Kana Jin Daɗin Karanta da Kuma Yin Nazarin Kalmar Allah Kuwa?
“SA’AD da na soma karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, na ɗauke shi kamar abu mai cin rai marar daɗi,” in ji Lorraine. “Saboda haka ba na mai da hankali sosai domin yana da wuyar fahimta.”
Wasu ma sun yarda cewa sa’ad da suka soma karanta Littafi Mai Tsarki, ba sa jin daɗinsa. Duk da haka, sun nace domin sun san cewa ya dace a karanta Nassosi Masu Tsarki. Marc ya ce: “Yana da sauƙi mu ƙyale abubuwa da suke raba hankali su hana mu karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin nazari na kanmu. Na yi addu’a sosai kuma na yi ƙoƙari don na riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai.”
Mene ne za ka iya yi don ka nuna godiya ga rubutacciyar Kalmar Allah, wato, Littafi Mai Tsarki? Ta yaya za ka ji daɗin karanta shi? Ka yi la’akari da shawarwari na gaba.
Maƙasudai da Hanyoyin Yin Hakan
Ka riƙa yin addu’a sa’ad da kake son ka karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka mai da hankali ga karatun. Ka roƙi Jehobah ya taimake ka ka yi ɗokin yin nazarin Kalmarsa. Ka roƙe shi ya buɗe zuciyarka da kuma tunaninka don ka fahimci hikimarsa sosai. (Zab. 119:34) Ba za ka ji daɗin ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki idan ba ka yi hakan ba. Lynn ta ce: “Ina cika sauri sa’ad da nake karanta Littafi Mai Tsarki kuma yin hakan yana sa na rasa abubuwa masu muhimmanci da ke ciki. Sau da yawa, ba na fahimtar ainihin abubuwan da ke ciki. Amma dai, na yi addu’a cewa Allah ya ba ni kamewa, kuma hakan ya taimake ni na mai da hankali ga abin da nake karantawa.”
Ka ɗauki abin da ka koya da muhimmanci. Ka tuna cewa fahimta da kuma yin amfani da gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su sa ka samu rai. Saboda haka, ka yi ƙoƙari sosai don ka samu abubuwa masu muhimmanci kuma ka yi amfani da su. Chris ya ce: “Na bincike abubuwan da suka taimake ni na ga ra’ayoyi da sha’awoyi marar kyau da nake da su. Ganin yadda Littafi Mai Tsarki da littattafanmu da yawa suke ɗauke da abubuwa da suke amfane ni sosai, ko da marubutan ba su taɓa haɗuwa da ni ba, yana da ban wartsakewa sosai.”
Ka kafa wa kanka maƙasudai da za ka iya cim ma su. Ka yi ƙoƙari ka koya sabon abu game da waɗanda aka ba da labaransu a cikin Littafi Mai Tsarki. Za ka iya samun abubuwa masu burgewa da yawa game da su ta bincika littattafan nan Insight on the Scriptures ko kuma Watch Tower Publications Index. Yayin da kake koya cewa maza da mata da aka ba da labarinsu a cikin Littafi Mai Tsarki suna da halaye da tunani kamar mu, za ka amfana sosai.
Ka nemi sababbin hanyoyi na bayyana Nassosi. (A. M. 17:2, 3) Sophia tana da wannan maƙasudi sa’ad da take karanta Littafi Mai Tsarki. Ta ce: “Muradi na shi ne na koya kuma na samu sabuwar hanyar yin mahawwara da mutane a hidima da kuma a wasu lokatai, don na samu na bayyana gaskiyar Littafi Mai Tsarki sosai ga mutane. Hasumiyar Tsaro kayan aiki ne mai kyau na cim ma wannan.”—2 Tim. 2:15.
Ka zana hoto na labarun Littafi Mai Tsarki a zuci. Ibraniyawa 4:12 ya ce: “Maganar Allah mai-rai ce.” Yayin da kake karanta Nassosi, ka bari Kalmar Allah ta kasance a tunaninka ta zana hoton zuci na abubuwan da waɗanda aka ba da labaransu a cikin Littafi Mai Tsarki suka gani. Ka yi ƙoƙari ka ji abin da suka ji kuma ka ji yadda suka ji. Ka gwada labaransu da wani yanayi na rayuwarka. Ka yi koyi da yadda suka aikata. Hakan zai daɗa fahiminka kuma zai sa labarun Littafi Mai Tsarki su kasance a zuciyarka.
Ka keɓe lokaci don nassosi masu wuya da kuma bayaninsu don ka fahimce su sosai. Ka keɓe lokaci mai yawa don yin kowanne nazari. Za ka iya ganin tambaya mai kyau da za ka bukaci yin ƙarin bincike a kai. Ka duba ma’anar kalmomin da ba ka sani ba a cikin ƙamus, idan kana da Littafi Mai Tsarki na wani yare da ke da wuraren ƙarin bincike, za ka iya yin amfani da shi. Idan ka fahimci kuma ka yi amfani da abin da ka karanta, za ka ji daɗin karanta rubutacciyar Kalmar Allah sosai. Za ka iya furtawa kamar marubucin wannan zaburar: “Na ɗauki shaidunka [Jehobah] su zama gādo a gareni har abada; Gama su ne ƙawar zuciyata.”—Zab. 119:111.
