“Ku Yi Kiwon Garken Allah Wanda Ke Wurinku”
“Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, kuna yin shugabanci, ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai.”—1 BIT. 5:2.
1. Wane yanayi ne Kiristoci suke ciki sa’ad da Bitrus ya rubuta wasiƙarsa ta farko?
MANZO Bitrus ya rubuta wasiƙarsa ta farko kafin Nero ya soma tsananta wa Kiristoci da ke Roma. Yana son ya ƙarfafa ’yan’uwansa masu bi. Iblis “yana yawo” yana neman ya halaka Kiristoci. Don su yi tsayayya da shi, suna bukatar su “yi hankali shinfiɗe” kuma su ‘ƙasƙantar da kansu a ƙarƙashin hannu mai iko na Allah.’ (1 Bit. 5:6, 8) Suna bukatar su kasance da haɗin kai. Bai kamata suna ‘cizon juna kuma suna cinye junansu’ don hakan zai sa su ‘halaka a bakin junansu.’—Gal. 5:15.
2, 3. Wane ne ya kamata mu riƙa kokawa da shi, kuma mene ne za mu bincika a cikin wannan jerin talifofi?
2 Muna fuskantar irin wannan yanayin a yau. Iblis yana neman zarafin halaka mu. (R. Yoh. 12:12) Kuma ba da daɗewa ba “za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya.” (Mat. 24:21) Mu ma za mu guji yin jayayya tsakaninmu kamar yadda Kiristoci na ƙarni na farko suke bukatar su guji yin hakan. A wasu lokatai muna bukatar taimakon dattawa da suka cancanta don mu yi hakan.
3 Bari mu yi la’akari da yadda dattawa za su ƙara yin godiya don gatar ziyarar ƙarfafa ‘garken Allah wanda ke wurinsu.’ (1 Bit. 5:2) Bayan haka, za mu yi koyi da hanyar da ta dace na yin aikin ziyarar ƙarfafa. A talifi na gaba, za mu bincika yadda ikilisiya za ta iya ‘girmama masu aiki tuƙuru a cikinsu, wato waɗanda ke shugabancin’ garken. (1 Tas. 5:12, Littafi Mai Tsarki) Bincika waɗannan batutuwa zai taimaka mana mu yi tsayayya da babban Magabcinmu, domin mun fahimci cewa da shi muke kokawa.—Afis. 6:12.
Ku Yi Kiwon Garken Allah
4, 5. Yaya ya kamata dattawa su ɗauki garken? Ka ba da bayani.
4 Bitrus ya ƙarfafa dattawan Kiristoci na ƙarni na farko su kasance da ra’ayin Allah game da garken da ke ƙarƙashin kulawarsu. (Karanta 1 Bitrus 5:1, 2.) Bitrus bai yi wa dattawa magana da reni ba kamar yana ɗaukan kansa mafifici ne, ko da yake an ɗauke shi a matsayin ginshiƙin ikilisiya. Maimakon haka, ya gargaɗe su a matsayin ’yan’uwansa dattawa. (Gal. 2:9) Kamar yadda Bitrus ya yi, Hukumar Mulki a yau tana yi wa dattawan ikilisiya gargaɗi su yi ƙoƙari su cika hakkinsu mai girma na ziyarar ƙarfafa garken Allah.
5 Manzon ya rubuta cewa dattawa za su yi ‘kiwon garken Allah wanda ke wurinsu.’ Yana da muhimmanci sosai su fahimci cewa garken na Jehobah ne da kuma Ɗansa Yesu Kristi. Dattawa za su ba da lissafin yadda suke kula da tumakin Allah. A ce abokinka na kud da kud ya gaya maka ka kula da yaransa sa’ad da ya yi tafiya. Shin ba za ka kula da su sosai kuma ka ciyar da su ba? Idan yaro ɗaya ya yi ciwo, shin ba za ka tabbata cewa ya samu magani daga asibiti ba? Haka nan ma, dattawa da ke cikin ikilisiya za su “yi kiwon ikilisiyar Allah, wadda ya sayi da jinin [Ɗansa].” (A. M. 20:28) Suna tunawa cewa an sayi kowace tunkiya da jini mai tamani na Yesu Kristi. Da yake za su ba da lissafi, dattawa suna ciyar da kāre da kuma kula da garken.
