TATTAUNAWA TSAKANIN SHAIDUN JEHOBAH DA MUTANE
Shaidun Jehobah Sun Yi Imani da Yesu Kuwa?
Tattaunawar da ke gaba misali ne na yadda Shaidun Jehobah suke yi wa mutane wa’azi. A ce wani Mashaidi mai suna Anthony ya ziyarci wani mutum mai suna Tim.
YIN IMANI DA YESU YANA DA MUHIMMANCI
Anthony: Barka da sake saduwa, malam Tim.
Tim: Yawwa, barka da zuwa.
Anthony: Na kawo maka mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! na kwanan nan. Na san za ka ji daɗin karanta su sosai.
Tim: Na gode. Na yi murna da zuwanka domin ina da wata tambaya da nake so in yi maka.
Anthony: Mece ce tambayar?
Tim: Akwai ran da nake magana da abokin aikina kuma na gaya masa cewa akwai wasu takardu masu ban sha’awa da kuke rarrabawa. Amma ya ce mini kada in karanta su domin Shaidun Jehobah ba su yi imani da Yesu ba. Na gaya masa cewa zan tambaye ka idan ka sake zuwa. Gaskiya ne cewa ba ku gaskata da Yesu ba?
Anthony: Na ji daɗin wannan tambayar da ka yi mini. Ai, idan mutum yana so ya san gaskiyar abin da wani ya yi imani da shi, zai fi dacewa ya tambayi mutumin, ko ba haka ba?
Tim: Haka ne, ai shi ya sa na tambaye ka.
Anthony: A gaskiya, Shaidun Jehobah sun yi imani da Yesu Kristi sosai. Kai, mun ma san cewa wajibi ne mutum ya yi imani da Yesu idan yana so ya sami ceto.
Tim: Na san cewa abin da kuka gaskata ke nan, amma sa’ad da abokin aikina ya ce ba ku yi imani da Yesu ba, sai na so in san ko hakan gaskiya ne. Ƙila domin ba mu taɓa tattauna wannan batun ba ne.
Anthony: To bari ma in nuna maka wasu ayoyi a cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna muhimmancin ba da gaskiya ga Yesu. Waɗannan ayoyin ne Shaidun Jehobah suke yawan amfani da su sa’ad da suke wa’azi.
Tim: To.
Anthony: Bari mu soma da abin da Yesu da kansa ya faɗa a littafin Yohanna 14:6. Yesu ya furta waɗannan kalmomin ne sa’ad da yake magana da ɗaya daga cikin manzanninsa. Wurin ya ce: “Yesu ya ce masa, Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai zuwa wurin Uban sai ta wurina.” Bisa ga wannan ayar, ta wace hanya ce kaɗai za mu iya zuwa wurin Uba?
Tim: Ta wurin Yesu.
Anthony: Haka ne. Kuma abin da Shaidun Jehobah suka yi imani da shi ke nan. Bari in tambaye ka: Bisa ga yadda ka fahimci farillan Allah, a cikin sunan waye ne ya kamata mutum ya yi addu’a?
Tim: A cikin sunan Yesu.
Anthony: Na yarda da kai. Shi ya sa duk wata addu’a da na yi da kai, ina yinta ne a cikin sunan Yesu. Haka ma yake da addu’o’in da dukan Shaidun Jehobah suke yi.
Tim: A gaskiya, na yi murnar jin haka.
Anthony: Wani nassi kuma da zai taimaka mana shi ne Yohanna 3:16. Saboda muhimmancin wannan ayar, mutane suna kiranta Linjila a taƙaice. Ma’ana, wannan ayar ce ta bayyana dukan abubuwa da aka rubuta game da rayuwar Yesu da kuma hidimarsa a nan duniya. Zan so ka karanta ayar.
Tim: To. Ta ce: “Gama Allah ya yi ƙaunar duniya har ya ba da Ɗansa [‘makaɗaici,’ Littafi Mai Tsarki] domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.”
