Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 1 p. 4
  • Ta Yaya Zan Soma Karatun?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Zan Soma Karatun?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ka Amfana Daga Karanta Littafi Mai Tsarki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Karatun Littafi Mai Tsarki—Mai Amfani Kuma Mai Daɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Kana Jin Daɗin Karanta da Kuma Yin Nazarin Kalmar Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Riƙe Kalmar Allah Gam
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 1 p. 4

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA KA JI DAƊIN KARANTA LITTAFI MAI TSARKI

Ta Yaya Zan Soma Karatun?

Wata mata tana addu’a kafin ta karanta Littafi Mai Tsarki

Mene ne za ka yi da zai sa ka ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka amfana daga karatun? Ga abubuwa biyar da suka taimaki mutane da yawa.

Ka nemi wuri mai kyau. Ka nemi inda ba a surutu. Ka kawar da abubuwan da za su iya raba hankalinka. Ka nemi wurin da akwai haske da kuma iska mai daɗi, hakan zai sa ka amfana sosai daga karatun.

Ka kasance da ra’ayin da ya dace. Tun da Littafi Mai Tsarki daga wurin Ubanmu na sama ne, za ka amfana sosai idan ka kasance da hali irin na yaron da yake so ya koyi abubuwa daga wurin iyayensa. Ka kawar da duk wani ra’ayi marar kyau da kake da shi game da Littafi Mai Tsarki don Allah ya koyar da kai.​—⁠Zabura 25:⁠4.

Ka riƙa yin addu’a kafin ka soma karatun. Ba abin mamaki ba ne cewa muna bukatar taimakon Allah don mu fahimci Littafi Mai Tsarki, domin Kalmarsa ce. Allah ya yi alkawarin cewa zai ba da “ruhu mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa.” (Luka 11:13) Ruhu mai tsarki zai taimaka maka ka fahimci Kalmar Allah. Da shigewar lokaci, zai sa ka iya fahimtar “zurfafan al’amuran Allah.”​—⁠1 Korintiyawa 2:​10, Littafi Mai Tsarki.

Ka karanta yadda za ka fahimta. Kada ka riƙa karantu kawai. Amma ka riƙa yin tunani a kan abin da kake karantawa. Ka tambayi kanka: ‘Waɗanne halaye ne mutumin da nake karantu a kansa yake da su? Ta yaya zan yi koyi da shi?’

Ka kafa maƙasudai. Idan kana so ka amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki, kana bukatar ka koyi abin da zai iya kyautata rayuwarka. Za ka iya kafa maƙasudai kamar su: ‘Ina so in san Allah sosai.’ ‘Ina so in zama mutumin kirki ko miji ko kuma matar kirki.’ Bayan haka, sai ka nemi nassosin da za su taimaka maka ka cim ma su.a

Waɗannan shawarwari guda biyar za su iya taimaka maka ka soma karatun Littafi Mai Tsarki. Amma mene ne zai sa ka ji daɗin karatun sosai? Talifi na gaba zai ba ka wasu shawarwari.

a Idan ba ka san ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka maka ba, Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka.

KA AMFANA DAGA KARATUN

  • Ka bi a hankali kuma kada ka riƙa sauri

  • Ka yi tunani sosai, wato ka ga kamar abin na faruwa a gabanka

  • Ka yi ƙoƙarin ganin yadda ayoyin suka shafe ka

  • Ka nemi darussa daga abin da kake karantawa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba