Ku Taimaki Waɗanda Suka Bar Garken
“Ku yi murna tare da ni, gama na sami tunkiyata wadda ta ɓace.”—LUKA 15:6.
1. Ta yaya ne Yesu ya nuna cewa shi makiyayi ne mai ƙauna?
AN KIRA Ɗa makaɗaici na Jehobah, Yesu Kristi, “babban makiyayin tumaki.” (Ibran. 13:20) Nassosi sun annabta zuwansa kuma sun nuna cewa shi fitaccen Makiyayi ne wanda ya zo neman “ɓatattun tumaki” na Isra’ila. (Mat. 2:1-6; 15:24) Bugu da ƙari, kamar yadda makiyayi zai iya sadaukar da ransa don ya kāre tumakinsa, Yesu ya ba da ransa a matsayin hadayar fansa don mutane masu kama da tumaki da za su amfana daga hadayarsa.—Yoh. 10:11, 15; 1 Yoh. 2:1, 2.
2. Menene wataƙila ya sa wasu Kiristoci suka daina zuwa taro?
2 Abin baƙin ciki shi ne, wasu da a dā suka nuna cewa sun san amfanin hadayar Yesu kuma suka keɓe kansu ga Allah, sun daina zuwa ikilisiyar Kirista. Sanyin gwiwa, rashin lafiya, ko wasu abubuwa dabam suna iya rage himmarsu kuma su zama marar ƙwazo. Amma fa, sai suna cikin garken Allah ne kawai za su iya more kwanciyar hankali da farin ciki da Dauda ya ambata a Zabura ta 23. Alal misali, ya rera: “Ubangiji makiyayina ne; ba zan rasa komi ba.” (Zab. 23:1) Waɗanda suke cikin garken Allah ba sa rasa komi a ruhaniyance, amma tumakin da suka bar garken ba sa shaida wannan farin cikin. Wanene zai iya taimaka musu? Ta yaya za a iya taimakawa? Menene ainihin abin da za a yi don a taimaka musu su koma cikin garken?
Wanene Zai Iya ba da Taimako?
3. Ta yaya ne Yesu ya nuna abin da ake bukata don a ceto tumakin da suka bar garken Allah?
3 Ana bukatar a ƙoƙarta sosai don a ceto tumakin da suka bar garken Allah. (Zab. 100:3) Yesu ya ba da misalin hakan sa’ad da ya ce: “Idan mutum yana da tumaki ɗari, ɗaya a cikinsu ta ɓace, ba sai shi bar tassain da taran nan ba, shi tafi wurin duwatsu, shi nemi wadda ta ɓace? Idan kuwa ya samu, hakika ina ce maku, murna da ya yi bisa gareta ta fi ta bisa kan tassain da taran nan waɗanda ba su ɓace ba. Hakanan kuma ba nufin Ubanku wanda ke cikin sama ba ne, guda ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.” (Mat. 18:12-14) Wanene zai iya taimaka wa mutane masu kama da tumaki da suka bar garken?
4, 5. Wane irin hali ne ya kamata dattawa su nuna wa tumakin Allah?
4 Idan dattawa Kiristoci suna son su taimaka wa tumakin da suka bar garke, suna bukatar su tuna cewa tumakin Allah tarin mutane ne da suka keɓe kansu ga Jehobah, wato, ƙaunatattun ‘tumakin da ke garken Allah.’ (Zab. 79:13, Littafi Mai Tsarki) Irin waɗannan ƙaunatattun tumaki suna bukatar kula sosai, kuma hakan na nufin cewa makiyaya masu ƙauna suna bukatar su nuna sun damu da su sosai. Ziyartarsu zai iya taimaka musu sosai. Ƙarfafa su da makiyayi zai yi zai iya sa su sake soma dangantaka da Jehobah kuma ya ƙara motsa muradinsu na komawa garken.—1 Kor. 8:1.
5 Masu kula da tumakin Allah suna da hakkin neman waɗanda suka bar garken Allah kuma su taimaka musu. Manzo Bulus ya tuna wa dattawa Kiristoci da ke Afisa na dā game da hakkinsu na zuwa ziyara sa’ad da ya ce: “Ku tsare kanku, da dukan garke kuma, wanda Ruhu Mai-tsarki ya sanya ku shugabannai a ciki, garin ku yi kiwon ikilisiyar Allah, wadda ya sayi da jinin kansa.” (A. M. 20:28) Hakazalika, manzo Bitrus ya ba dattawa shafaffu wannan umurnin: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, kuna yin shugabanci, ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta, amma da karsashin zuciya; ba kuwa kamar masu-nuna sarauta bisa abin kiwo da aka sanya a hannunku ba, amma kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.”—1 Bit. 5:1-3.
