KA SANI?
Mene ne bayi suke fuskanta a ƙasar Roma ta dā?
A zamanin dā, mutane da yawa sun zama bayi a Daular Roma bayan an ci su da yaƙi ko kuma an sace su. Ana sayar da duk waɗanda aka kwasa kuma ba sa sake ganin gidajensu ko kuma iyalansu.
Bayi da yawa sukan mutu a bakin haƙar ma’adinai, amma waɗanda aka ɗauke su noma da kuma aikace-aikacen gida ba sa cika shan wahala sosai. Ana saka wa bawa abin wuyar ƙarfe da ba zai iya cirewa ba, kuma a jikin abin wuyar ana rubuta ladan da za a ba duk wanda ya maido shi ga ubangijinsa idan ya gudu. Duk bawan da ya yi ƙoƙarin gudu sau da sau kuma aka kama shi, akan rubuta harafin nan F a goshinsa, wanda ke wakiltar fugitivus, wato maguji ke nan.
Littafin Filimon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya bayyana yadda manzo Bulus ya mayar ma Filimon bawansa Unisimus, wanda ya gudu. Filimon yana da izini ya hukunta Unisimus, amma Bulus ya gaya wa Filimon cewa ya “karɓe shi” hannu bibbiyu bisa ga ƙauna da kuma mutunci da ke tsakaninsu.—Filimon 10, 11, 15-18.
Me ya sa ƙasar Finikiya ta yi suna sosai da rinarta?
Ƙasar Lebanon na yanzu ita ce ƙasar Finikiya a dā, kuma an san ta sosai da yin rina mai launin shuni. Wannan rinar ta samo asali ne daga birnin Taya da ke ƙasar. Sarki Sulemanu na ƙasar Isra’ila ta dā ya ƙawata haikalin da ya gina da ‘shunayyar’ ulu da wani gwanin maɗinki daga birnin Taya ya yi.—2 Labarbaru 2:13, 14.
Shunin birnin Taya shi ne mafi tasiri a zamaninsa. Wani dalilin hakan shi ne yawan aikin da ake yi kafin a samo shi. Da farko, masu kamun kifi za su tara wani irin dodon-koɗia da yawa daga teku. Ana bukatar dodon-koɗin kamar guda 12,000 kafin a sami shunin rine tufa ɗaya. Bayan hakan, ana ƙwaƙule koɗin domin a cire sassansu da ke ɗauke da rinar. Masu yin rina suna haɗa waɗannan sassan da gishiri sa’an nan su bar haɗin ya sha iska da kuma rana na tsawon kwanaki uku. Bayan haka, suna zuba shi a cikin tukwane, su zuba ruwan teku kuma su rufe shi, sa’an nan su aza shi a kan wuta na ’yan kwanaki don ya riƙa dahuwa a hankali.
Ta kasuwancinsu da yadda suke mallakar ƙasashe, mutanen Finikiya sun ci gaba da zama na farko a cikin masu yi da kuma sayar da shunin Taya. Ana iya samun sauran rinar nan daga wajajen Bahar Maliya har birnin Cádiz, a Sifen.
a Tsawon dodon koɗin yana kai inci biyu zuwa uku.