Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/1 p. 16
  • Makiyayi Mai Kula Matta 18:12-14

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Makiyayi Mai Kula Matta 18:12-14
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Inda Za Ka Sami Ta’aziyya
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Ku Taimaki Waɗanda Suka Bar Garken
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • ‘Ni da Kaina Zan Nemi Tumakina’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Yesu Yana Kula da Tumakinsa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/1 p. 16

Ka Kusaci Allah

Makiyayi Mai Kula Matta 18:12-14

‘ALLAH ya damu da ni kuwa?’ Idan ka taɓa yi wa kanka irin wannan tambayar, to ka san kuna da yawa. Yawancinmu muna fuskantar wahala da matsaloli, kuma a wani lokaci muna iya yin shakka ko Mahaliccin wannan sararin samaniya mai faɗi haka yana damuwa da mu. Muna bukatar mu sani ko, Jehobah Allah yana kula da kowannenmu ɗaɗɗaya kuwa? Sa’ad da yake duniya Yesu wanda ya fi kowa sanin Jehobah, ya ba da kwatancin da ya ba da amsa mai daɗaɗa rai ga wannan tambayar.

Ta wajen yin amfani da kwatancin yadda makiyayi yake kula da tumakinsa, Yesu ya ce: “Idan mutum yana da tumaki ɗari, ɗaya a cikinsu ta ɓace, ba sai shi bar tassain da taran nan ba, shi tafi wurin duwatsu, shi nemi wadda ta ɓace? Idan kuwa ya samu, hakika ina ce maku, murna da ya yi bisa gareta ta fi ta bisa kan tassain da taran nan waɗanda ba su ɓace ba. Hakanan kuma ba nufin Ubanku wanda ke cikin sama ba ne, guda ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.” (Matta 18:12-14) Bari mu ga yadda Yesu ya kwatanta yadda Jehobah yake kula da kowanne cikin masu bauta masa.

Makiyayi ya san yana da hakkin kula da kowanne cikin tumakinsa. Ya san kowacce tunkiyar da ta ɓace. Ya san sunan da ya ba kowacce tunkiya. (Yohanna 10:3) Makiyayi mai kula ba zai huta ba har sai ya nemo tunkiyar da ta ɓace. Sa’ad da ya tafi neman tunkiyar da ta ɓace, ba zai jefa sauran tumaki 99 a cikin haɗari ba. Makiyaya sau da yawa suna zama tare ne, kuma suna ƙyale tumakinsu su yi wasa tare.a Ta yin hakan, makiyayin da ya ɗan tafi neman tunkiyarsa da ta ɓace zai iya barin sauran tumakinsa a hannun abokansa makiyaya. Idan ya nemo tunkiyar da ta ɓace kuma ba ta ji rauni ba, makiyayin zai yi farin ciki sosai. Sa’ad da ya ɗaura tunkiyar da ta tsorata a kan kafaɗarsa zai mai da ta cikin garken inda za ta kasance cikin kāriya da kwanciyar hankali.—Luka 15:5, 6.

Ta wajen bayyana ma’anar kwatancin, Yesu ya ce Allah ba ya son “ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.” Dā ma can Yesu ya gargaɗi almajiransa kada su sa ‘guda ɗaya a cikin ƙanƙananan nan masu-bada gaskiya gareshi’ ya yi tuntuɓe. (Matta 18:6) To, menene kwatancin Yesu ya koya mana game da Jehobah? Shi Makiyayi ne da ke kula da kowanne tumakinsa, har da “ƙanƙananan” wato, waɗanda kamar ba su da muhimmanci a idanun mutanen duniya. Hakika, a idanun Allah kowanne cikin masu bauta masa yana da muhimmanci da kuma tamani.

Idan kana son a tabbatar maka cewa kana da tamani a gaban Allah, ka ƙara koya game da Makiyayi Mai Girma, Jehobah Allah, da kuma yadda za ka fi kusantarsa. Ta wajen yin hakan, za ka kasance da tabbaci kamar manzo Bitrus wanda babu shakka ya ji kwatancin Yesu na tunkiyar da ta ɓace da kunnensa. Bitrus daga baya ya rubuta: “Kuna zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.”—1 Bitrus 5:7.

[Hasiya]

a Ware tumakin ba matsala ba ce tun da yake kowacce tunkiya ta san muryar makiyayinta.—Yohanna 10:4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba