Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 11/1 p. 4
  • Ta Yaya Muka Soma Wanzuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Muka Soma Wanzuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Allah Ya Halicci Mutane?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Aljannar da Aka Rasa
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Me Ya Sa Akwai Mugunta da Wahala a Ko’ina?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Menene Allah ya Nufa ga Duniya?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 11/1 p. 4

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | WANE SAƘO NE KE LITTAFI MAI TSARKI?

Ta Yaya Muka Soma Wanzuwa?

A taƙaice, littafi na farko a cikin Littafi Mai Tsarki wato, Farawa ya bayyana yadda sararin samaniya ya soma wanzuwa. Ya ce: “A cikin farko Allah ya halici sama da ƙasa.” (Farawa 1:1) Allah ya halicci mutane na farko, wato, Adamu da Hawwa’u bayan halittar tsiro da itatuwa da kuma dabbobi. ’Yan Adam sun bambanta da dabbobi domin suna da halaye irin na Allah, har da ’yancin yin zaɓi. Saboda haka, za su fuskanci sakamakon duk abin da suka yi. Idan suka bi umurnin Allah, za su iya cika nufinsa ta wajen zama iyaye na farko da za su yi rayuwa a matsayin kamiltattu cikin salama har abada.

Amma, wani mala’ika ya soma kasancewa da mugun buri, sai ya yi amfani da waɗannan mutanen wajen cim ma burinsa. Shi ya sa aka ba shi suna Shaiɗan, wanda yake nufin “Ɗan tawaye.” Shaiɗan ya yi amfani da maciji wajen yaudarar Hawwa’u kuma ya gaya mata cewa ba ta bukatar ja-gorancin Allah. Adamu da Hawwa’u sun yi biyayya da Shaiɗan kuma hakan ya sa suka ɓata dangantakarsu da Mahaliccinsu. Mummunan zaɓi da iyayenmu na farko suka yi ya sa sun yi hasarar rai madawwami kuma sun jawo mana zunubi da ajizanci da kuma mutuwa, wadda ta zama rigar kowa.

Nan da nan Allah ya sanar cewa zai magance wannan yanayin kuma ya yi wa ’yan Adam hanyar samun rai na har abada. Allah ya annabta cewa wata “zuriya” wato, wani mutum mai girma zai halaka Shaiɗan kuma ya kawar da wahalar da Shaiɗan da kuma Adamu da Hawwa’u suka ɓaro. (Farawa 3:15) Wane ne zai zama wannan ‘zuriyar’? Bari mu gani.

Amma kafin wannan zuriyar ta bayyana, Shaiɗan ya yi ƙoƙarin birkitar da nufin Allah. Zunubi da mugunta sun yaɗu ko’ina a duniya. Allah ya tsai da shawara cewa zai halaka masu mugunta da rigyawa. Ya umurci adalin nan Nuhu ya gina wani jirgi kamar babban akwatin da ba zai nitse ba, don ya ceci kansa da iyalinsa da kuma dabbobin da Allah ya umurce shi ya shigar da su cikin jirgin.

Shekara ɗaya bayan somawar Rigyawar, Nuhu da iyalinsa suka fito daga jirgin kuma suka zauna a cikin duniya da aka tsabtace daga mugunta. Amma, ‘zuriyar’ ba ta bayyana ba tukun.

​—Bisa ga abin da ke littafin Farawa surori 1-11; Yahuda ayoyi 6, 14, 15; Ru’ya ta Yohanna 12:9.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba