Allah Yana Lura Da Kai Kuwa?
“Ni matalauci ne, mai-talauci; duk da haka Ubangiji yana tuna da ni.”—Zabura 40:17; DAUDA NA ISRA’ILA, ƘARNI NA 11 KAFIN ZAMANINMU.
Shin wauta ce da Dauda ya sa rai cewa Allah zai kula da shi? Allah yana lura da kai kuwa? Mutane da yawa ba su ba da gaskiya cewa akwai Allah maɗaukaki da yake lura da su ba. Me ya sa?
Wani dalilin shi ne cewa Allah ya fi ’yan Adam girma sosai. A gaban Allah, al’ummai gaba ɗaya ‘suna kama da ɗigon ruwa cikin guga’ da kuma “ƙura mai-labshi a bisa mizani.” (Ishaya 40:15) Wani marubuci da bai gaskata da Allah ba, ya ce “girman kai ne sosai mutum ya gaskata cewa akwai Allah da yake lura da abin da kowane mutum yake yi.”
Wasu kuma suna ganin ba su cancanci Allah ya lura da su ba domin halinsu. Alal misali, wani mutum mai suna Jim ya ce: “Nakan yi addu’a a kai a kai don in sami kwanciyar hankali da kuma kamun kai, amma kafin ka ce kwabo, na soma fushi. Hakan ya sa na gaya wa kaina cewa tsabar muguntata ne ya sa Allah ya ƙi ya taimaka mini.”
Shin Allah ya yi nisa da ’yan Adam sosai ne da ba zai san cewa muna wanzuwa ba? Mene ne ra’ayinsa game da halittunsa ajizai? Babu ɗan Adam da zai iya sanin amsoshin waɗannan tambayoyin idan Allah bai bayyana su ba. Amma Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da cewa Allah bai yi nisa da mutane har da ba zai iya lura da su ba. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.” (Ayyukan Manzanni 17:27) A cikin talifofi huɗu da ke biye, za mu tattauna kalmomin Allah da suka nuna cewa ya damu da mutane kuma yana lura da mutane kamar kai.