6. Wane hakki ne makiyaya na dā suke da shi?
6 Ka yi tunanin hakkin da makiyaya na zahiri suke da shi a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Suna jimrewa da zafin rana da sanyin dare domin su kula da garken. (Far. 31:40) Suna ma sa ransu cikin kasada don tumakin. Dauda, yaro makiyayi ya ceci garkensa daga namomin jeji, har da zaki da kuma bear. Da yake magana a kan kowanne mutum, Dauda ya ce ya ‘kama shi a gemunsa, ya buga shi, ya kashe shi.’ (1 Sam. 17:34, 35) Hakika, wannan jarumtaka ne! Dabbar ta kusan yin kaca-kaca da shi! Duk da haka, ya yi iya ƙoƙarinsa don ya ceci tumakin.
7. A hanya ta alama, ta yaya dattawa za su kwato tumaki daga wurin Shaiɗan?
7 A yau, dattawa suna bukatar su mai da hankali ga harin Iblis da ya yi kama da na zaki. Hakan ya ƙunshi aikatawa da gaba gaɗi kuma a alamance a kwato tumaki daga hannu Iblis. Ta wurin kama gemun dabbar, a alamance dattawa za su iya ceton tumakin. Suna iya tattaunawa da ’yan’uwa da ba sa a faɗake da Shaiɗan yake gwada su da tarkunansa. (Karanta Yahuda 22, 23.) Hakika, dattawa suna yin hakan da taimakon Jehobah. Suna bi da ɗan’uwa da ya ji rauni a hankali, su ɗaure masa raunin kuma su shafa masa māi na Kalmar Allah mai warkarwa.
8. Dattawa suna ja-gorar garken zuwa ina ne, kuma ta yaya suke hakan?
8 Makiyayi na zahiri yana ja-gorar garken zuwa wurin kiwo da ya dace da kuma wuri mai dausayi. Haka nan ma, dattawa suna ja-gorar ’yan’uwa zuwa ikilisiya, suna ƙarfafa su su riƙa halartan taro a kai a kai don a ciyar da ’yan’uwan sosai kuma su samu “abincinsu a lotonsa.” (Mat. 24:45) Dattawa suna iya bukatar su ba da ƙarin lokaci don su taimaki waɗanda suke ciwo a ruhaniya su ci abinci daga Kalmar Allah. Wataƙila, tunkiya da ta bijire tana ƙoƙari ta dawo garken. Maimakon su tsoratar da ɗan’uwansu, dattawa suna bayyana masa ƙa’idodin Nassi a hankali kuma su nuna masa yadda zai yi amfani da su a rayuwarsa.
9, 10. Yaya ya kamata dattawa su kula da masu ciwo a ruhaniya?
9 Wane irin likita ne ka fi so sa’ad da kake rashin lafiya? Wanda yake ba da ɗan lokaci don ya saurare ka kuma nan da nan ya gaya maka maganin da za ka sha domin wani majiyyaci ya shigo ne? Ko kuwa za ka je wurin likitan da yake sauraronka da kyau, kuma ya bayyana abin da yake damunka, kuma ya gaya maka magungunan da za su iya taimakonka?
10 Haka nan ma, dattawa suna iya sauraron wanda yake ciwo a ruhaniya kuma su ba da taimako don warkar da ciwon, da hakan, a alamance suna “shafe shi da mai cikin sunan Ubangiji.” (Karanta Yaƙub 5:14, 15.) Kamar māi na Gilead, Kalmar Allah za ta iya warkar da mai ciwo. (Irm. 8:22; Ezek. 34:16) Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka wa wanda ya raunana ya soma hidimarsa kuma ga Jehobah, idan ya yi amfani da su. Hakika, dattawa suna taimakawa sosai sa’ad da suka ji damuwar wanda ya raunana kuma su yi addu’a tare da shi.
Ba Kamar na Tilas ba amma da Yardan Rai
11. Me ke motsa dattawa su yi kiwon garken Allah da yardan rai?
11 Sai Bitrus ya tuna wa dattawa yadda ya kamata su yi aikin ziyarar ƙarfafa da kuma abin da bai kamata su yi ba. Dattawa za su yi kiwon garken Allah “ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai.” Mene ne ke motsa dattawa su yi wa ’yan’uwansu hidima da yardan rai? Mene ne ya motsa Bitrus ya yi kiwon tumakin Yesu da kuma ciyar da su? Ƙaunar da yake wa Ubangiji ne ainihin abin da ya motsa shi. (Yoh. 21:15-17) Domin ƙauna, dattawa ba sa “ƙara rayuwa da kansu, amma ga wanda ya mutu . . . sabili da su.” (2 Kor. 5:14, 15) Wannan ƙaunar, tare da ƙaunarsu ga Allah da kuma ’yan’uwansu ce ke motsa dattawa su yi hidima ga garken, suna ba da ƙoƙarce-ƙoƙarcensu da dukiyarsu da kuma lokacinsu ga yin hakan. (Mat. 22:37-39) Suna ba da kansu ba don dole ba ne amma da yardan rai.
