Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 11/1 pp. 8-9
  • Muna Bauta wa Jehobah da Farin ciki Duk da Talaucinmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Muna Bauta wa Jehobah da Farin ciki Duk da Talaucinmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • GAGARUMIN CANJI A RAYUWARMU
  • SABABBIN MATSALOLI
  • ABUBUWA MASU BAN FARIN CIKI
  • JEHOBAH YA AMSA ADDU’ARMU
  • HAR ILA MUNA BAUTA WA JEHOBAH
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 11/1 pp. 8-9

LABARI

Muna Bauta wa Jehobah da Farin Ciki Duk da Talaucinmu

Alexander Ursu ne ya ba da labarin

Kakana da mahaifina sun zauna a wani gida da ba a kammala gininsa ba a ƙauyen Cotiujeni da ke arewancin ƙasar Moldova. A wannan ƙauyen ne aka haife ni a watan Disamba na shekara ta 1939. Iyayena sun zama Shaidun Jehobah wajen shekaru bakwai kafin a haife ni. Bayan mahaifiyata ta fahimci cewa kakana yana da ilimin Littafi Mai Tsarki fiye da firist da ke ƙauyen, sai ta yarda ta zama Mashaidiya.

Sa’ad da nake ɗan shekara uku, an kai mahaifina da kawuna da kuma kakana sansanin bauta don sun ƙi su yi yaƙi da kuma siyasa. Mahaifina ne kawai ya tsira. A shekara ta 1947 bayan Yaƙin Duniya na Biyu, mahaifina ya dawo gida da mummunan ciwon baya. Ko da yake yana rashin lafiya sosai, ya ci gaba da riƙe imaninsa.

GAGARUMIN CANJI A RAYUWARMU

A ranar 6 ga Yuli a shekara ta 1949 sa’ad da nake ɗan shekara tara, an cunkushe iyalinmu da ɗarurruwan Shaidu daga ƙasar Moldova a cikin motocin kwashe shanu kuma aka kai mu bauta a Siberiya. Bayan mun yi tafiya mai nisan mil fiye da 4,000 cikin kwanaki 12, sai muka tsaya a tashar jirgi da ke garin Lebyazhe. Hukumomin garin suna nan suna jiran mu. Da muka iso, sai suka rarraba mu zuwa ƙananan rukunoni kuma nan da nan aka kai mu wurare dabam-dabam a yankin. Waɗanda suke rukuninmu sun zauna a cikin wata makaranta da an daina amfani da ita. Mun gaji tilis kuma muna matuƙar baƙin ciki. Wata tsohuwar ’yar’uwa a cikinmu ta soma waƙa ciki-ciki. Wasu Shaidu ne suka rubuta waƙar a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, kuma dukanmu muka rera waƙar tare. Ga kalmomin waƙar:

“An kai ’yan’uwa da yawa zuwa bauta a wurare masu nisa.

An kai su arewa da kuma gabas.

An wahal da su kuma aka tsananta musu domin sun yi aikin Allah.”

Da shigewar lokaci, mun soma halartan taro kowane Lahadi a wani wuri mai nisan mil 8 don mu koyi Littafi Mai Tsarki. Sau da yawa mukan tashi da asuba a cikin ɗāri, a lokacin da ake bala’in sanyi kuma mu yi tafiya cikin ƙanƙara da ke kama mu a kwankwaso. Mu 50 ko fiye da hakan mukan cunkushe a wani ƙaramin ɗaki. Muna soma taron da rera waƙoƙi biyu ko uku. Sai a yi addu’a sa’an nan a tattauna amsoshin tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki. Muna hakan har tsawon awa ɗaya ko fiye da hakan, sa’an nan mu rera wasu waƙoƙi kuma mu tattauna wasu amsoshin tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki. Babu shakka, wannan tsarin ya ƙarfafa bangaskiyarmu sosai!

SABABBIN MATSALOLI

A shekara ta 1960, mu da aka kai mu bauta mun ɗan sami ’yanci kuma hakan ya ba ni damar zuwa ƙasar Moldova ko da yake mu talakawa ne. A nan ne na haɗu da Nina, wadda iyayenta da kakanninta ma Shaidu ne. Ba da daɗewa ba muka yi aure kuma muka koma Siberiya inda aka haifi ’yarmu Dina a shekara ta 1964 sa’an nan ɗanmu Viktor a shekara ta 1966. Shekaru biyu bayan haka, muka koma ƙasar Yukiren kuma muka kama zama a cikin wani ƙaramin gida a Dzhankoy, wani birni mai nisan mil 100 daga Yalta a tsibirin Crimea.