6. Me ya sa tumakin Allah suke bukatar samun kula daga makiyaya a yau?
6 Kiristoci makiyaya suna bukatar su yi koyi da “makiyayi mai-kyau,” Yesu. (Yoh. 10:11) Ya damu sosai da tumakin Allah kuma ya nanata muhimmancin kula da su sa’ad da ya gaya wa Siman Bitrus ya ‘zama makiyayin tumakinsa.’ (Karanta Yohanna 21:15-17.) Tumakin sun fi bukatar irin wannan kular a yau, domin Iblis ya daɗa ƙoƙarce-ƙoƙarcen da yake yi na karya amincin waɗanda suka keɓe kansu ga Allah. Shaiɗan yana amfani ne da kasawarmu na jiki da kuma duniya don ya sa tumakin Jehobah su yi ayyukan zunubi. (1 Yoh. 2:15-17; 5:19) Waɗanda suka daina zuwa taro musamman za su iya faɗawa tarkonsa da wuri, saboda haka, suna bukatar taimako don su yi amfani da umurnin nan na ‘yin tafiya bisa ga Ruhu.’ (Gal. 5:16-21, 25) Taimakawa irin waɗannan tumakin na bukatar a dogara ga Allah ta hanyar addu’a, a nemi ja-gorar ruhunsa, a kuma yi amfani da Kalmarsa yadda ya kamata.—Mis. 3:5, 6; Luk 11:13; Ibran. 4:12.
7. Me ya sa yake da muhimmanci dattawa su ziyarci masu kama da tumaki da ke ƙarƙashin kulawarsu?
7 Makiyayi a Isra’ila ta dā yana amfani ne da dogon lanƙwasashen sanda don ya yi wa tumakinsa ja-gora. Sa’ad da tumakin suke shiga ko fita daga inda suke kwana, za su bi ‘ƙarƙashin sanda’ kuma da haka, makiyayin zai iya ƙirga su. (Lev. 27:32; Mi. 2:12; 7:14) Hakazalika, Kirista makiyayi yana bukatar ya san tumakin Allah da ke ƙarƙashin kulawarsa sosai kuma ya san yanayinsu. (Gwada Misalai 27:23.) Saboda haka, yin ziyara don ƙarfafawa yana ɗaya daga cikin batutuwa masu muhimmanci da rukunin dattawa suke tattaunawa. Wannan ya haɗa da yin shiri don taimakawa tumakin da suka bar garken. Jehobah da kansa ya ce zai nemi tumakinsa kuma zai ba su kulawar da suke bukata. (Ezek. 34:11) Saboda haka, Allah yana farin ciki sa’ad da dattawa suka ɗauki irin waɗannan matakan don su taimaki tumakin da suka bijire su dawo cikin garken.
8. Ta waɗanne hanyoyi ne dattawa za su iya kula da tumaki?
8 Sa’ad da ɗan’uwa mai bi yake rashin lafiya, ziyarar da mai kula da tumakin Allah zai kai za ta iya faranta masa rai kuma ta ƙarfafa shi. Hakan zai iya kasancewa yanayin tumakin da ke rashin lafiya ta ruhaniya idan aka mai da masa hankali. Dattawa suna iya karanta nassosi, su maimaita wani talifi, su tattauna batutuwa masu muhimmanci da aka faɗa a taro, kuma su yi addu’a tare da wanda ya daina zuwa taro, da sauransu. Suna iya ambata cewa waɗanda suke cikin ikilisiya za su yi farin cikin ganin ya soma halartar taro a ikilisiya. (2 Kor. 1:3-7; Yaƙ. 5:13-15) Kai ziyara, yin waya, ko kuwa rubuta wasiƙa za su iya taimaka masa sosai! Kula da bukatun tunkiyar da ta bar garke zai iya faranta ran Kirista dattijo da ke taimakonsa.
Mu Haɗa Hannu Don Taimakawa
9, 10. Me ya sa za ka iya cewa ba dattawa kaɗai ba ne za su nuna damuwa ga tunkiyar da ta bar garke?
9 Muna zaune a lokatai masu tsanani da ke cike da harkoki, saboda haka, zai yiwu ba mu lura ba cewa ɗan’uwa mai bi ya soma barin ikilisiya. (Ibran. 2:1) Duk da haka, Jehobah yana ɗaukan tumakinsa da tamani. Kowannensu yana da amfani, kamar yadda kowanne fanni na jikin mutum yake da amfani. Saboda haka, mu duka muna bukatar mu nuna cewa mun damu da ’yan’uwanmu kuma muna kula da juna da gaske. (1 Kor. 12:25) Kana da irin wannan halin?
