Allah Yana So Ka Ƙulla Dangantaka Da Shi
“Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.”—YOHANNA 6:44.
ABIN DA KE SA WASU SHAKKA: Mutane da yawa da suka yi imani da Allah suna ganin ba zai yiwu su kusace shi ba. Christina, ’yar ƙasar Ireland, wadda ke halartan coci kowane mako a dā ta ce: “Ni dai ina ɗaukan Allah a matsayin mahaliccin kome kawai.” Ta daɗa da cewa: “Amma ban san shi ba kuma ban taɓa jin zan iya kusantarsa ba.”
ABIN DA KALMAR ALLAH TA CE: Ko da muna ji kamar mun gama yawo, Jehobah ba ya fid da rai a kanmu. Don ya nuna yadda Allah yake kula da mu, Yesu ya ba da kwatancin nan: “Idan mutum yana da tumaki ɗari, ɗaya a cikinsu ta ɓace, ba sai shi bar tassain da taran nan ba, shi tafi wurin duwatsu, shi nemi wadda ta ɓace?” Wane darasi ne hakan ya koyar? Yesu ya ce: “Hakanan kuma ba nufin Ubanku wanda ke cikin sama ba ne, guda ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.”—Matta 18:12-14.
Allah yana ɗaukan kowanne “cikin waɗannan ƙanƙanana” da tamani. Ta yaya Allah yake neman wanda ya soma ‘ɓacewa’? Nassi na farko a wannan talifin ya nuna cewa Jehobah ne ke jawo mutane wurinsa.
Ka yi la’akari da yadda Jehobah da kansa ya jawo masu gaskiya. A ƙarni na farko a zamaninmu, Allah ya tura wani almajiri Kirista mai suna Filibus wurin wani ma’aikacin Habasha da ke tafiya a karusarsa domin ya bayyana ma’anar annabcin Littafi Mai Tsarki da ma’aikacin yake karantawa. (Ayyukan Manzanni 8:26-39) Daga baya, Allah ya umurci manzo Bitrus ya je gidan wani jarumin sojan Roma, wanda ya daɗe yana addu’a da kuma ƙoƙarin bauta wa Allah. (Ayyukan Manzanni 10:1-48) Allah ya kuma sa manzo Bulus da abokan wa’azinsa su je wani kogi a bayan garin Filibi. A wurin suka tarar da Lidiya, wata “mai-sujjada ga Allah” kuma “Ubangiji kuwa ya buɗe zuciyarta,” don ta ji ‘abin da Bulus yake faɗi.’—Ayyukan Manzanni 16:9-15.
A waɗannan labaran, mun ga yadda Jehobah ya tabbata cewa waɗanda suke biɗarsa sun sami damar saninsa. A yau, su wa suke bin mutane gida-gida da kuma inda akwai jama’a don su sanar da saƙon Littafi Mai Tsarki game da Allah? Mutane da yawa za su ce “Shaidun Jehobah ne.” Ka tambayi kanka, ‘Ko su ne mutanen da Allah yake aikawa su taimaka mini in ƙulla abota da shi?’ Muna ƙarfafa ka ka roƙi Allah ya taimake ka ka kusace shi.a
a Don ƙarin bayani, ka kalli bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? a dandalin www.pr418.com/ha.