12. Yaya yawan yadda manzo Bulus ya ba da kansa?
12 Yaya yawan yadda dattawa za su ba da kansu? Wajen kula da tumakin, za su yi koyi da manzo Bulus, kamar yadda ya yi koyi da Yesu. (1 Kor. 11:1) Da yake yana ƙaunar ’yan’uwa da ke Tasalonika, Bulus da abokansa sun ji daɗin yin ‘bisharar Allah da kuma ba da rayukansu.’ Sa’ad da suke hakan, sun zama kamar mai reno wadda “ta ke kiyayar da ’ya’yan kanta.” (1 Tas. 2:7, 8) Bulus ya fahimci yadda mai reno take ji game da yaranta. Za ta yi musu kome, har da tashiwa da tsakar dare don ta ba su aminci.
13. Dattawa suna bukatar su kasance da wane daidaitaccen ra’ayi?
13 Dattawa suna bukatar su mai da hankali don su daidaita hakkinsu na ziyarar ƙarfafa da kuma hakkinsu ga iyalansu. (1 Tim. 5:8) Lokacin da dattawa suke amfani da shi don ikilisiya lokaci ne mai tamani da za su kasance tare da iyalansu. Hanya ɗaya da za su iya daidaita waɗannan hakkoki biyu ita ce su gayyaci ’yan’uwa zuwa Bautarsu ta Iyali da yamma a wasu lokatai. Fiye da shekaru da yawa, wani dattijo mai suna Masanao da ke ƙasar Japan, yakan gayyaci ’yan’uwa da ba su yi aure ba da kuma iyalai da ubanninsu ba masu bi ba ne zuwa nazarinsu na iyali. Da shigewar lokaci, wasu da aka taimaka musu suka zama dattawa kuma suka yi koyi da misali mai kyau na Masanao.
Ku Guji Riba Mai Ƙazanta, Ku Yi Kiwon Garken da Karsashin Zuciya
14, 15. Me ya sa dattawa za su guje wa “riba mai-ƙazanta,” kuma ta yaya za su yi koyi da manzo Bulus a wannan batun?
14 Bitrus ya kuma ƙarfafa dattawa su yi kiwon garken ba da “riba mai-ƙazanta ba, amma da karsashin zuciya.” Aikin dattawa yana ɗaukan lokaci mai yawa, duk da haka ba sa sa rai cewa za a biya su. Bitrus ya ga bukatar yi wa ’yan’uwansa dattawa gargaɗi a kan haɗarin kiwon garken don “riba mai-ƙazanta.” Ana ganin wannan haɗarin a rayuwar sukuni da shugabannan addinai na “Babila babba” suke yi, yayin nan kuma suna tilasta wa mutane da yawa su yi rayuwa na talauci. (R. Yoh. 18:2, 3) Dattawa a yau suna da dalili mai kyau na mai da hankali da kasancewa da irin wannan halin.
15 Bulus ya kafa wa dattawan Kirista misali mai kyau. Ko da yake shi manzo ne, bai “nauwaita ma” Kiristoci da ke Tasalonika ba, kuma bai “ci abinci kyauta daga hannu kowa ba.” Maimakon haka, ya yi ‘wahala yana aiki dare da rana.’ (2 Tas. 3:8) Dattawa da yawa a zamani har da waɗanda suke aikin ziyara sun kafa misali mai kyau a yin hakan. Ko da yake suna amincewa da halin karɓan baƙi da ’yan’uwa suke nuna musu, ba sa “nauwaita ma” kowa ba.—1 Tas. 2:9.
16. Mene ne yake nufi a yi kiwon garken da “karsashin zuciya”?
16 Dattawa suna kiwon garken Allah da “karsashin zuciya.” Ana ganin hakan ta wurin halinsu na sadaukar da kansu wajen taimakon garken. Amma, hakan ba ya nufin cewa suna tilasta wa garken su bauta wa Jehobah kuma dattawa masu ƙauna ba sa ƙarfafa wasu su bauta wa Allah ta wajen yin gasa da juna. (Gal. 5:26) Dattawa sun fahimci cewa kowane bawan Allah yana da irin halinsa dabam. Suna ɗokin taimaka wa ’yan’uwansu su bauta wa Jehobah da farin ciki.