Anthony: Na gode. Ka san wannan ayar sosai ko?
Tim: E. Ana yawan ambata ta a cocinmu.
Anthony: Hakika, nassin nan sananne ne. Bari mu sake la’akari da abin da Yesu ya faɗa a wurin. Ya ce ƙaunar Allah ga ’yan Adam ta buɗe musu hanyar samun rai madawwami. Amma mene ne ya wajaba su yi kafin su sami rai ɗin?
Tim: Wajibi ne su ba da gaskiya.
Anthony: Tabbas. Musamman ma, idan sun ba da gaskiya ga Ɗansa makaɗaici, wato, Yesu Kristi. Kuma an bayyana wannan batun samun rai madawwami ta hanyar ba da gaskiya ga Yesu a shafi na 2 a cikin wannan mujallar da na kawo maka. A cikin manufar mujallar Hasumiyar Tsaro, an bayyana cewa mujallar “tana sa a ba da gaskiya ga Yesu Kristi, wanda ya mutu domin mu sami rai madawwami kuma wanda a yanzu shi ne Sarkin Mulkin Allah.”
Tim: Ashe, akwai tabbaci a cikin mujallunku da ya nuna cewa Shaidun Jehobah suna imani da Yesu.
Anthony: Haka.
Tim: To, me ya sa mutane suke cewa ba ku yi imani da Yesu ba?
Anthony: Akwai dalilai da yawa da suke sa mutane su faɗi hakan. A wasu lokatai, mutane sukan faɗi hakan ne domin sun ji wasu sun faɗa. A wasu lokatan kuma, limamansu ne suka koya musu wannan ƙaryar.
Tim: A ganina, wataƙila mutane suna cewa ba ku yi imani da Yesu ba domin kuna kiran kanku Shaidun Jehobah, maimakon Shaidun Yesu.
Anthony: E, yana iya zama haka.
Tim: To me ya sa kuke yawan magana game da Jehobah haka?
“NA . . . SANAR MUSU DA SUNANKA”
Anthony: Mun san cewa yana da muhimmanci sosai mu yi amfani da sunan Allah, wato, Jehobah, kamar yadda Ɗansa Yesu ya yi. Dalilin kuwa shi ne abin da Yesu ya faɗa sa’ad da yake addu’a ga Ubansa. An rubuta addu’ar a Yohanna 17:26. Don Allah ka karanta mana ayar.
Tim: To. Ayar ta ce: “Na kuma sanar musu da sunanka, zan kuma sanar da shi; domin wannan ƙauna wadda ka ƙaunace ni da ita ta zauna cikinsu, ni kuma a cikinsu.”
Anthony: Na gode. Ka lura cewa Yesu ya ce ya sanar da sunan Allah. Me ya sa kake ganin ya yi hakan?
Tim: Hmm. Gaskiya ban sani ba.
Wajibi ne mu ba da gaskiya ga Yesu idan muna so mu sami ceto
Anthony: To bari mu sake karanta wani nassi da ya ba da ƙarin haske a kan wannan batun. Nassin shi ne Ayyukan Manzanni 2:21, kuma ya ce: ‘Dukan wanda ya yi kira bisa sunan Ubangiji [“Jehobah,” New World Translation] zai tsira.’ Na san za ka yarda cewa idan kira bisa sunan nan Jehobah, babban farilla ce don samun ceto, babu shakka Yesu ya san da wannan farillar.
Tim: E, gaskiyar ka.
Anthony: Saboda haka, Yesu yana so mabiyansa su sani kuma su yi amfani da sunan Allah, domin yana so su sami ceto. Kuma wannan yana ɗaya daga cikin muhimman dalilan da suka sa muke yawan magana game da Jehobah. Muna ganin yana da muhimmanci sosai mu sanar da sunan Allah, kuma mu taimaka wa mutane su kira bisa sunansa.
