni ɗan shekara 20 ne kawai a lokacin. An koyar da ni na ’yan makonni, sai na soma ziyarar ikilisiyoyi a kai a kai don in ƙarfafa su. Ko da yake ni matashi ne, amma ’yan’uwa ba su rena ni ba, sun daraja aikin da nake yi.
Ina ziyarar ikilisiyoyi a hanyoyi dabam-dabam. Wani mako nakan yi tafiya da bas, wani mako kuma da jirgin ƙasa, a wani lokaci kuma da mota ko kuma a kan babur ina riƙe da jakar ɗaukan kaya da kuma jakar wa’azi. Zama da ’yan’uwa yana sa ni farin ciki sosai. Wani ɗan’uwa mai tsara ayyukan rukunin dattawa yana son in zauna tare da shi ko da yake ana kan gina gidansa. Wannan makon an yi mini wurin kwanciya a cikin baho, amma mun ƙarfafa juna sosai!
A shekara ta 1953, an gayyace ni zuwa aji na 22 na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead kuma hakan ya ba ni mamaki sosai. Ko da yake ina farin ciki amma na damu ƙwarai, saboda a cikin shekara ɗaya, yayata ta yi rashin lafiya kuma ta rasu a ƙasar Pakistan, inda aka tura ita da mijinta hidima bayan sun sauke karatu a Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead a ranar 30 ga Yuli a shekara ta 1950. Yaya iyayena za su ji idan aka tura ni hidima zuwa wata ƙasa bayan na sauke karatun? Amma sun ce: “Ka tafi ka bauta wa Jehobah a duk inda yake so.” Ban sake ganin Mahaifina ba. Ya rasu a shekara ta 1957.
Ba da daɗewa ba, ni da wasu ’yan’uwa ’yan ƙasar Ostareliya biyar, muka fara tafiya mai tsawon makonni shida a cikin jirgin ruwa zuwa Birnin New York. Sa’ad da muke tafiya, muka yi ta karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma tattaunawa da fasinjoji da suke cikin jirgin. Da muka isa, kafin mu je inda ake makarantar a South Lansing, a New York, muka halarci taron ƙasashe da aka yi a filin wasan Yankee a watan Yuli na shekara ta 1953. Mutane 165,829 ne suka halarci taron!
A ajinmu, mu ɗalibai guda 120 ne daga ƙasashe dabam-dabam. Bayan mun sauke karatu ne aka gaya mana inda za mu je yin hidima. Ba tare da ɓata lokaci ba muka shiga cikin laburaren Gilead don mu koya game da waɗannan ƙasashe da aka tura mu hidima. Na karanta cewa ƙasar Paraguay, inda aka tura ni hidima, ƙasa ce da aka sha yin rikicin siyasa da kuma juyin mulki. Wata rana da gari ya waye bayan na isa ƙasar, sai na tambayi wasu abokan wa’azina dalilin da ya sa ake yin hayaniya daddaren. Sai suka yi murmushi suke ce: “Wannan shi ne juyin mulki na farko da ka shaida. Ka duba waje.” Da na duba sai na ga sojoji a ko’ina!
ABIN DA BA ZAN TAƁA MANTAWA BA
Akwai wani lokacin da na bi wani mai kula da da’ira zuwa wata ikilisiya da ke da ɗan nisa don mu nuna wannan fim na The New World Society in Action. Muka yi tafiya na sa’o’i takwas ko tara, da farko, mun hau jirgin ƙasa, bayan haka muka hau keken da doki yake ja kuma a ƙarshe muka yi amfani da keken shanu. Mun ɗauki na’urar nuna silima da kuma janareto. Sa’ad da muka isa garin, muka je wa’azi a gonakin da ke wajen kuma muka gayyaci mutane su zo su kalli fim da za mu nuna a daren. Mutane 15 ne suka hallara.
Bayan mun nuna fim ɗin na minti 20, sai mutane suka gaya mana cewa mu shiga cikin gida ba tare da ɓata lokaci ba. Muka ɗauki na’urar muka gudu cikin gida. A lokacin ne wasu maza suka soma ihu kuma suna harba bindiga suna waƙa suna cewa: “Allahnmu mai shan jini ne, kuma yana so ya sha jinin waɗannan baren.” Bare guda biyu ne kawai ke wajen kuma ni ne ɗaya daga cikinsu! Waɗanda suka zo kallon fim ɗin suka hana ’yan zanga-zangan shiga cikin gidan. Sai ’yan zanga-zangan suka tafi, amma suka sake dawowa da misalin ƙarfe uku na asuba, suna harban bindiga kuma suka ce za su kama mu sa’ad da muke komawa cikin garin da rana.
’Yan’uwan suka samu ɗan dokar garin, sai ya zo da rana tare da dawaki guda biyu don ya kai mu cikin gari. Sa’ad da muke komawa, duk lokacin da muka yi kusa da jeji ko inda itatuwa suke, sai ya cire bindigarsa kuma ya yi gaba don ya bincika wurin da kyau. Na zo na lura cewa ana sufuri da doki sosai a wannan wurin, saboda haka, ni ma na sayi doki daga baya.