Kada Ku Nuna Sarauta Bisa Garken, amma Ku Nuna Gurbi
17, 18. (a) Me ya sa a wani lokaci ya yi wa manzannin wuya su fahimci koyarwar Yesu game da tawali’u? (b) A wane makamancin yanayi ne za mu iya tsinci kanmu?
17 Kamar yadda muka tattauna, ya kamata dattawa su tuna cewa garken da suke kiwonsa na Allah ne ba nasu ba. Suna mai da hankali don kada su ‘nuna sarauta bisa abin kiwo da Allah ya sanya a hannunsu.’ (Karanta 1 Bitrus 5:3.) A wasu lokatai, manzannin Yesu sun nemi su samu gata da muradi da bai dace ba. Kamar waɗanda suke sarauta bisa al’ummai, suna son su samu matsayi mai girma.—Karanta Markus 10:42-45.
18 A yau, ya kamata ’yan’uwa maza da suke “biɗan aikin” kula da ikilisiya su bincika kansu game da dalilin da ya sa suke biɗan wannan aikin. (1 Tim. 3:1) Yana da kyau dattawa su tambayi kansu ko suna son iko ko kuma yin suna kamar yadda wasu manzanni suka yi. Idan ya yi wa manzannin wuya su yi hakan, ya kamata dattawa su yi ƙoƙari su guji kowanne halin duniya na jin daɗin nuna iko bisa wasu.
19. Me ya kamata dattawa su tuna da shi sa’ad da suke ɗaukan mataki don su kāre garken?
19 Hakika, da akwai lokatai da dattawa suke bukatar su yi tsayin daka, kamar sa’ad da suke kāre garken daga “kerketai masu-zafin hali.” (A. M. 20:28-30) Bulus ya gaya wa Titus ya ci gaba da ‘yin gargaɗi da tsautarwa’ da cikakken iko. (Tit. 2:15) Duk da haka, sa’ad da suke yin hakan, dattawa za su yi ƙoƙari su daraja waɗanda suke yi musu hakan. Sun san cewa maimakon su yi zargi da zafin rai, yin rinjaya a hankali ya fi amfani wajen taɓa zuciya da kuma sa mutum ya bi tafarkin da ya dace.
20. Ta yaya dattawa za su yi koyi da Yesu wajen nuna misali mai kyau?
20 Misali mai kyau na Kristi ya motsa dattawa su ƙaunaci garken. (Yoh. 13:12-15) Muna farin ciki sa’ad da muka karanta yadda ya koya wa almajiransa wa’azi da kuma aikin almajirtarwa. Misalinsa na tawali’u ya taɓa zukatan almajiransa, kuma ya sa su bi tafarkin nuna ‘tawali’u da mai da wani ya fi su.’ (Filib. 2:3) Hakan ma ya sa dattawa a yau su bi misalin Yesu, kuma su zama ‘gurbi ga garken.’
21. Wane lada ne dattawa suke ɗokin samu?
21 Bitrus ya kammala gargaɗinsa ga dattawa wajen yin magana ga alkawari da zai faru a nan gaba. (Karanta 1 Bitrus 5:4.) Masu kula shafaffu za su “karɓi rawanin daraja wanda ba shi yin yaushi ba” da Kristi a sama. Makiyaya da suke cikin “waɗansu tumaki” za su samu gatar kiwon garken Allah a duniya a ƙarƙashin sarautar “babban Makiyayi.” (Yoh. 10:16) Talifi na gaba zai tattauna hanyoyi da waɗanda suke cikin ikilisiya za su iya tallafa wa waɗanda aka naɗa su yi shugabanci.
Ta Hanyar Bita?
• Me ya sa ya dace Bitrus ya ƙarfafa ’yan’uwansa dattawa su yi kiwon garken Allah da suke ƙarƙashin kulawarsu?
• Yaya ya kamata dattawa su yi kiwon waɗanda suke ciwo a ruhaniya?
• Mene ne ke motsa dattawa su yi kiwon garken da ke ƙarƙashin kulawarsu?
[Hoto a shafi na 21]
Kamar makiyaya na zamanin dā, dole ne dattawa a yau su kāre “tumakin” da ke ƙarƙashin kulawarsu