10 Ko da yake dattawa ne suke da ainihin hakkin nema da taimaka wa tumakin da suka bar garke, ba dattawa Kiristoci ba ne kawai za su nuna damuwa ga ’yan’uwa masu bi da suka bar garke. Sauran ’yan’uwa za su iya haɗa hannu da waɗannan dattawan. Za mu iya, kuma muna bukatar mu ƙarfafa kuma mu taimaka wa ’yan’uwanmu maza da mata da suke bukatar taimako na ruhaniya don su koma cikin garke. Ta yaya za a iya ba da wannan taimakon?
11, 12. Ta yaya za ka iya samun gatan taimaka wa waɗanda suke bukatar taimako na ruhaniya?
11 A wasu yanayi, dattawa suna iya aika ƙwararrun masu shelar Mulki su je su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da waɗanda suka daina zuwa taro da ke son a taimaka musu. Manufar wannan ƙoƙarce-ƙoƙarcen ita ce a motsa su su dawo da ‘ƙaunarsu ta fari.’ (R. Yoh. 2:1, 4) Ana iya ƙarfafa irin waɗannan ’yan’uwa masu bi a ruhaniyance ta wajen yin nazarin abubuwan da ba su sani ba tare da su sa’ad da suka daina zuwa taro.
12 Idan dattawa suka gaya maka ka yi nazari da ɗan’uwa mai bi da ke bukatar wasu taimako na ruhaniya, ka roƙi Jehobah ya yi maka ja-gora kuma ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenka. Hakika, “ka damƙa ma Ubangiji ayukanka, Nufe nufenka kuma za su tabbata.” (Mis. 16:3) Ka yi bimbini a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki da bayanai masu ƙarfafawa da za ka iya tattaunawa da waɗanda suke bukatar taimako ta ruhaniya. Ka yi tunani a kan misali mai kyau na manzo Bulus. (Karanta Romawa 1:11, 12.) Bulus yana ɗokin ganin Kiristocin da ke Roma don ya ba su wasu kyauta ta ruhaniya da za ta ƙarfafa su. Kuma yana sa ran cewa za su ƙarfafa juna. Bai kamata ba ne mu ma mu kasance da irin wannan halin sa’ad da muke son mu taimaka wa tumakin da suka bar garken Allah?
13. Menene za ka iya tattaunawa da wanda ya daina zuwa taro?
13 A lokacin da kuke tattaunawa, kana iya tambayarsa, “Ta yaya ka koyi gaskiya?” Ka taimaka masa ya tuna farin cikin da ya shaida a dā, ka ƙarfafa wanda ya daina zuwa taro ya ambata abubuwa masu kyau da ya shaida a taro, a aikin wa’azi, da kuma taron gunduma. Ka ambata abubuwa masu ban farin ciki da kuka more tare a hidimar Jehobah. Ka ambata farin cikin da ka shaida ta wajen kusantar Jehobah. (Yaƙ. 4:8) Ka ambata godiyarka game da yadda Allah yake yi mana tanadi a matsayin mutanensa, musamman ta wajen ƙarfafa mu kuma ya sa mu kasance da bege a lokacin wahala.—Rom. 15:4; 2 Kor. 1:3, 4.
14, 15. Waɗanne albarkatu da suke morewa a dā ne ya kamata mu tuna wa waɗanda suka daina zuwa taro?
14 Zai dace a tuna wa wanda ya daina zuwa taro wasu albarkatun da ya mora a dā a sakamakon tarayya na kud da kud da yake yi da ikilisiya. Alal misali, akwai albarkar samun ƙarin sani na Kalmar Allah da manufofinsa. (Mis. 4:18) A lokacin da yake ‘tafiya bisa ga ruhu,’ guje wa jarrabobin yin zunubi bai yi masa wuya ba. (Gal. 5:22-26) Kuma saboda lamiri mai kyau da yake da shi, hakan ya sa yana addu’a ga Jehobah kuma ya more ‘salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, wadda take tsare zukatanmu da tunaninmu.’ (Filib. 4:6, 7) Ka saka waɗannan batutuwa a zuciya, ka nuna kulawa sosai, kuma ko ta yaya, cikin ƙauna, ka ƙarfafa ’yan’uwanka na ruhaniya maza ko mata su dawo cikin garke.—Karanta Filibbiyawa 2:4.