Tim: Amma, ko da mutane ba su san sunan Allah ba ko kuma ba su yi amfani da shi kai tsaye ba, sun san wanda suke zancensa a duk lokacin da suka ambata Allah.
Anthony: Ko da hakan gaskiya ne, yadda Allah ya gaya mana sunansa ya sa ya yi mana sauƙi mu kusace shi.
Tim: Me kake nufi?
Anthony: Ka yi tunanin wannan: Ba wajibi ba ne mu san sunan Musa. Za mu iya kiransa mutumin da ya raba Jar Teku ko kuma wanda ya karɓi Dokoki Goma kawai. Hakazalika, ba wajibi ba ne mu san sunan Nuhu. Da za mu iya kiransa mutumin da ya gina jirgi don ya ceci iyalinsa da kuma dabbobi. Haka ma yake da Yesu Kristi. Za mu iya kiransa mutumin da ya sauko daga sama kuma ya mutu domin zunubanmu kawai, ko ba haka ba?
Tim: E fa.
Anthony: Amma Allah ya sa mun san sunayen waɗannan mutanen. Sanin sunayen mutane yana sa mu san cewa labarinsu ba tatsuniya ba ce. Ko da yake ba mu taɓa haɗuwa da Musa ko Nuhu ko kuma Yesu ba, sanin sunayensu ya ƙara mana tabbaci cewa mutanen nan sun rayu da gaske.
Tim: Ban taɓa tunani a kan wannan bayanin ba, amma a gaskiya, na gamsu.
Anthony: Wannan shi ne dalili na biyu da ya sa Shaidun Jehobah suke yawan amfani da sunan Allah. Muna so mu taimaka wa mutane su gaskata cewa Jehobah yana wanzuwa da gaske kuma za su iya kusantar sa. Amma kuma muna taimaka wa mutane su fahimci cewa Yesu yana taka muhimmiyar rawa a batun cetonmu. Bari mu sake karanta wani nassi domin mu tabbatar da wannan bayani.
Tim: Da kyau.
Anthony: Da farko mun karanta Yohanna 14:6. Ka tuna cewa Yesu ya ce ‘shi ne hanya, shi ne gaskiya, shi ne rai.’ Bari mu ga abin da ya faɗa a Yohanna 14:1. Don Allah ka karanta abin da Yesu ya faɗa a ƙarshen wannan ayar.
Tim: To. Wurin ya ce: ‘Ku ba da gaskiya ga Allah, ku ba da gaskiya gare ni kuma.’
Anthony: Na gode. Kana ganin imani na gaske batun ba da gaskiya ga wanda muka ga dama ne tsakanin Yesu da kuma Jehobah?
Tim: A’a. Yesu ya ce wajibi ne mu ba da gaskiya ga su biyun.
Anthony: Haka ne. Kuma na san za ka yarda da ni cewa ba faɗa da baki kawai cewa muna ba da gaskiya ga Allah da kuma Yesu ne yake da muhimmanci ba. Hakika, muna bukata mu yi rayuwar da za ta nuna cewa mun ba da gaskiya gare su.
Tim: Tabbas.
Anthony: Amma, ta yaya ne mutum zai iya nuna cewa yana ba da gaskiya ga Allah da kuma Yesu? Za mu tattauna wannan batun a wani lokaci dabam.a
Tim: Da kyau. Ina sauraron dawowarka.
Ka taɓa tunanin wani abu da za ka so ka sami ƙarin bayani a kai daga cikin Littafi Mai Tsarki? Za ka so ka ƙara sanin wasu daga cikin koyarwar Shaidun Jehobah ko kuma dalilin da ya sa suka yi imani da wasu abubuwa? Idan kana so, ka sami Shaidun Jehobah don su bayyana maka waɗannan batutuwan. Za su yi farin cikin tattaunawa da kai.
a Don ƙarin bayani, ka duba babi na 12 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.