Ka guji yin hanzari don kammala karatun. Ka keɓe lokaci daidai wa daida don nazari na kanka. Ka daidaita wannan da lokacin da kake amfani da shi don yin shirin tarurrukan ikilisiya. Raquel ya ce: “Sau da yawa ina yin fargaba sosai har ba zan iya mai da hankali ba. Saboda haka, keɓe lokaci kaɗan don nazari yana da amfani. Hakan yana taimaka mini na amfana sosai daga nazari na.” Chris ya amince: “Sa’ad da na yi hanzari, lamiri na yakan dame ni domin ba na amfana sosai. Nazarin ba ya yawan kai zuciya ta.” Saboda haka, ka natsu sosai.
Ka koyi yin marmarin kalmar Allah sosai. Manzo Bitrus ya ce: “Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto.” (1 Bit. 2:2) Jarirai ba sa ƙoƙartawa kafin su yi marmarin shan madara. Wannan marmarin daga haihuwa ne. Amma Nassosi sun faɗi cewa muna bukatar mu yi marmarin Kalmar Allah. Idan kana karanta shafi ɗaya kawai na Littafi Mai Tsarki kullum, za ka soma yin marmari. Abin da a farko kana gani kamar yana da wuya zai zama abin sha’awa.
Ka yi bimbini a kan ayoyin Nassi. Za ka amfana sosai idan ka yi bimbini a kan abin da ka karanta. Yin hakan zai taimake ka ka harhaɗa batutuwa na ruhaniya da ka bincika. Ba da daɗewa ba, za ka samu tarin hikima kamar lu’u ’lu’u, wadda dukiya ce mai kawo murna.—Zab. 19:14; Mis. 3:3.
Kwalliya Ce da Ke Biyan Kuɗin Sabulu
Nacewa a halin yin nazari a kai a kai yana bukatar ƙoƙari, amma albarkar tana da yawa. Za ka kyautata fahiminka na Nassi. (Ibran. 5:12-14) Fahimi da hikima da ka samu don karanta hurarrun Nassosi suna sa ka samu farin ciki da lumana da kuma salama. Hikima da ke cikin Kalmar Allah tana kama da “itacen rai” ga waɗanda suka samu kuma suka yi amfani da ita.—Mis. 3:13-18.
Yin nazari mai zurfi na Kalmar Allah zai iya sa ka samu zuciya mai hikima. (Mis. 15:14) Hakan zai sa ka riƙa ba da shawara da ke bisa Littafi Mai Tsarki. Idan ka ƙyale abin da ka karanta daga Nassosi da kuma littattafai da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya wallafa su ja-gorance ka, za ka shaida wartsakewa da kuma lumana da hurarriyar Kalmar Jehobah take bayarwa. (Mat. 24:45) Za ka daɗa kasancewa da hali mai kyau da gaba gaɗi da kuma halin da ya jitu da Kalmar Allah. Bugu da ƙari, dukan abu da ya shafi dangantakarka da Allah zai yi nasara.—Zab. 1:2, 3.
Zuciya da ke ƙaunar Allah sosai za ta motsa ka ka faɗa wa wasu imaninka. Yin wannan ma yana kawo sakamako mai kyau. Sophia tana ƙoƙari wajen tunawa da kuma yin amfani da Nassosi dabam dabam don ta jawo hankalin masu gida kuma ta sa hidimar Kirista ta kasance da amfani sosai. Ta ce: “Ganin mutane suna aikatawa bisa ga kalmomin Littafi Mai Tsarki yana kawo farin ciki sosai.”
Amfani mafi muhimmanci na jin daɗin karanta Kalmar Allah shi ne, samun dangantaka na kud da kud da Jehobah. Nazarin Littafi Mai Tsarki yana sa ka san mizanansa kuma ka daraja ƙaunarsa da karimcinsa da kuma adalcinsa. Babu kowaɗanne biɗe-biɗe da suka fi wannan muhimmanci. Ka shagala sosai a yin nazarin Kalmar Allah. Yin hakan kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu.—Zab. 19:7-11.
[Akwati/Hotuna da ke shafi na 5]
YIN KARATUN KALMAR ALLAH: MAƘASUDAI DA KUMA HANYOYIN YIN HAKAN
▪ Ka riƙa yin addu’a sa’ad da kake son ka karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka mai da hankali ga karatun.
▪ Ka ɗauki abin da ka koya da muhimmanci.
▪ Ka kafa wa kanka maƙasudai da za ka iya cim ma su.
▪ Ka nemi sababbin hanyoyi na bayyana Nassosi.
▪ Ka zana hoto na labarun Littafi Mai Tsarki a zuci.
▪ Ka keɓe lokaci don nassosi masu wuya da kuma bayaninsu don ka fahimce su sosai.
▪ Ka guji yin hanzari don kammala karatun.
▪ Ka koyi yin marmarin kalmar Allah sosai.
▪ Ka yi bimbini a kan ayoyin Nassi.
[Hoton da ke shafi na 4]
Sa’ad da kake karanta labari na Littafi Mai Tsarki, ka zana hoton zuci cewa kana cikin irin yanayin