15 A ce kai dattijo ne da ya kai ziyara don ƙarfafawa. Kana iya ƙarfafa ma’aurata da suka daina zuwa taro su yi tunani a kan lokacin da suka fara koyan gaskiya daga cikin Kalmar Allah. Gaskiyar tana da ban al’ajabi, ta sa sun san abin da ya kamata, ta gamsar da su, kuma ta ’yantar da su! (Yoh. 8:32) Su tuna yadda zuciyarsu ta cika da godiya domin abubuwan da suke koya game da Jehobah, ƙaunarsa, da kuma manufofinsa masu ban al’ajabi! (Gwada Luka 24:32) Ka tuna musu dangantaka ta kud da kud da Jehobah da kuma gatan yin addu’a da Kiristocin da suka keɓe kansu suke morewa. Ka ƙarfafa waɗanda suka daina zuwa taro su sake yin na’am ga “bishara ta darajar Allah mai-albarka,” Jehobah.—1 Tim. 1:11.
Ku Ci Gaba da Nuna Musu Ƙauna
16. Ka ba da misalin da ya nuna cewa ba da taimako na ruhaniya yana da amfani sosai.
16 Shawarwarin da aka ambata a baya suna aiki sosai kuwa? Ƙwarai kuwa. Alal misali, wani matashi da ya zama mai shelar Mulki yana ɗan shekara 12 ya daina zuwa taro sa’ad da ya kai ɗan shekara 15. Daga baya ya soma zuwa taro, kuma yana hidima ta cikakken lokaci fiye da shekaru 30 a yanzu. Ya soma halartan taro ne musamman domin wani dattijo Kirista da ya taimaka masa. Kuma ya nuna godiya sosai domin taimakon da dattijon ya yi masa!
17, 18. Waɗanne halaye ne za su taimake ka ka taimaki wanda ya bar garken Allah?
17 Ƙauna ce ke motsa Kiristoci su taimaki waɗanda suka bar cikin garke su dawo cikin ikilisiya. Game da mabiyansa, Yesu ya ce: “Sabuwar doka ni ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:34, 35) Hakika, ƙauna ce alamar da ke sa a gane Kiristoci na gaskiya. Bai kamata ba ne a nuna irin wannan ƙaunar ga Kiristocin da suka yi baftisma amma suka daina zuwa taro? Ƙwarai kuwa! Sa’ad da muke taimaka wa waɗanda suka daina zuwa taro, muna bukatar mu nuna halaye dabam dabam na Kirista.
18 Idan kana son ka taimaka wa wanda ya bar garken Allah, waɗanne halaye ne kake bukatar ka nuna? Bayan ƙauna, kana bukatar ka nuna juyayi, alheri, haƙuri, da jimiri. Bisa ga yanayin, wataƙila za ka bukaci ka nuna gafara. Bulus ya rubuta: “Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa; kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowanne mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku, hakanan kuma sai ku yi: gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.”—Kol. 3:12-14.
19. Me ya sa yake da amfani sosai a ƙoƙarta wajen taimaka wa masu kama da tumaki su koma cikin garken Kirista?
19 Talifi na gaba a fitowar nan, zai tattauna dalilai da suka sa wasu suke barin garken Allah. Kuma zai nuna yadda za a marabci waɗanda suka dawo. Yayin da kake nazarin wancan talifin kuma kake bimbini a kan wannan, ka tabbata cewa duk wani ƙoƙarin da ka yi don taimaka wa mutane masu kama da tumaki su dawo cikin garken Kirista zai kasance mai amfani. A wannan zamanin, mutane da yawa suna amfani da dukan lokacin da suke da shi a rayuwa wajen tara dukiya, amma rai guda ya fi dukan kuɗin da ke duniyar nan tamani. Yesu ya nanata hakan a cikin kwatancin tunkiyar da ta ɓace. (Mat. 18:12-14) Bari ka ci gaba da tuna waɗannan batutuwan yayin da kake ƙoƙartawa cikin gaggawa don taimaka wa mutanen Jehobah ƙaunatattu masu kama da tumaki da suka bar garken.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane hakki ne makiyaya Kiristoci suke da shi game da masu kama da tumaki da suka bar garke?
• Ta yaya za ka iya taimaka wa waɗanda suka daina tarayya da ikilisiya?
• Waɗanne halaye ne za su iya taimaka maka ka taimaki waɗanda suka bar garke?
[Hoto a shafi na 10]
Kiristoci makiyaya suna ƙoƙartawa cikin ƙauna don su taimaka wa waɗanda suka bar garken Allah