MUN SAMU ƘARIN MASU WA’AZI
Ko da yake limamai suna tsananta mana, amma mun ci gaba da samun nasara sosai a aikin wa’azi. A shekara ta 1955, muka samu ƙarin masu wa’azi har da wata ’yar ƙasar Kanada mai suna Elsie Swanson, wadda ta sauke karatu a aji na 25 na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead. Muka yi hidima tare a ofishin reshe na ɗan lokaci kafin a tura ta wani gari. Ta ba da kanta ga hidimar Jehobah ba tare da taimakon iyayenta ba domin su ba Shaidu ba ne. A ranar 31 ga watan Disamba, na shekara ta 1957, na auri Elsie kuma muka fara zama a inda masu wa’azi a ƙasashen wajen suke zama a kudancin ƙasar Paraguay.
Ba mu da ruwan famfo a gidan, amma akwai rijiya a bayan gidan. Wurin wanka da ban-ɗaki suna waje, babu na’urar wanki kuma babu firiji. Muna sayan abinci da za mu dafa kowace rana. Amma, irin wannan rayuwa mai sauƙi da kuma zumuncin da ke tsakaninmu da ’yan’uwanmu a cikin ikilisiya ya sa mun ji daɗin zaman aurenmu sosai.
A shekara ta 1963, jim kaɗan bayan mun je ziyarar mahaifiyata a ƙasar Ostareliya, sai ta samu ciwon zuciya sanadiyyar farin cikin ganina bayan shekara goma. Yayin da lokaci ya kai da za mu koma wurin da muke hidima a ƙasar Paraguay, mun fuskanci wata babbar matsala. Mun yi tunani cewa ko zai dace mu bar mahaifiyata a asibiti kuma wani ya kula da ita mu kuma mu koma hidimarmu a ƙasar Paraguay. Bayan da muka yi addu’a sosai a kan batun, ni da matata Elsie muka tsai da shawara mu zauna a gida mu yi jinyar mahaifiyata. Mun yi hakan kuma muka ci gaba da hidima ta cikakken lokaci har ta rasu a shekara ta 1966.
Na samu gatan yin hidimar kula da da’ira da kuma gunduma a ƙasar Ostareliya na wasu shekaru da kuma koyar da dattawa a Makarantar Hidima ta Mulki. Muka sake samun wani gata. An naɗa ni yin hidima a matsayin wanda yake ɗaya daga cikin Kwamitin Reshe na farko a ƙasar Ostareliya. A lokacin muna son mu gina sabon ofishin reshe, kuma aka naɗa ni ciyaman ɗin kwamiti na ginin. Muka gina kyakkyawan reshe da taimakon ƙwararrun ma’aikata masu haɗin kai.
Daga baya, aka mai da ni Sashen Kula da Hidima, wato, sashen da ke kula da aikin wa’azi. Aka sake ba ni wani gata har ila, na ziyarar rassa a dukan duniya a matsayin mai ziyara mai kula da reshe don tanadar da taimako da kuma ƙarfafawa. Wani abin da ya ƙarfafa ni sosai shi ne ziyarar wasu ƙasashe da na yi inda wasu ’yan’uwa suka yi shekaru da yawa suna cikin kurkuku da kuma sansanin fursuna saboda biyayya da kuma aminci da suka nuna ga Jehobah.
HIDIMAR DA MUKE YI YANZU
Bayan da na dawo daga wata ziyara a matsayin mai ziyara mai kula da reshe a shekara ta 2001, sai na samu wata wasiƙar gayyata zuwa Brooklyn, New York, don in yi hidima a matsayin ɗan Kwamitin Reshe na Amirka da aka kafa ba da daɗewa ba. Da ni da Elsie muka yi addu’a a kan wannan sabon gatan kuma muka yi na’am da wannan gayyatar. Bayan fiye da shekara 11 yanzu muna kan hidima a Brooklyn.
Ina farin ciki sosai cewa Jehobah ya ba ni matar da take farin cikin yin duk wani abin da yake so. Yanzu da ni da Elsie ’yan shekara 81 ne kuma muna da koshin lafiya. Muna ɗokin more koyarwar Jehobah har abada da kuma albarkar da waɗanda suka ci gaba da yin nufinsa za su samu.
[Bayanin da ke shafi na 19]
Wani mako nakan yi tafiya da bas, wani mako kuma da jirgin ƙasa, a wani lokaci kuma da mota ko kuma a kan babur ina riƙe da jakar ɗaukan kaya da kuma jakar wa’azi
[Bayanin da ke shafi na 21]
Muna ɗokin more koyarwar Jehobah har abada
[Hotona a shafi na 18]
Hagu: Sa’ad da nake hidimar kula da da’ira a ƙasar Ostareliya
Dama: Ni da iyayena
[Hoto a shafi na 20]
Aurenmu, a ranar 31 ga Disamba, 1957