Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 3 p. 14-p. 15 par. 3
  • Adamu da Hauwa’u Sun Ki Bin Dokar Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Adamu da Hauwa’u Sun Ki Bin Dokar Allah
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Abin Da Ya Sa Suka Yi Rashin Gidansu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Wasu Sun Fi Mu Matsayi
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • An Fara Rayuwa Mai Wuya
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 3 p. 14-p. 15 par. 3
Adamu da Hauwa’u sun fita daga lambun Adnin

DARASI NA 3

Adamu da Hauwa’u Sun Ƙi Bin Dokar Allah

Adamu ya rike ʼya’yan itacen da Hauwa’u ta ba shi

Wata rana, Adamu ba ya nan, sai wani maciji ya yi wa matarsa Hauwa’u tambaya. Ya ce: ‘Gaskiya ne cewa Allah ya ce kada ku ci daga dukan ’ya’yan itacen da ke wannan lambun?’ Sai Hauwa’u ta ce: ‘Guda ɗaya ne kawai ya ce kada mu ci. Ya ce idan mun ci ’yaʼyan itacen, za mu mutu.’ Sai macijin ya ce: ‘Ba za ku mutu ba. Idan kuka ci, za ku zama kamar Allah.’ Shin abin da ya ce gaskiya ne? A’a, ƙarya ce. Amma Hauwa’u ta yarda da ƙaryar. Sai ta soma kwaɗayin ’ya’yan itacen. Bayan haka, sai ta tsinka ta ci kuma ta ba Adamu. Adamu ya san cewa idan sun ƙi bin dokar Allah, za su mutu. Duk da haka, ya ci ’ya’yan itacen.

Yayin da Adamu da Hauwa’u suke fita daga lambun Adnin, mala’iku da takobin wuta suna tsaron kofar shigan lambun

Bayan haka, sai Jehobah ya yi magana da Adamu da Hauwa’u. Ya tambaye su dalilin da ya sa suka ƙi bin dokarsa. Hauwa’u ta ɗora wa macijin laifi, Adamu kuma ya ɗora wa Hauwa’u. Jehobah ya fitar da Adamu da Hauwa’u daga lambun domin sun ƙi bin dokarsa. Sai Jehobah ya ajiye mala’iku da wani dogon wuƙa mai wuta a ƙofar lambun domin kada su sake komawa.

Jehobah ya ce zai yi wa mala’ikan da ya yi wa Hauwa’u ƙarya horo. Ba maciji ba ne ya yi wa Hauwa’u magana ba. Jehobah bai yi macizai su riƙa magana ba. Amma wani mugun mala’ika ne ya sa macijin ya yi magana. Ya yi hakan ne don ya ruɗi Hauwa’u. Sunan mala’ikan shi ne Shaiɗan. Jehobah zai halaka Shaiɗan a nan gaba don kada ya ci gaba da ruɗin mutane.

Shaiɗan ‘mai kashe mutane ne tun daga farko, bai tsaya a kan gaskiya ba, domin babu gaskiya a cikinsa.’​—Yohanna 8:44

Tambayoyi: Me ya sa Hauwa’u ta ci ’ya’yan itacen? Me ya faru sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka ƙi bin dokar Jehobah? Wane ne Shaiɗan Iblis?

Farawa 3:​1-24; Yohanna 8:44; 1 Yohanna 3:8; Ru’ya ta Yohanna 12:9

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba