Sashe 2
Aljannar da Aka Rasa
Wani mala’ika ɗan tawaye ya rinjayi mace da namiji na farko, Adamu da Hauwa’u su ƙi sarautar Allah. A sakamakon haka, zunubi da mutuwa suka addabi ’yan adam
TUN da daɗewa kafin a halicci mutane, Allah ya halicci halittun ruhohi masu yawa, wato, mala’iku. A lambun Adnin, wani mala’ika ɗan tawaye, wanda ya zama Shaiɗan Iblis, ya jarraba Hauwa’u cikin dabara don ta ci ’ya’yan itacen da Allah ya hana.
Ta wajen yin magana ta hanyar maciji, Shaiɗan ya faɗi cewa Allah yana hana matar da mijinta wani abu mai kyau. Mala’ikan ya gaya wa Hauwa’u cewa ita da mijinta ba za su mutu ba idan suka ci ’ya’yan itacen da aka hana. Da haka, Shaiɗan ya zargi Allah cewa Yana yi wa ’ya’yansa ’yan adam ƙarya. Mai Ruɗin ya gabatar da rashin biyayya ga Allah a matsayin tafarki mai kyau da zai kai ga wayewa da kuma ’yanci. Amma, hakan ƙarya ne, kuma shi ne ƙarya na farko da aka fara yi a duniya. Ainihin batun da hakan ya ƙunsa shi ne ikon mallaka na Allah, ko kuwa yin sarautar dukan duniya, wato, ko Allah yana da ikon yin sarauta da kuma ko yana amfani da ikonsa cikin adalci don talakawansa su amfana sosai.
Hauwa’u ta yarda da ƙaryar da Shaiɗan ya yi. Ta soma sha’awar ’ya’yan itacen, kuma daga baya ta ci daga ciki. Bayan haka, ta ba mijinta, kuma ya ci. Da haka, suka zama masu zunubi. Wannan abin da suka yi alama ce na tawaye. Ta wajen yin rashin biyayya ga dokar Allah da gangan, Adamu da Hauwa’u sun ƙi sarautar Mahalicci wanda ya ba su komi, har da kamiltaccen rai.
Allah ya yi wa ’yan tawayen hukunci domin abubuwan da suka aikata. Ya annabta zuwan Iri da aka alkawarinsa, ko Mai Ceto, wanda zai halaka Shaiɗan, da maciji ya wakilta. Allah bai halaka Adamu da Hauwa’u nan da nan ba, ta hakan, ya nuna tausayi ga yaran da ba su haifa ba. Waɗannan yaran za su kasance da bege domin Wanda Allah zai aiko zai kawar da sakamako marar kyau da ya samo asali daga Adnin. Yayin da aka ci gaba da rubuta Littafi Mai Tsarki, an bayyana a hankali yadda za a cika nufin Allah game da Mai Ceto da zai zo a nan gaba da kuma Wanda za a aiko.
Allah ya kori Adamu da Hauwa’u daga Aljannar. Za su yi aiki tuƙuru da jiɓi don su tallafa wa kansu ta wajen yin shuka a waje da lambun Adnin. Bayan haka, Hauwa’u ta yi ciki kuma ta haifi Kayinu, wanda shi ne ɗan fari na Adamu da Hauwa’u. Ma’auratan sun haifi yara maza da mata, har da Habila da Shitu, kakan-kakan Nuhu.
—An ɗauko daga Farawa surori 3 zuwa 5; Ru’ya ta Yohanna 12:9.
◼ Wace ƙarya ce ta farko, kuma wanene ya yi ta?
◼ Ta yaya ne Adamu da Hauwa’u suka yi hasarar Aljanna?
◼ Sa’ad da yake yi wa ’yan tawayen hukunci domin abubuwan da suka aikata, wane bege ne Allah ya yi tanadinsa?
[Bayanin da ke shafi na 5]
Zuriyar “za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.”—Farawa 3:15
[Akwati a shafi na 5]
AJIZANCI DA MUTUWA
Allah ya halicci Adamu da Hauwa’u a matsayin kamiltattu, da begen cewa za su rayu har abada a Aljanna. Sun yi zunubi sa’ad da suka yi tawaye ga Allah. Da haka, Adamu da Hauwa’u suka zama ajizai kuma suka ɓata dangantakarsu da Tushen rai, Jehobah. Tun daga wannan lokacin, su da dukan zuriyarsu ajizai sun kasa guje wa zunubi da mutuwa.—Romawa 5:12.
[Taswira a shafi na 5]
Farawa ●
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna