Mene Ne Zai Faru da Kakannina da Suka Mutu?
SHEKARUN baya, wata jaridar ƙasar Koriya, wato Chosun Ilbo ta ɗauki wannan kan labari mai ƙayatarwa: “‘Shim Cheong Mace Mai Kirki,’ Wadda Ta Rasu Ba Ta San Yesu Ba Ta Shiga Gidan Wuta Ne?”
Wannan kan labarin ya ta da hankalin mutane domin Shim Cheong ƙaunatacciyar mace ce a wata tatsuniyar ƙasar Koriya, wadda ta sadaukar da ranta wajen kula da mahaifinta makaho. An yi shekaru ana yaba mata. A ƙasar Koriya ma, ana ɗaukan Shim Cheong a matsayin yarinya mai kyan tarbiyya da ya kamata a yi koyi da ita.
Saboda haka, mutane da yawa suna ganin rashin adalci ne a ce irin wannan yarinyar ta shiga gidan wuta don kawai ba ta yi baftisma a matsayin Kirista ba, kuma ba sa farin cikin jin hakan. Ballantana ma, ana ganin kamar wannan tatsuniyar ta faru ne shekaru da yawa kafin mutanen ƙauyenta su ji bishara game da Kristi.
Wannan talifin ya ɗauki ganawa da aka yi da wani limami. An tambaye shi ko dukan waɗanda suka mutu ba su san Yesu ba za su shiga gidan wuta. Sai ya ce: “Ba mu sani ba. Mu dai muna zato cewa Allah ya san yadda zai hukunta [irin waɗannan mutanen].”
SHIN SAI DA HAKAN MUTUM ZAI SAMI CETO?
Littafin nan The New Catholic Encyclopedia ya ce: “Wajibi ne mutum ya yi baftisma kafin ya sami ceto. Kamar yadda Kristi kansa ya faɗa, in ba an sake haifan mutum ta ruwa da Ruhu Mai Tsarki ba, ba zai shiga Mulkin Allah ba (Yh. 3.5).” Hakan ne ya sa wasu mutane suka gaskata cewa ana jefa dukan waɗanda suka mutu ba su yi baftisma ba a gidan wuta ko kuma a azabtar da su a wata hanya dabam.
Duk da haka, akwai mutane da yawa da ba su amince da wannan koyarwar ba. Miliyoyin mutane sun mutu ba tare da sanin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ba. Shin zai dace a azabtar da su har abada? Mece ce koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan wannan batun?
BEGEN DA KE CIKIN LITTAFI MAI TSARKI
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ba ya yin banza da mutanen da suka mutu ba tare da sanin farillansa ba. Littafin Ayyukan Manzanni 17:30 ya ba da tabbaci cewa: ‘Kwanakin jahilci fa Allah ya yi biris da su.’ To, mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru da waɗanda suka mutu da ba su sami damar sanin Allah ba?
Amsar wannan tambayar na cikin abin da Yesu ya faɗa ma wani ɓarawo da aka kashe su tare. Ɓarawon ya gaya wa Yesu cewa: “Ka tuna da ni lokacinda ka shiga mulkinka.” Sai Yesu ya amsa masa, za ka kasance “tare da ni cikin Aljanna.”—Luka 23:39-43.
Shin Yesu yana masa alkawarin zuwa sama ne? A’a. Domin wajibi ne a ‘sāke haifan’ mutum ta ruwa da ruhu kafin ya shiga Mulkin sama, amma hakan bai faru da wannan ɓarawon ba tukun. (Yohanna 3:3-6, Littafi Mai Tsarki) A maimakon hakan, Yesu yana yi ma wannan ɓarawon alkawari ne cewa zai sake rayuwa cikin Aljanna. Tun da yake mutumin Bayahude ne, mai yiwuwa ya san da labarin lambun Adnin da ke cikin littafi na farko a cikin Littafi Mai Tsarki. (Farawa 2:8) Alkawarin Yesu ya sa ya kasance da begen tashin matattu da kuma rayuwa a lokacin da za a mai da duniya Aljanna.
Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa za a yi “tashin matattu, na masu adalci da na marasa adalci.” (Ayyukan Manzanni 24:15) “Marasa adalci” su ne waɗanda ba su bi mizanan Allah ba domin ba su san waɗannan mizanan ba. Yesu zai ta da wannan ɓarawo marar adalci da kuma biliyoyin mutane da suka mutu cikin jahilci. Sa’an nan a cikin Aljanna, za a koya musu mizanan Allah kuma hakan zai ba su damar nuna ƙaunarsu ga Allah ta wajen bin dokokinsa.
BAYAN AN TA DA MARASA ADALCI
Sa’ad da aka ta da marasa adalci, shin za a yi musu shari’a bisa ga ayyukan da suka yi kafin su mutu ne? A’a. Littafin Romawa 6:7 ya ce: “Wanda ya mutu ya kuɓuta daga zunubi.” Mutuwar da marasa adalci suka yi a bakin zunubansu ne. Saboda haka, za a yi musu shari’a bisa ga ayyukansu bayan an ta da su daga mutuwa ne, ba bisa ga ayyukansu kafin mutuwarsu ba. Ta yaya hakan zai amfane su?
Bayan tashin matattu, marasa adalci za su sami zarafin koyon dokokin Allah, waɗanda za su bayyana sa’ad da aka buɗe littattafai na alama. Bayan haka, za a yi musu shari’a “gwargwadon ayyukansu,” wato bisa ga matakin da suka ɗauka bayan sun koyi dokokin Allah. (Ru’ya ta Yohanna 20:12, 13) Wannan ne zai zama dama na farko da marasa adalci da yawa za su samu na sani da kuma yin nufin Allah don su rayu har abada a duniya.
Wannan koyarwar Littafi Mai Tsarki ta taimaki mutane da yawa su sake yin imani da Allah. Wata da aka taimake ta ta sake yin imani da Allah ita ce, Sug Yeong. Iyayenta sun tarbiyyartar da ita a cikin koyarwar Katolika. Wasu a cikin iyalinta firistoci ne. Tun da yake ta so ta yi hidimar coci a matsayin nun, sai ta ƙaura zuwa gidan da masu irin wannan hidimar suke zama. Daga baya, ta bar wurin domin wasu abubuwa da ake yi a wurin da ba su dace ba. Ƙari ga haka, ba ta amince da koyarwar wutar jahannama ba domin a ganinta azabtar da mutane a cikin wuta har abada ba adalci ba ne.
Wata rana, wata Mashaidiyar Jehobah ta karanta wa Sug Yeong wannan ayar a cikin Littafi Mai Tsarki: “Gama masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba, ba su kuwa da sauran lada; gama ba a ƙara tuna da su ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Mashaidiyar ta taimaka wa Sug Yeong ta fahimci cewa kakanninta da suka rasu ba sa shan azaba a cikin jahannama. A maimakon haka, suna jiran ranar da za a ta da su.
Sug Yeong ta san cewa mutane da yawa ba su taɓa jin ainihin koyarwar Littafi Mai Tsarki ba, saboda haka, ta ƙudura ta bi umurnin Yesu da ke littafin Matta 24:14, cewa: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” A yanzu, tana yin wa’azin bishara kuma tana gaya wa mutane begen da ta koya a cikin Littafi Mai Tsarki.
“ALLAH BA MAI-TARA BA NE”
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.” (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Ba abin mamaki ba ne cewa Allah zai nuna adalci ga dukan mutane, domin shi mai “ƙaunar adalci da kuma shari’a” ne.—Zabura 33:5.