A Crimea da kuma ƙasar Rasha ta dā, an sa takunkumi a kan ayyukan Shaidun Jehobah. Amma ba a matsa mana lamba ko kuma tsananta mana kamar yadda aka saba ba. Wannan ya sa wasu Shaidu suka soma sanyi-sanyi a bautarsu. Sun ɗauka cewa tun da sun riga sun sha wahala a yankin Siberiya, yanzu zai dace su mai da hankali ga tara dukiya.

ABUBUWA MASU BAN FARIN CIKI

A ranar 27 ga Maris a 1991, an ba mu ’yancin bauta a duk ƙasar Rasha ta dā, kuma an yi rajistar addininmu. Nan da nan aka soma shirin taron gunduma na musamman na tsawon kwanaki biyu a wurare bakwai. Mu za mu halarci wanda za a yi a Odessa, a ƙasar Yukiren, kuma za a soma shi a ranar 24 ga Agusta. Na tafi wurin wata ɗaya kafin wannan lokacin don mu shirya babban filin wasa da aka samu don taron.

Mukan wuni muna aiki, kuma sau da yawa idan dare ya yi muna kwana a kan benci da ke cikin filin. ’Yan’uwanmu Shaidu mata da yawa sun share filin wasan. Sharar da aka kwashe a filin zai cika wajen babban tirela biyu ko kuma wajen tan 70. Waɗanda suke hidima a sashen da ke kula da masauki sun yi iya ƙoƙarinsu don su samu masauki wa mutane 15,000 da za su halarci taron. Farat ɗaya kawai, ana wani sai ga wata!

A ranar 19 ga watan Agusta, kwanaki biyar kafin a soma taron, an yi wa Mikhail Gorbachev, Shugaban tarin ƙasashe da ake kira USSR ɗaurin talala, sa’ad da ya je hutun shaƙatawa a birnin Yalta, kusa da inda muke. Sai aka hana mu izinin gudanar da taron. Waɗanda za su zo taron sun soma kiran ofishin reshe kuma suna tambaya: “Me za mu yi da tikitin bas da kuma jirgin ƙasa da muka saya?” Bayan waɗanda suke tsara taron sun yi addu’a sosai, sai suka gaya musu cewa su zo kawai.

An ci gaba da yin addu’a da shirye-shirye. Sa’ad da baƙin suka soma isowa daga ƙasashen Soviet Union, ’yan’uwa a sashen da ke kula da jigilar masu zuwa taron sun tafi tarban su don su kai su masaukai. Kowace safiya, mambobin Kwamitin Taron Gundumar suna zuwa wurin hukumar birnin. Kowane dare da ’yan’uwan nan suke dawowa, ba sa kawo wani albishiri.

JEHOBAH YA AMSA ADDU’ARMU

A ranar Alhamis, 22 ga watan Agusta, kwana biyu kafin ranar da aka sanya za a soma taron, sai Kwamitin Taron Gundumar suka dawo da albishiri. Sun ce an ba mu izini mu gudanar da taron! Yayin da muke waƙar buɗe taron da kuma addu’a a bayan hakan, kamar mu zuba ruwa a ƙasa mu sha saboda murna. Bayan da aka tashi taron a ranar Asabar, ba mu koma masaukinmu nan da nan ba domin muna ta taɗi har dare da abokai da muka yi kwan-biyu da ganin juna. Waɗannan Kiristoci ne masu bangaskiya sosai da suka jimre mawuyacin gwaji.

An sami ci gaba sosai tun shekaru 22 bayan wannan taron gundumar. An gina Majami’un Mulki da yawa a duk ƙasar Yukiren, kuma adadin masu wa’azin Mulkin Allah ya haura daga mutum 25,000 a shekara ta 1991 zuwa sama da 150,000 a yanzu!

HAR ILA MUNA BAUTA WA JEHOBAH

Har ila, iyalinmu na zama a cikin wannan gidan da muka samu a birnin Dzhankoy da ke da kimanin mutane 40,000 a yanzu. Ko da yake iyalan Shaidun Jehobah kaɗan ne kawai a Dzhankoy a lokacin da muka zo daga Siberiya a shekara ta 1968, yanzu akwai ikilisiyoyi shida a birnin.

Iyalina ma ta samu ƙaruwa. A yau, ni da matata da yaranmu da jikokinmu da kuma tattaɓa-kunnenmu ne muke da rai kuma muna bauta wa Jehobah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba